Wannan waƙa na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin da “Fasihi Usman Mai Riga Jega” ya rubuta. Usman matashi ne da Allah ya zuba wa basirar gudanar da abubuwa daban-daban. Ciki har da baiwar rubuta waƙoƙi masu matuƙar ilimantarwa da faɗakarwa. Yana zaune a garin Jega da ke jahar Kebbi a Nijeriya.

Usman Mai Riga Jega
07067998315
Mairigajega@gmail.com
Kukan Kurciya

1- To ya sarkina ka bani sa'a,
    Akan waƙar ga da za ni ƙago.

2- Kullum salatina wurin Ma'aki,
    Ɗan Abdallah gun mu shi ne jigo.

3- Duk ko wanda ke zagin Sahabbai,
    Ranar mutuwarsa ransa za a fisgo.

4- Dubi yaro mai Abin mamaki ne,
    Don wata rana shi ne ke zama Ango.

5- Kai! Yaro wallahi miƙe ka bar fashi,
   tabbas ai haushi na gun uwar Raggo.

6- Lallai mai son ka shi ne ke ta begenka,
    Domin shi so na can cikin ɓargo.

7- Kun san fa Amarya dole ta yo ƙunci,
   Matuƙar yau aka ce babu ran Ango.

8- Tabbas abin mamaki yana da yawa,
    Yau mai nama ya zagi mai mango.

9- Ai kun san kurin wada na banza ne,
   Dubi shi ma ya san ba ya kai dogo.

10- To Matuƙar ko in za a yo layya,
      An faɗa an fi so kowa ya sai Raago.