Wannan waƙa na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin da “Fasihi Usman Mai Riga Jega” ya rubuta. Usman matashi
ne da Allah ya zuba wa basirar gudanar da abubuwa daban-daban. Ciki har da
baiwar rubuta waƙoƙi masu matuƙar ilimantarwa da faɗakarwa. Yana zaune a garin Jega da ke jahar Kebbi a
Nijeriya.
Usman Mai Riga Jega
07067998315
Mairigajega@gmail.com
Auren Dole
1.To Bismillah Allah zan fara
Taimakeni laifukana in
gyara,
Masoyana ina muku bushara,
Yau wata waƙa ce ni na tsaro.
2.To ku bari dai in fara salatina
A wurin Manzona mai
cetona,
Alihi da sahabbansa
masoyana
Wajibi ne in zan waƙa sai na
jero.
3.Kuma bayanina akan Auren dole,
Shin Matsalar ta ina ne ta ɓalle?
Ku biyoni ku ji ku daina ta
tsalle,
Yau zan cire tsakuwa a
cikin gero.
4.Ku ma kun san fa auren dole illa ce
Laifin daga iyaye ne, ni
haka zance,
Ko da fa akwai zumunci zai
lalace,
Shi ne ke sa yarinya yawon
kwararo.
5.Komai kuɗinka Wata
ai ba ta sonka,
Kan auren dolen ta na iya
yankeka,
Kai za ta iya cin mutuncin
iyayenka,
In ba a sonka to ka daina
nuna taro.
6. Da mai sonka da mai ƙin ka wa ya fi?
Ashe dai ni kam ku zan
azawa laifi,
Kun jefa kan ku cikin rame
mai zurfi,
Wallahi wanga wauta ce ko
ga yaro.
7. In ka Aureta ba ta ganinka da ƙima,
Ballai ta yi sauri Abinci
ta girka ma,
Ai kodayaushe za ka ganta
da rama,
Ba ta ba ka ruwan kofi ballai
na faro.
8. To shi ke sa yarinya ta kashe kanta,
Don tunaninta fa shi ne ƙaɗai mafita,
Ta ce ba ta so iyayen sun ƙi
fahimta,
Iyayen ke gargaɗinta duk ta zaburo.
9. Dubi wurin kwanciya sai ta jayema,
To daga nan wani bala'i zai
soma,
Ai tamkar mahaukaci za ka
koma,
Sarkin ƙarfi ai ba ya kai sarkin taro.
10. Matsalolin kam ai suna da yawa,
Auren dole shi ne baƙar
haduwa,
Wallahi ba nisa auren ke rabuwa,
Ko da an yi Addu'a an raba
goro.
11. Kar dai in ce Auren haramun ne,
Amma ina ta kiranku ya
mutane,
Ku bar Auren dole don wauta
ne,
Mata da Maza zancena a
sauraro.
12. Ta silarsa Yarinya ta na shan duka,
Koda da cikinta wallahi ba
shakka,
In ba sonka wallah kar ma ka ɗauka,
Don da ka Aureta gwara kana gwabro.
13. Dubi fa ga wanda ta ke so a zuciya,
An ɗauketa an ba wawan duniya,
Kai shi ma ya san babu zama
lafiya,
In dan kuɗi ne to wallahi daina doro.
14. Tabbas Aure ni'ima ce
mai yawa,
Ta silar Auren dole fa ba
a ƙaruwa,
Ko ciki ta samu ta na iya
zubewa,
Ni fatana in an yi aure a
samu yaro.
15. Wata ba ta ko gaisawa da iyayenta,
Domin ko sun cuci duk
rayuwarta,
Amma su gani suke sun yo
bajinta,
Soyayya haɗin Allah
ce dubi sauro.
16. To fa duk da ni ilimina bai da zurfi,
Mai haɗa Auren
dole ai ya yi laifi,
Domin da hauka ai ba a kama kifi,
In har ba ta so kar ma a
sayi goro.
17. Wata fa ba ta ko kwana gidan miji,
Kar ma kuce ta saɓawa Ubangiji,
Kai gare shi ma take neman
agaji,
Alƙali
shawarata dai a ɗauko
biro.
18. To Alƙalai ku kashe fa Auren dole,
Da Sarakuna to matsalar ku
kulle,
Malammai duk ku zo ku daddale,
To ku ɗauki
maganar wanga yaro.
19. To Usman Mai Riga ni ake kirana,
Kun dai ji Matsalar da ke
damuna,
In an ka gyara wallahi zan
yi murna,
Alhamdu lilah ta soyayya na gangaro.
20. Zan tsaya nan Ɗan Jega na yi godiya,
Gun Sarkina mai kyauta ai
duniya,
Wanda ya sanya a Jikinmu
soyayya,
Allah ka sa Usman na zamo
tauraro.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.