Ticker

6/recent/ticker-posts

Shaye-ShayeWannan waƙa na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin da “Fasihi Usman Mai Riga Jega” ya rubuta. Usman matashi ne da Allah ya zuba wa basirar gudanar da abubuwa daban-daban. Ciki har da baiwar rubuta waƙoƙi masu matuƙar ilimantarwa da faɗakarwa. Yana zaune a garin Jega da ke jahar Kebbi a Nijeriya.

Usman Mai Riga Jega
07067998315
Mairigajega@gmail.com
Shaye-Shaye

1. Allah mai shiryar da kowa na ke roƙo,
Ya tsareni sharrin maƙwabta bata gari.

2. ka iyamin duk aikin da na sa a gabana
Ka sa na tsare sallah da ni yawan zikiri.

3. Ka yi salatinka ga manzo maras dadi,
Masoyina kowa yasan shi ba ya fahari.

4. ka hada iyalansa da sahabban nasa,
Ƙaunarsu na ke mai zagi ai ba na uzuri.

5. Tabaraka Sarkina ka zuba min basira,
Akan Waƙar ga ni da na ke ta yin ƙudiri.

6. To Bari dai in sauke abin da na nauko,
Ni shi ke damuna akan sa na ke nazari.

7. Ni illar shaye-shaye na ke so mu duba,
Wallahi shi ke kawo yawan bala'i a gari.

8. Amfanin shaye shaye ni ban gane ba,
To shi ake yayi yanzu ƙauye har da gari.

9. An ce ku daina kun ce ku kuna ra'ayi,
Ga shi har ya kai wasunku cikin ƙabari.

10. Wasu ko gasu can an kulle a gida,
Ana dukansu gasu an ɗaure su da mari.

11. Wasunku da girman su ba sa azumi,
Kuma ba sa sallah ta farilla ballai witiri.

11. Girmanku na banza ne kam na lura,
Ina ganinku da ƙima lallai can dori.

12. shaye-shaye ya sa kun fada lahani,
Iyayenku na kallonku kuna yin garari.

13. Wani har a gidan su yake yin mayen,
Har da maƙwabta na jin mugun ƙauri.

15. Matsayinka kamar dabba ne ka sani,
Kai dubi ko dabba ya fika samun katari.

16. Lallai gobe mala'iku sai sun kama ka,
Don ba ka yin sallah kuma ba ka zikiri.

17. Shaye-shaye fa ke jawo yawan roƙo,
Kuma shi ke kawo sata ni da nai nazari.

18. Kuma mutuwar aure yana kawowa,
Da zinace-zinace ina so ku yo nazari.

19. Zance na a fili yake fa babu musawa,
Wasu ma'aikata ai sun zama ɓata gari.

20. Kai! Allah wadaran na ka ya lalace,
Dubi har da kuma yanzu ake yin bidiri.

21. Ni da na aurar da ƴa ta ga mashayi,
Ni kam gwara na shekara biyu da mari.

22. Kar ku ce wai shaye-shaye jarabtace,
 In ma haka ne ai magani shi ne haƙuri.

23. Zancen da na ke fa abin dubawa ne,
Shaye-shaye ba alkhairi ni na yo nazari.

24. Domin Allah da Manzonsa ba sa so,
Lallai mai yi ku tabbata ya faɗa haɗari.

25. Ku duba mashaya da yawa na duka,
Wannan zancen tabbas ya zarce ɗari.

26. Wasu ma kai sun kashe iyayen na su,
To ai maganar ta zagaye ƙauye da gari.

27. kuma ku ji tsoron yawo da mashayi,
Don ko mai yi wataran zai faɗa haɗari.

28. Ni da in bi hanya ɗaya da mashayi,
Na gwamace ace Usman zaga gari.

29.Ni fa da in dauki mashayi aminina,
To ni na fi so in saɓa babban alƙawari.

30. Da in ci abinci da ɗan shaye-shaye,
Ya dai yi haƙuri ko sunansa Abubakari.

31. Hanyar daina shaye-shaye zan faɗa,
Farko dai sai da yin kyakkyawan ƙuduri.

32. To ku rin ƙa roƙon Allah koyaushe,
Sannan da yawan sauraren tafsiri.

33. Ciwon zuciya kai har ciwon ƙuda,
Mashaya ai anan ne sun ci gari.

34. Dubi abin da ke bugarwa maye ne,
To wannan hadisi ne ba mai yin inkari.

35. Kuma ku share duk abkkai ƴan'iska,
Roƙona Allah ya ba ku wasun na gari.

36. Tammat bari in tsaya waƙar in huta,
Laifi in na yo muku ku yo min uzuri.

37. To ni Usman mairiga ake ce min,
Kuma Jega lallai ita ce na mu gari.

38.To ya sarkinmu mai yawan kariya,
Ka rabamu da abokai ɓata gari.

Post a Comment

0 Comments