Ticker

6/recent/ticker-posts

Abin Mamaki Dangane da Abinda Jiki ke ji "i"


Ko kun san cewa akasarin kalmomi da kuke jin yanayinsu kama daga: 
1. Harshe/ Maƙogoro
2. Fatar jiki
3. Hanci
4. Zuciya/ ƙwaƙwalwa

Duk ƙarshensu na ƙarewa ne da wasalin /i/?

To amma ga misalai kaɗan a nan 

A hanci ana jin

1. Wari
2. Ƙamshi
3. Ɗoyi
4. Zarni
5. Hamami
6. Gafi
7. Ƙarni

A harshe/Maƙogoro ana jin

1. Ɗaci
2. Tsami
3. Zaƙi
4. Bauri
5. Garɗi
6. Maƙaƙi

A fatar jiki ana jin 

1. Sanyi
2. Zafi
3. Ɗari
4. Turiri
5. Ƙaiƙayi
6. Raɗaɗi
7. Tsanani
8. Sauƙi
9. Ɗumi

Sai kuma waɗanda ake jinsu cikin zuciya ko ƙwaƙwalwa. Kamar

1. Daɗi
2. Haushi
3. Takaici.
4. Ƙyanƙyami
5. Ɗoki
6. Marmari.
7. Shauƙi
8. Nishaɗi
9. Fushi 
10. Tunani,    da sauran su. 

NB.
Ban ce ba za a iya samun wasu kalmomin da suka saɓa da wannan tsarin ba. Amma dai  yawanci na ce. Na gode.

Mallaka: Hausa Club

Post a Comment

0 Comments