Ticker

6/recent/ticker-posts

Gaskiyar Magana


Wannan waƙa na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin da “Fasihi Usman Mai Riga Jega” ya rubuta. Usman matashi ne da Allah ya zuba wa basirar gudanar da abubuwa daban-daban. Ciki har da baiwar rubuta waƙoƙi masu matuƙar ilimantarwa da faɗakarwa. Yana zaune a garin Jega da ke jahar Kebbi a Nijeriya.

Usman Mai Riga Jega
07067998315
Mairigajega@gmail.com
Gaskiyar Magana

1. Allah sarki kai ke bayar da baiwa,
 Ga wanda ka so ba mai hanawa.

2. Fiyayyen halitta Annabin rahama,
 Wanda duk ya bishi ya yi dacewa.

3. Zuciya kamar shuka ce ku duba,
 In ba ruwa tabbas ai tana bushewa.

4. Ido fa da kunnuwa ba sa da amfani,
 Dubi matukar zuciya ba ta yin kulawa.

5. Rayuwar duniya sai fa an bita sannu,     
 Wasu har yau dai sun ka sa ganewa.

6. Hankali in 'Dan'adam ba ya da shi,
Wallahi kamar dabba ya ke komawa.

7. Tsuntsu ai kukansa dama jawani ne,
 Amma sai masu hankali ke ganewa.

8. Kar ka yi ƙunci sosai komai ka rasa,
To dubi ko duniyar ma ta na ƙarewa.

9. Tabbas ko ka yi abin azo a yaba ma,
 To wallahi wasu sam ba su yabawa.

10. Soyayyar zamani ta na bani tsoro,
 Mafi yawa yaudara ce ake tafkawa.

11. Mata da mazan dukkansu na duba,
 Gaskiya yanzu kowa ana cutawa.

12. Wata sai ta tara samari sun fi goma,
Koma ba wanda za ta aure muguwa.
      
13. Hakama iyaye halinku akwai tsoro,
Kun manta aikinku mai tarin yawa.

14. Tarbiyyar yaranku na ke ta yin duba,
Yanzu wallah na duba ba ku kulawa.

15. Au, bari na koma kan shugabanni,
 Waɗanda Haƙinmu sun yi dafewa.

16. Mutuwa gaskiya ce ba batun wasa,
 Tun yanzu ku gyara halinku 'yan'uwa.

17. Shugabanni na ke kira bana rufewa,
 Mai faɗin gaskiya shi ake kamawa.
       
18. Kun san akwai damar magana na jiya,
 Shin wai ko shafin dai an yi shafewa?

19. Ɓarawon kaza an masa dukan tsiya,
 Na miliyoyin Kuɗi shi an yi ƙyalewa.

20. Ɗan maikuɗi shi ba ya da hukunci,
 Ko da ko ya kashe mutune ɗarurwa.

21. Shi fa mai waƙa burinsa a yi nazari,
Usman nake Maula ai ba ni farawa.

22. Ya Ɗan'adama ke rayuwa ba hutu?
 Kai ni wallahi ina tausan talakkawa.

23. Su Zaɓe ka ka bar su cikin damuwa,
 Kana ta hutu kowa ba ka ma kulawa.

24. Kai! Bari na tsaya kar raina ya ɓaci,
 Abin kam Wallah akwai fa damuwa.

25. Usman Mairiga haka ne ake kirana,
 'Dan Jega nake ni ne mai gidan Arawa.

26. Godiya a gun sarkina ai mai duniya,
  Har lahira fa shi ne shugaban kowa.

Post a Comment

0 Comments