Ticker

6/recent/ticker-posts

Zamantakewar Al’umma a Lokacin Yunwa: Tsokaci Daga Wasu Waƙoƙin Baka na Hausa

 A al’adance, Hausawa mutane ne masu zamantakewa irin ta cuɗe-ni-in-cuɗe-ka, ba zamantakewa irin ta kaɗaici ba, irin wanda kowa kansa kawai ya sani sai kuwa iyalansa. Irin zamantakewar da al’ummar Hausawa ke yi irin wannan ce ta, mu gudu tare, mu kuma tsira tare.

Hausawa al’umma ce da take zaune a yankin arewa maso yamma na ƙasar Nijeriya, da kuma wani sashe na kudancin ƙasar Nijar. Wannan yanki ya kasance ne tsakanin sabana ta sudan da kuma sahel. Waɗannan yankunan a wani lokaci kan yi fama da ƙamfar ruwan sama a lokacin damina wanda wani sa’ili kan haifar da rashin kyawon kayan amfanin gona da ake nomawa. Sakamakon haka akan sami aukuwar yunwa ko ƙarancin cimaka, lokaci-lokaci.

Misali, ‘Yar Gusau yunwa ce da ta addabi wani sashe na ƙasar Hausa a shekara ta 1943. An yi fama da yunwar Muɗa a shekara ta 1953. Yunwar Bankaura kuwa, a shekarar 1973. ‘Yar Buhari, ta faɗawa ƙasar Hausa ne a shekara ta 1984. Nufin wannan muƙala ne ta yi tsokaci kan yadda lamarin zamantakewa a tsakanin al’ummar Hausawa kan kasance a lokacin yunwa, musamman kamar yadda wasu mawaƙan baka suka ƙyallaro shi, suka kuma suranta hoton zamantakewar a cikin waƙoƙinsu na baka, musamman waƙoƙin da aka yi a baya-baya wato daga 1984 da aka yi ‘Yar Buhari, ya zuwa yunwar da aka yi a wajajen 1996.

yunwa

Zamantakewar Al’umma a Lokacin Yunwa: Tsokaci Daga Wasu Waƙoƙin Baka na Hausa

DR. MUSA FADAMA GUMMI

Email: gfmusa24@gmail.com

Phone No.: 07065635983

1.0 Gabatarwa

 Adabi madubi ne ko hoto na rayuwar al’umma. Abu ne da ya game dukkanin rayuwar al,umma musamman fasaharsu, da hikimominsu. Fasahohi da hikimomin al’umma kan haɗa da maganganun hikima kamar kirari, da take, da habaici, da gugar zana, da baƙar magana, da Karin magana, da tatsuniyoyi, da labarai, kai har da uwa uba, waƙa. Waƙar baka wani rukuni ne daga cikin rukunan adabin baka sannan waƙa wani ma’adani ce ko rumbu na tarihi kuma tana nuna hoto na rauyar al’umma.

Wannan dalili ne ya sanya wannan muƙala ta ƙuduri anniyar duba wannan rumbu na ajiyar tarihi domin duba yadda zamantakewa tsakanin al’ummar Hausawa kan kasance a lokacin yunwa, kamar yadda wasu mawaƙan baka suka hanga, suka kuma bayyana a cikin waƙoƙin yunwa na baka da suka rera a lokuta daban-daban. Yunwa bala’i ce don haka takan shafi yadda al’umma kan gudanar da rayuwarta. Abin dubawa a gani a nan shi ne shin yunwar kyautata zamantakewar take yi ko a’a zamantakewar gurɓata take? Duba waƙoƙin zai ba da haske a kan yadda lamarin kan kasance. Kafin duba wannan lamari a cikin waƙoƙin baka, ya dace a kalli ma’anar yunwa da kuma waƙar baka.

1.1 Ma’anar Yunwa

 Masana daban-daban sun yi ƙoƙari a wurare daban-daban, su bayyana abin da ake kira yunwa. A ƙamus na Longman cewa aka yi yunwa ita ce tsananin rashin abinci ga jama’a masu yawa.

Bargery (1933:1117) a cikin Ƙamusun Hausa da Turanci, cewa ya yi yunwa tana nufin jin buƙatar cin abinci irin yadda aka saba idan an ɗauki lokaci mai tsawo ba a ci abinci, wato abin da a harshen Ingilishi ake kira ‘Hunger’. Ɗaya ma’anar da Ƙamusun ya kawo shi ne cewa kalmar yunwa tana iya ɗaukar ma’anar wani bala’i na ƙaranci abinci ga wata al’umma ta wani yanki ko ƙasa, wato abin nan ake kira ‘famine’ a harshen Ingilishi.

A cikin kundin Encylopidae Brittanica, cewa aka yi yunwa ita ce matsanancin ƙarancin abinci a wani yanki ko wata ƙasa baki ɗaya, wanda ke sa a tagayyara har ma da mace-mace.

 Watts, (1983:1) cewa ya yi yunwa tana nufin wani bala’i da kan shafi al’umma, wanda ke haddasa ƙarancin abinci ta yadda jama’a masu dama za su tagayyara.

 Umar, (1992:5) gani yake cewa yunwa ita ce matsanancin ƙarancin abinci. Watau mutane su rasa abincin da zai wadace su.

 Malumfashi, (2002), cewa ya yi wasu za su ce ai ba komi ba ne yunwa face zafin ciki da mutum kan ji idan bai ci abinci ba, ko rashin isasshen abinci mai sa ƙoshin lafiya. Haka ne amma yunwa ta wuce nan. Duk wanda ya ɗauki yunwa a matsayin rashin cin abinci ko ramewa saboda rashin ƙoshi to bai fahimci yunwa sosai ba. A ganinsa yunwa ta haɗa da talauci da fatara.

Fadama (2008), cewa ya yi idan Bahaushe ya ce yunwa to tana iya ɗaukar ɗaya daga cikin ma’anoni biyu. Na farko dai tana nufin zafin cikin da mutum kan ji idan bai ci abinci ba na wani ɗan lokaci, ko da kuwa yana da abincin. Ma’ana da zarar mutum ya ji yana matuƙar buƙatar abinci to kuwa yana jin yunwa. Irin wannan yunwa ta yi daidai da abin da wani mawaƙin noma, Makaɗa Illon Kalgo, a jihar Kebbi ya ce a wata waƙa tasa ta gonar Sardauna.

Jagora:                        Shehu Kalgo taho rakkan ni

 : Mu zo waƙar gona

 : Ni kam gona can nika wasa

 : In kwan can

 : In yini can in koma hantci

 : Raina kwal

 : Gonar Sardauna

 : Ba ka jin yunwak komi

 : Kowa shiga gonar Amadu

 : Has shi wuce duniyag ga

‘Yan Amshi: Bai yunwa ko ɗai.

 

 ( Makaɗa Illon Kalgo Waƙar Gonar Bakura gonar Sardauna)

           

Ɗaya ma’anar kuwa ita ce hali na matuƙar ƙarancin abinci ga mafi yawan jama’a na wata al’umma wanda ke sa a tagayyara, wani lokaci har da mace-mace. Irin wannan bala’i na yunwa ya yi daidai da abin da wani mawaƙi, Amali Sububu na ƙasar Maradun a jihar Zamfara yake cewa:

Jagora:             “Rani wanga ya yi rani

Ya sa maza lage,

            Tafiya wagga ta yi nisa

                        Ta sa maza gaba

            Yunwa wagga ta yi yunwa

             Ta ba mu arkane

                         Ga mata da ‘yan ɗiya

 Ka ji ƙatonta ya yi lalata

 Ya ba ta wuri

Yara: Ya tcere yana ta kai nai”.

 ( Amali Sububu: ‘Noma Ba ya Sa Ka Rama’)

Watau ke nan yunwa iri biyu ce, akwai ta al’ada wadda aka saba da ita yau da kullum da kuma ta bala’i wadda kan sami al’umma lokaci-lokaci.

1.2 Ma’anar Waƙar Baka.

 Masana da dama sun yi namijin ƙoƙari wajen bayyana abin da waƙar baka take nufi. Bisa ma’ana, Yahya, (1997:4) yana kallon waƙa a matsayin tsararriyar maganar hikima da ta ƙunshi saƙo cikin zaɓaɓɓaɓun kalmomi da aka auna domin maganar ta reru ba faɗa kurum ba. Masanin ya ce ita waƙar baka ana rera magana ne tare da amfani da kayan kiɗa bayan zaɓen kalmomi da tsaru su.

 A wurin Gusau (2003: xiii), waƙar baka wani zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin tsari da daidaitawa a rere cikin sautin murya da amsa-amon kari da kiɗa da amshi.

 Idan aka yi la’akari da abin da masana suka faɗa dangane da abin da suke ganin ake kira waƙar baka, to ana iya cewa waƙar baka wani zance ne na hikima ko magana wadda aka shirya ta hanyar tsara kalmomi zaɓaɓɓu kuma zaunannu, a rera su gutsure-gutsure cikin azanci da salon armashi, tare da yin kiɗa, da amshi, da nufin isar da saƙo.

 Yanzu ya dace a duba yadda zamantakewar al’umma kan kasance a lokacin yunwa kamar yadda wasu mawaƙan baka suka hango.

2.0 Yanayin Zamantakewa A Lokacin Yunwa

A al’adance, Hausawa mutane ne masu zama irin na cuɗe-ni-in-cuɗe-ka. Ba zama irin na kaɗaici wanda kowa kansa ya sani ba. Irin zaman da al’ummar Hausawa ke yi irin zaman nan ne na ‘mu gudu tare mu tsira tare’. Wannan ya sa tun fil azal Hausawa suke irin zaman nan na gandu wanda uba tare da iyalansa da iyalan danginsa har da barori suke zaune a wuri ɗaya. A irin wannan zama komai tare ake yi. Bayan an fitar da mutum daga gandu sai ya kama aikin kansa. To amma duk da haka, ranar da ya kasa, watakila sakamakon wata rashin lafiya ko wani abu mai kama da haka, to kuwa ana taruwa a taimaka masa. Irin haka, na ɗaya daga cikin abin da ya sa ake yin aikin gayya. Irin zaman cuɗe-ni-in-cuɗe-ka da Hausawa ke yi ya sa idan lalurar bukin aure ko na haihuwa ta sami ɗan’uwa ko ma duk wani makusanci, akan taru kowa ya ba da tasa gudunmawa ko ta kuɗi ko ta abinci. Yin haka, ga dukkan alamu, shi ya haifar da al’adar nan ta buki. Ko ma ba wannan ba, duk wata matsalar da ta sami wani wadda ake ganin ta fi ƙarfinsa, to taruwa ake yi a haɗa ƙarfi don a warware masa ita.

Irin wannan zama da Hausawa ke yi wanda har ya zame masu al’ada, wani lokaci akan kauce masa, musamman a lokacin matsuwa. Watau lokacin da wani bala’i, na rashin abincin da za a ci, ya auka wa wata al’umma. Tarihi ya nuna irin wannan kan auku daga lokaci zuwa lokaci. A lokacin yunwa akan sami akasi na kyakkyawar zamantakewa da aka san Hausawa da ita. Zamantakewa sai ta gurɓace, a sami rayuwa ta kaɗaici, da rowa, zama da ƙazanta, da kisan aure, da hali na talaucewa, da yaudara, da uwa uba ƙaura. Yanzu sai a bi su ɗaya bayan ɗaya, a ga yadda suke aukuwa kamar yadda aka kawo su a cikin waƙoƙin baka daban-daban.

2.1 Rayuwar Kaɗaici Da Rowa.

A lokacin yunwa, musamman ma dai idan ta yi tsanani, akan sami rayuwa ta kaɗaici. Rayuwa irin wadda kowa kansa kawai ya sani. Rayuwar da idan mutum ya sami ɗan abin da zai ci sai ya manta da wasu makusantansa. Irin wannan hoton rayuwa ne Amali Sububu na ƙasar Maradun a jihar Zamfara, ya ambata a cikin wata waƙa tasa. Amali Sububu, yana cewa:

“Ashe yunwag ga na sa,

Mutum ya gaza da mata,

Ya sa a yi mai jiƙo,

Ba ya ce mata tashi ga shi”.

(Amali Sububu, waƙar Mai batun yaƙi da sabra).

 A wani ɗan waƙa da Shayau Maizari Gayari, ƙasar Gummi a jihar Zamfara ya rera, yana cewa:

 “ Yunwa bala’i ta Shaya

 Mai sa a kama gudun dangi.”

 ( Shayau Maizari, ‘Maiƙwandama’)

 Hoton da Amali Sububu ke son ya nuna mana a cikin wannan ɗa na waƙarsa shi ne cewa, saboda yunwa mutum zai kasa cika wani haƙƙi da addininsa da kuma al’adarsa suka ɗora masa na ciyar da matarsa. Ya sa a jiƙa masa garin rogo/kwaki amma kuma ya manta ba zai ba matarsa ba. Wannan rayuwa ce irin ta lokacin yunwa. Shayau kuwa cewa ya yi yunwa tana sa a guji dangi.

2.2 Yawan Fushi Da Kisan Aure

 Aure halacci ne na zamantakewa tsakanin mace da namiji su kasance mata da miji domin samar da zuriya ta halat ta yadda za a sami danƙon zumunci a tsakanin al’umma da kuma mutane nagartattu. Al’ummar Hausawa ta rungumi al’adar aure tun gabanin saduwarta da kowace al’umma ta duniya walau daga gabas ko daga yamma. Hausawa kan ƙulla aure ne da niyar ɗorewarsa har abada face in lamurra sun dagule ne ake samu rabuwa tsakanin ma’aurata. A lokacin yunwa akan sami yawan hushi saboda zafin rai da yunwar take haddasawa wanda wani lokaci kan haifar da yawan kisan aure. A kan yawan husata da zafin rai wanda yunwa take haddasawa, wani mawaƙi a wani ɗan waƙa tasa yana cewa:

 

Jagora:                        Hunger is very danger

            If you are feeling hunger

            It will make you anger.

Yara:   Wai yunwa bala’i ta

            In yazzan kana jin ta,

Zahin rai take sa wa.

            (Alh. Sani Da’aino Gyalange Waƙar Sarkin Noma Maigayya).

A kan kisan aure kuwa, wata Mawaƙiya mai waƙar begen Manzon Allah, Gwamma Maibege Iyaka, ƙasar Gummi a Jihar Zamfara ta faɗa a wani ɗan waƙa tata, cewa:

 “ In hwaɗa maka

 Yunwam Muɗa marar albarka

 Ta sa maza sakin matansu

 Ta sa maza su tudda ɗiyansu

 Abdu an wani ɗa sai lahira ya gane gidansu.”

 ( Gwamma Maibege, ‘Yunwar Muɗa’)

Shayau Maizari Gayari kuwa cewa ya yi:

 “ Maikwandama zakkay yunwa

 Ta bi wake ta ride

 Ta bi maiwa ta ride

 Ta bar mazanmu cikin ragga

 Koyaushe mata na kotu

 Kowa a kai mashi sammace

 Kowace a ce mata na bakki.”

 ( Shayau Maizari, ‘Maiƙwandama’)

A wani ɗan waƙa na daban, cikin waƙarsa ta ‘Maiƙwandama’, Shayau na cewa:

 “ Maiƙwandama babbay yunwa

 Ko mai idanu ta kamtce

 Yau kam makahi tah hwarma.”

 “ Maiƙwandama ka kashin arme

 Don kak ku ce mana mata na.”

 “ Ga mace ba komi na kari

 Macce babu hurak kurɓi

 Waken Adar ya ƙare

 Ɗan hanƙurin nan guntu na.”

 ( Shayau Maizari, ‘Maiƙwandama’)

 

2.3 Zama Da Ƙazanta ko Rashin Tsabta

Tsabta masu iya Magana suka ce cikon addini. Hausawa mutane ne da al’adarsu da kuma addininsu na musulunci suka tanadi a yi tsabta ta jiki da ta sutura. Wannan ya haɗa kwalliya ta hanyar saka sutura kyakkyawa, da ɗaura lalle tare da shafe-shafe a fuska ga mata, Wannan kyakkyawan al’amari kan sami naƙasu a lokacin da al’umma ke fama da yunwa. Makaɗa Shayau maizari Gayari ya ambaci wannan a wani ɗan waƙa tasa ta ‘‘Yar wara’ inda ya ce:

 “ ‘Yar wara Shayau in gaya ma

 Mai hana mata shafa kwalli

 Ɗarmin lalle ba a yi nai.”

 “ Haba ‘yar wara!

 Shayau yunwa ba ta tausai

 Ka tcinkai mata sun yi gungu

 Kowace na shafah hawaye

 Ɗarmin lalle ba a yi nai

 Har da kitso bana ba su yi nai.”

 ( Shayau Maizari, Waƙar ‘ ‘Yar wara’)

Wara wake ne da aka fi sani da waken soya. Ana sarrafa shi a yi wani abinci na ƙwalama da ake kira wara. A shekara ta 1996, zamanin mulkin soja na Janar Sani Abaca, mutane sun shiga cikin matsi na tattalin arziki da ta kai har wasu suna cin dusa ta waken soya, bayan an haɗa ta da ƙuliƙuli da gishiri. Wannan matsi na rayuwa ne Shayau Mai zari Gayari a ƙasar Gummi, jihar Zamfara ya waƙe, ya kuma saka wa wannan yunwa suna ‘Yar wara.

Ɗaurin lalle kwalliya ce da matan Hausawa kan yi ta hanyar kwaɓa garin lalle a saka a hannu da ƙafafuwa domin jiki ya kasance ja. Ana saka gishirin lalle domin a samu baƙi a ƙafa da hannu, abin gwanin sha’awa. Kitso ma kwalliya ce da ake wankewa tare tsefe gashin mata a kuma shirya ta hanyar tufƙa. Lalle da kitso gyaran jiki ne da al’adar Bahaushe ta tanadar wa mata. A lokacin yunwa kamar yadda wannan Mawaƙi ya nuna mata ba sukan damu da yin irin wannan kwalliya ba saboda sai ciki ya cika ake zancen kwalliya.

2.3 Yaudara Da Sata                    

 Yaudara da sata miyagun halaye ne da al’adar Bahaushe da kuma addinin musulunci ba su ba gurbin zama ba a cikin al’umma. Don haka ne ma ya sa duk wanda yake yin waɗannan ɗabi’u, akan yi masa wani kallo na mutumin banza kuma ma akan yi masa kyara, wani lokaci akan yi hukunci ga wanda ya aikata ɗaya daga cikin ɗabi’un. Duk wannan matsayi da ɗabi’un suke da shi a al’umma, a lokacin da rayuwa ta shiga cikin ƙunci na matsanancin talauci da yunwa sai a tarar wasu suna aikata halayen ba don suna da muradin yin haka ɗin ba sai don halin matsi da ƙunci na rayuwa da suka sami kansu a ciki. Halin ɓera ne Shayau Maizari Gayari ya kawo a cikin wani ɗan waƙa nasa. Wai wani ya saci ƙullin garin kwaki a wurin wata Bayaraba amma sai ta gan shi.

 “Ya tai wurin garin kwaki

 Sai da yah hizgo ƙulli

 Mama sai tas sa kuwa

 ‘Soho’ a zan ‘soron’ Allah

 Koyaushe sai ke dau kulli.”

 ( Shayau Maizari, waƙar “ Maiƙwandama”)

Ita ma Gwamma Maibege Iyaka ta kawo hoton yaudara a cikin wani ɗan waƙa tata ta ‘Shahwa’atu’ inda take cewa:

 Jagora: Ba ka san ƙabdogala ba

 Shiga mota babu kuɗɗi

 Yara: Muhammadu Ɗanlarabawa

 Jagora: Yaro ba ka san ƙabdogala ba

 A shige mota babu kuɗɗi.

Wai a lokacin wata yunwa ce da ake kira ‘Shahwa’atu’ mawaƙiyar da yaranta suka shiga motar haya ba tare da suna da kuɗin biya ba. Sai da aka kai su wajen da za su sauka aka tambayi kuɗin mota shi ne take yi wa yaron mota wannan tambayar .

2.4 Talaucewa

Yunwa da talauci, abokan tafiyar juna ne, wato Ɗanjumma ne da Ɗanjummai. A lokacin yunwa, ba ƙarancin abinci kawai ake fama da shi ba, har ma da talauci. A sakamakon matsanancin rashin abinci da na kuɗi, mutane kan sayar da kayayyakinsu har ma da dabbobi don su sayi abinci. Matan aure kuwa sukan sayar da kayan ɗakinsu kamar kwanoni da gadaje, don su sami kuɗin sayen abinci, lokacin da mazajensu suka kasa. Waƙoƙin yunwa sukan ƙunshi bayani irin wannan. Misali, wani ɗan waƙa na waƙar ‘‘Yar Zanhwara’ yana cewa:

‘Yaz zanhwara ba ki barin kanta

Ke canye kabid da tasohi

Balle kwalla abin banza

Hwanteka ba a ko magana

Kai hadda zanen gado an kai

An canye ɓula da ɗan sululuf

       (Hira da sa’a Maiƙosai Gummi, ranar 6/11/04).

Zamfara jiha ce da aka ƙirƙiro a watan Oktoba na shekarar 1996, lokacin mulkin soja ƙarƙashin jagorancin Janar Sani Abaca. A daidai wannan lokaci, mutane suna cikin wani hali na ƙaƙa-ni-ka yi soboda matsi na tattalin arziki da kuma ƙarancin abinci. Wannan matsin shi ne wasu suke kira ‘Yar Zamfara”. Wannan waƙa ta nuna yadda matan aure suke kwashe kayan ɗakinsu kamar kwanoni, da tasoshi, da katifu domin sayarwa a sami kuɗin sayen abin da za a ci.

A wata mai kama da wannan, Shayau Maizari yana cewa:

Nit tai bara Shayau ƙauye

Ni iske mata na shiƙa

Nit tai bara Shayau ƙauye

Manu na kukan yunwa

Ga ni ba ni gani Shaya

Dac can guda tac ce shaya

Shaya koma birninku

Koyaushe birni, birni na

Na sai da hwanteƙa shidda

Na ba miji ya sai tsaba

Sai guda tacce shaya

Ko ni awaki sun ƙare

Saura na ga-kiwo ɗai an nan

       (Shayau Maizari: ‘Maiƙwandama’).

A wani ɗa na waƙarsa ta “‘Yar Wara” ’, Shayau yana cewa:

‘Yar wara Shayau in gaya ma

Ta ci awaki, ta ci kaji

Ta amshe shanun talakka

Ta bar ƙato na hawaye

Ta amshe shanun talakka

To Allah ka jiƙam Musulmi

 (Shayau Maizari: ‘‘Yar wara’).

Ita ma Gwamma Maibege tana cewa a wani ɗa na waƙarta ta ‘Shahwa’atu’.

Jagora:                  Ina kurin na wanke Jamila

                  Uba bai sai gado ba

                  Na za ka na tara kaya

                  Shahwa’atu taf faɗa kaya

                  Tac ce ko ɗai ba ya saura

‘Yan amshi:         Muhammadu Danlarabawa

 

Jagora:                  Nic ce in ke canye kaya

                  Ga mata na kiɗa na turmi

                  Wasu had da kwarya

                  Suna ɓacin ki, ni kau

                  Gwamma nike yaw waziri

                  Allahu ya taimake ni

                  In nit tahi bege na Allah

                  Sai na shiri na tallata ki

                   (Gwamma Maibege: ‘Waƙar Shahwa’atu’).

Idan aka dubi waɗannan ɗiyan waƙa da aka kawo daga waƙoƙi daban-daban za a ga kowannensu yana ɗauke da turken sayar da kaya da mutane ke yi a lokacin yunwa domin a sayi abinci. Wannan kuwa alama ce ta talaucewa.

2.5 Ƙaura

A lokacin yunwa mutane kan yi ƙaura daga wuri zuwa wuri, musamman ana barin inda rashin abinci ya fi tsanani zuwa wurin da ake ganin an fi wadatarsa. Galibi mutanen da ke arewa sun fi yin ƙaura zuwa kudu. Ba abin mamaki ba ne ko kaɗan don waƙoƙin yunwa sun ƙunshi irin wannan hali don kuwa abu ne da ke faruwa a zahiri. Tabbacin samuwar irin wannan ya zo ne a cikin waƙar Amali Sububu ta ‘Mai batun yaƙi da Sabra’, inda yake cewa:

Wanga irin baƙin zamani Allah kiyaye

Wasu na ta tashi suna tahiyassu Gwambe

Mu kam mun tsaya nan muna gyaran gidaje

In mun cimma gyaranta ba tashi mukai ba

In ta ɓaci ko Singa ga ba ta rigyam mu Bima

           

A nan Amali ya nuna hali na mutane suna ƙaura zuwa Gombe to amma su kam ba su tafi ko’ina ba, amma idan lamari ya ƙara tsananta to su ma bisa kafafunsu suke na yin ƙaura. Ita ma Gwamma Maibege Iyaka, cikin waƙarta ta Muɗa tana cewa:

Tac ce ina maza manoma gero

Ina maza manoma dawa

Ƙaƙa ƙara ƙaƙa kun ji

Kun gani tsuma, bulala

In rimbiɗe ku in rabke ku

In lalabo ku in koro ku

In gargaɗo ku duk ku yi Bauci

Ita ta muɗa marar alabrka

 

Da tag gargaɗo maza suka watce

Waɗansu sun wuce Tadurga

Dibo waɗansu sun kai Kanya

Wasu ko na Magajiya sun zauna

Wasu ko sun wuce a Dirin Daji

Duk korenta na marar albarka

Ta yamutce maza sun watce

Ta ce ta yi rantsuwa da ikon Allah

Wani sai lahira da shi da gidansu

 (Gwamma Maibege Iyaka: waƙar Muɗa).

A waɗannan ɗiyan waƙa, Gwamma ta mutuntar da yunwa cewa ta yi wa maza bulala ta kuma gargaɗo su duk sun haura zuwa ƙasar Zuru. Ta ma rantse wai wani da shi da dawowa gidansu sai lahira. A wani ɗan waƙa har wa yau, Amali Sububu ya kawo irin wannan zance na yin ƙaurar jama’a a lokacin yunwa musannan yunwa ‘Yar Buhari wadda aka yi fama da ita a shekara ta 1984, zamanin mulkin soja ƙarƙashin jagorancin Janar Muhammadu Buhari. A ciki yana cewa:

Yunwa ta taho da gorori

Ta iske maza

Duk ƙaton da taƙ ƙuma ga wuya

Sai ya shantala

Sai ya hurce Kwantagora

Dan nan ta waiwayo

Ta ga katon da bai ɗaga ba

In taƙ ƙumai bugu

Wajjen yamma za ya sauka

 

‘Yan amshi:         Riƙa da gaskiya

      Rana ba kashi ta kai ba

      Yari ɗan bangi rana ba ta sa ka rama.

 

Jagora:      Ga hwa kudun muna ta yi

Amma ba a yin arewa

       (Amali Sububu: ‘Waƙar Noma ba ya sa ka rama’).

A cikin wannan ɗan waƙa, Amali ya kawo yadda yunwa take korar maza, ta tarwatsa su, su warwatse zuwa wurare daban-daban don neman sauƙi a wurin da ake gani ana iya samunsa. A nan Amali ya mutunta yunwa ya ce tana ɗaukar gora ta riƙa dukar maza. Duk wanda ta duke shi komai zamansa ƙato, sai ya sheƙa a guje, ya yi ƙaura zuwa kudanci, wasu har sai sun zarce Kontagora a jihar Neja. Idan yunwa ta sake waiwayowa, duk wanda bai ƙaura ba, shi za ta sake doka, idan ta sha shi gora, yamma zai dosa, ya yi tasa ƙaurar.

Kammalawa

 Wannan muƙala ta yi ƙoƙarin duba irin halaye na ƙunci da rayuwa kan sami kanta a zamantakewar Hausawa musamman a lokacin yunwa wadda kan faɗa ƙasar Hausa lokaci-lokaci sakamakon rashin wadatar ruwan sama da kuma talauci da ya yi wa al’umma katutu a wannan ƙasa. Muƙalar ta yi waiwaye ne kan irin yadda zamantakewar kan sauya daga abu kyakkyawa zuwa mai muni a duk lokacin da al’umma ta jarabtu ta bala’in yunwa. Waɗannan halaye kuwa an zaƙulu su ne kamar yadda wasu mawaƙan baka suka ƙyallaro su, suka kuma bayyanar da hotonsu a cikin waƙoƙinsu daban-daban.

 Kamar yadda aka faɗa, waɗannan abubuwa ko halaye ba abin da zuciya take muradi ba ne. Hasali ma abubuwa ne masu ɗarsasa zuciya. Da yake rayuwa juyi-juyi ce, in ji kwaɗo, wai da ya faɗa ruwan zafi, ba illa don an yi waiwaye a kansu tun da mawaƙan sun ga dacewar ambaton su a cikin waƙoƙinsu, ba abin da zai hana mai nazari ya zaƙulo su a cikin waƙoƙin. Waɗannan misalai da aka kawo daga wasu waƙoƙi, ba iyakacin su ke nan ba amma dai duk da ba a kawo su duka ba, muƙalar ta yi nasarar tsokaci a kan matsalolin zamantakewa da ake samu a lokacin yunwa kamar yaudara da sata ko rashin gaskiya, da yadda mutane suke talaucewa, su karar da abubuwan da suka mallaka domin sayen abinci, da yadda ake samun yawan kisan aure, da yadda ake samun rayuwa ta kaɗaici wanda ke haddasa rowa, da kuma uwa uba yadda mutane suke yin ƙaura zuwa inda suke sa ran za su sami abinci. Wannan ƙaura ana yin ta ne, wani lokaci ba tare da iyali ba. Wannan kuma sai ya haddasa wasu matsalolin na daban.

 A ƙarshe wannan muƙala tana kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohi da su ɗauki matakai na tallafa wa manoma ta hanyar samar masu da isasshen takin zamani mai rahusa, da kuma ba su tallafi na kuɗi ko da bashi ne marar ruwa, wanda za su biya ko da da kayan gona da suka yi rara ne. Haka hukuma ta sayi kayan amfani gona daga hannun manoma a lokacin kaka, a farashi mai armashi ta yadda za a kare lagon ‘yan baranda. Wannan zai taimaka matuƙa wajen rage aukuwar yunwa, da rage talauci a tsakanin al’umma.

 

Manazarta

Tuntuɓi mai takarda.

Post a Comment

0 Comments