Wannan waƙa na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin da “Fasihi Usman Mai Riga Jega” ya rubuta. Usman matashi ne da Allah ya zuba wa basirar gudanar da abubuwa daban-daban. Ciki har da baiwar rubuta waƙoƙi masu matuƙar ilimantarwa da faɗakarwa. Yana zaune a garin Jega da ke jahar Kebbi a Nijeriya.

Usman Mai Riga Jega
07067998315
Mairigajega@gmail.com
Magada Annabawa

1- Rabbana kareni a cikin dare,
  Ko da rana kar in sha wuya.

2- To bani iko ya sarkina gwani,
Don ban da kamarka a duniya.

3- Yau zan yi waƙata yar Zamani,
 Domin abin da ke cikin zuciya.

4-  Salatin Manzona ni shi na riƙe,
 Koda yaushe da shi nake godiya.

5- Alihi da sahabbai ai suna biye,
Dukkansu ina son su a zuciya.

6- Malammai waƙar nan fa ta ku ce,
To sai ku karɓa ban da hayaniya.

7- Kar ku damu yanzu zan bayyana,
Tunda wasu sai sun yo tambaya.

8- To malammai ai ku ne ginshiƙai,
Tunda An ce ku ne Magada Anbiya.

9- Duniyar ga da ku ake yi lallai ko'ina,
Kar ku yarda ku ɗau son zuciya.

10- Kar ku yarda zuga ta kifar da ku,
Kunga ƙarshe a sakaku a hawuya.

11- Da'awa ita ma sai ku yo da kyau,
Harshenku please sai ku tausaya.

12- Ku ne ke cewa ai tuni Allah ya faɗa,
Kar a same ku cikin wai kun antaya.

13- Masu zaginku kuma ku yi Haƙuri,
Don kun kasance a tsaka mai wuya.

14- To fa ai Allah ne ya Aza muku shi,
Kar ku bar shaiɗan zai muku dariya.

15- Kun san wasu sam ba su da hankali,
Ba illimi sannan ba sa yin tambaya.

16- Kai kar ku zam masu yin jiji da kai,
Don Allah fa baya son mai fariya.

17- To wanda duk ke zagin mallamai,
 Ai don aƙida ne ko kuma ƙungiya.

18- Laifin wani sam baya shafar wani,
 Ayar Alƙur'ani ku je ku mu bibiya.

19- Wasu aikinsu ƙazafi ga mallamai,
 Kai musamman ma social midiya.

20- San da duk malami yai kwalliya,
  Sai su ce kai Malam ya cika fariya.

21- Matuƙar Ko Malam na da Arziki,
 Sai suce lallai da Alamar tambaya.

22- To in har Malam Motoci gareshi,
 Sai su ce wai Malami ake wa jiniya?

23- Malami in da'awa ya je a ƙasar waje,
 Garesu Malam ba ya zama Najeriya.

24- Su ce ba ya saye kuma bai saisuwa,
Kuɗinmu da su yake ta sharholiya.

25- To in ko Malam ya yo musu raddi,
 Sai su ce ai an yi dubunka a Duniya.

26- Na ga Malam an zagai a gidansa,
 Wallah zagin kuma mai taɓa zuciya.

27- Waƙata Ban cire kowa a cikinta ba,
 Amma kuskurena ku yo min yafiya.

28- Wallahi falalar ilimi kam tai yawa,
 Banda ilimi ballaima ku yi tambaya.

29- To ashe neman ilimi lallai da ƙyar,
Duk wanda ke so sai ya yo juriya.

30-  Wanda duk ka gan shi fa da illimi,
 Rayuwarsa ta baya je ka yi tambaya.

31- Don Allah Mallammai ku yi hankali,
Wallahi Ku ji tsoron wannan Duniya.

32- Na san komai zan faɗi ai kun sani,
Haka yassa ni zan ɗan tsaya.

33- Gafara nake nema gun Sarki gwani,
 To ya Allah ka gyara muna zuciya.

34- Usman Mai Riga sunan mai batun,
 Jega can nake gun mai Tambaya.

35- Ma sha Allah tammat waƙa ta cika,
 Ai da iyawar Sarkin nan mai kariya.