Maƙalar da aka gabatar a taro ƙara wa juna sani wanda Cibiyar Nazarin Hausa, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato ta shirya a ranar 19 ga Satumba, 2012.
Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan Ph.D
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
E-main: ibrasskg@gmail.com
Lambar Waya: 0803 6153 050
1.0 GABATARWA
A duk lokacin da mutane suka aminta su zauna a wuri ɗaya kuma su gudanar da rayuwa bai ɗaya to za su samar da waɗansu hanyoyi na gudanar da wannan rayuwar gwargwadon bukatun su ko kuma irin fahimtar da suka yi wa rayuwar. Haƙiƙa duk wani tunani da al’uma za su yi na shimfiɗa rayuwarsu ba zai rasa dalili na wasu fa’idoji ko alfanu da za su samu ba. Hakan kuwa yana iya kasancewa wata kariya ce gare su ko kuma waraka daga wani abu da yake muzguna musu. Nazarin irin wannan rayuwa yana ba da damar fito da hikimomin da ke ƙunshe a cikin su ko da kuwa ba shi ne ainihin dalilin samar da wannan al’adar ba.
Maƙasudin wannan nazari shi ne ƙoƙarin fito da falsafar da ke ƙumshe a ɗaurin auren Maguzawa. ɗora al’umar Maguzawa a wannan nazari yana da alaƙa da tunanin cewa, ɗaurin auren nasu ya yayo abubuwa masu jan hankali da sosa zuciya da mamaki musamman da yake sun saɓa wa abin da aka saba da shi na ɗaurin auren Hausawa (Musulmi). Wane irin tunani ke cikin ɗaurin auren na Maguzawa? Wannan ita ce tambayar da wannan nazari ya yi ƙoƙarin amsawa.
2.0 FASHIN BAƘI
A taken wannan nazari, akwai wasu muhimman kalmomi guda biyu da suke bukatar sharhi ga mai karatu. Wannan fasalin zai yi ƙoƙarin fashin waɗannan kalmomi domin a bayar da haske.
2.1 Ɗaurin Aure:
Wata al’ada ce mai muhimmanci da ake gudanarwa a al’umomi da yawa na duniya wadda ke bayar da damar sakewa don kawar da sha’awa da taimakon juna tsakanin mace da namiji. Ita wannan al’adar takan bukaci gudanarwar mutane baya ga mace da namijin da suke son ƙulla wannan dangantakar. A taƙaice, haɗuwa ne na mutane da ake yi don a gudanar da wasu ayyuka da za su haɗa mace da namiji a matsayin ma’aurata, saɓanin zamantakewar dabbobi. ɗaurin aure, ginshiƙi ne da ya fi kowane muhimmanci daga cikin ginshiƙan aure wanda rashin sa yana iya haifar da matsaloli da gurɓacewar nasaba.
2.2 Maguzawa:
Su ne Hausawan asali waɗanda ba Musulmi ba, masu gudanar da rayuwarsu ta hanyar bin tanadin da aka yi a al’adunsu da addininsu na gargajiya. (Krusius 1915, Fletcher 1929, Ibrahim 1982, Yusuf 1986, Kado 1987, Safana 2001, Akodu 2001, Malumfashi 2002, ….)
3.0 ƊAURIN AUREN MAGUZAWA
Ɗaurin aure shi ne matakin ƙoli daga cikin matakan auren Maguzawa. Aure bai taɓa ƙulluwa da kuma karɓuwa a al’umar Maguzawa ba tare da an yi shi ba. Don haka, al’ada ta yi masa kyakkyawar tanadi. Maguzawa sukan yi ɗaurin aure ne a ƙofar gidan iyayen amarya. Abin alfahari ne a ɗaura wa mace (budurwa) aure a ƙofar gidan iyayenta maza. Haka kuma dattijai masu shekaru daga cikin dangin uba su ke da alhakin ɗaura wa budurwa aure.
Sa rana na daga cikin shirye-shiyen ɗaurin auren Maguzawa. Akan sa rana ta musamman wadda ake ɗammahar mutane za su sami sukunin halarta. Kaiwa ga matsaya dangane da ranar ɗaura aure yakan biyo bayan shawarwari ne tsakanin iyayen amarya da masu alhaki daga dangin ango. An fi yin irin wannan buki a lokacin rani, wato lokacin da ba a ruwan sama, kuma ba a aikin gona.
Ba kamar wasu al’adu na Maguzawa ba, ɗaurin aure sake yake ga duk mai sha’awar halarta maza da mata, babba da yaro. Wannan ne ya sa ake yin sa a fili, gindin wata itaciya ko itatuwa. Tsarin zama a wajen ɗaurin auren Maguzawa bai ba da damar kowa ya zauna inda yake so ba. Mata sukan zauna gefe ɗaya, dattijai maza gefe ɗaya, samari ɓangaren su daban, yara kuma da nasu gefen. Dangane da lokaci kuma, an fi yin ɗaurin auren da rana, duk da yake akan sami masu yi da safe ko bayan rana ta faɗi.
Da yake taro ne na buki da farin ciki, iyayen amarya sukan tanadi abincin da za a ci da giyar da za a sha wajen wannan bukin. Haka su ma dangin ango sukan zo da abinci iri-iri waɗanda za a ci baya ga abubuwan da al’ada ta ɗora musu na kayan ɗaurin aure. Duk wanda ke da wata alaƙa ta jini ko ta sanayya da amarya ko ango sukan nuna ƙarfin dangantakar ne ta hanyar kawo gudunmuwa na abinci ko dabbobi a lokacin irin wannan bukin. Abin alfahari ne ga Bamaguje a ci abinci da nama har a bari a muhallin ɗaurin aurensa.
Kayan Ɗaurin Aure
Al’adar Maguzawa ta yi tanadin kayayyaki daban-daban waɗanda ake ɗammahar iyayen ango (waɗanda za su karɓar masa aure) su zo wannan muhalli da su ko kuma a kawo su kafin ranar ɗaurin auren (gwargwadon tanadin da al’ada ta yi). Waɗannan kayayyaki sukan bambanta daga wuri-wuri. Ga misali wasu muhallan Maguzawa a jihar Katsina:
MUHALLI
|
KAYAN ƊAURIN AURE
|
Maguzawan Ƙwanƙi
|
Sukan bukaci a kawo tulunan giya da ’ya’yan gauɗe. Idan uban amarya ya riga ya mutu to za a ce su zo da ɗan akuyar maraici. Haka kuma in uwa ta mutu to, akuyar maraicin za a kawo.
|
Maguzawan Lezumawa
|
Giya ake kawowa da tabarmi da kuma goro in akwai. Haka kuma idan ba kuɗi ana iya biyan dukiyar auren da akuya.
|
Maguzawan Gidan Bakwai
|
Sukan nemi a zo da kaji huɗu. Daga cikinsu a sami jan zakara da jar shirwa, da kaza mai jan gaba. Haka kuma za su zo da rago mai kwalli. Waɗannan dabbobi ba za a yanka su ba sai bayan amarya ta tare da kwana bakwai. Za a yi abinci mai yawa. Ba wanda zai ci sai amarya da ango sun ci sun ƙoshi sannan a kawo wa sauran jama’a.
|
Maguzawan Gidan Gwarzo
|
Idan iyayen yaron maharba ne za su zo da gatari da ’yar baka na ƙarfe. Haka kuma za a zo da tunkiya wadda take a matsayin dukiyar aure. Bayan kwana biyu da ɗaura aure ake yanka tunkiyar a yi abinci a ba jama’a su ci. Za a zo da kaji guda biyu da ɗan akuya. Idan amaryar gidansu tsafin Bagiro ake bauta wa, za a ce dangin ango su zo da ɗan akuya daban. Wannan ɗan akuyan na tsafin gidan ne. Haka ma za a kawo wani ɗan akuya daban wai na riƙon gida. Wannan ɗan akuyar shi za a yanka, amarya ta ƙetare jinin a daidai ƙofar gida a lokacin da za a kai ta gidan miji.
|
Maguzawan Gidan Bakori
|
Iyayen ango za su zo ɗaurin aure ne da tulu huɗu na giya da awaki guda biyu da kaji guda biyu da dukiyar aure da kuɗin kalwa da kuɗin mai. Awakin nan da kaji na dangin uwa da dangin uba ne.
|
Maguzawan Kaibaki
|
Tunkiya suke karɓa a matsayin dukiyar aure. Uwa maƙunshiya za a ba ta akuya, haka shi ma uban riƙo. Za a kawo lèfé na kaba da akuya ɗaya wadda za a yanka amarya ta ƙetare jinin.
|
Maguzawan Kainafara
|
Za a kai baƙin ɗan akuya da sabon másássábí da kibiya biyu. (ɗaya mai kunne biyu, ɗayan kuma mai kunne ɗaya) da tulunan giya huɗu zuwa goma sha biyu. A hannun uban amaryar waɗannan kaya za su kwana kafin ranar ɗauri aure.
|
Fuskokin da Lafuzzan ɗaurin Auren Maguzawa
Bambancin wurin zaman Maguzawa yakan kawo ’yan sauye-sauye ga yadda ake ainihin ɗaurin auren. Wannan ne ya samar da fuskoki daban-daban na yadda ake tabbatar da mallakar mace ga namiji a matsayin matar aure. Ga wasu daga ciki.
3.2.1 Amfani da Ƙasa
Bayan jama’a sun taru ana ta cin abinci ana ba’a, can da rana sai a kira wakilan ango da na amarya su nemi aure. Bayan tsohon da zai ɗaura auren ya tabbatar sun nema an ba su, kuma sun kawo duk kayan da al’ada ta tanada, sai ya tara ƙasa a wuri ɗaya. Ya sami wata ‘yar sanda ya riƙe. Zai ɗaga murya yadda kowa zai ji, ya ce:
“Ni Wane (ya ambaci sunansa) na ɗaura auren Wane da Wance in ga ɗan babban bura-uban da zai raba.”
Sai ya bugi ƙasar nan da sandar da ke hannunsa tim. Haka zai yi har sau uku. Yana ƙarewa sai a yi guɗa a ci gaba da shagali.
3.2.2 Ɗamar
Bayan dangin ango sun kawo kayan ɗaurin auren da aka bukata, za a sami wani dogon kara ko sanda a ba wani ya tashi tsaye ya riƙe. Tsohon da zai ɗaura auren yana zaune zai ce wa mai riƙe da karan:
Mai ɗaura aure:
|
Hango mini ’ya’ya.
|
Mai riƙe da kara:
|
(zai juya ya dubi arewa) Arewa ’ya’ya ga su nan sun taho zuwa ɗakin Wance (ya ambaci sunan amaryar). Wanda ya raba auren nan ya faɗa rijiya mai gaba ɗari.
|
Mai ɗaura aure:
|
Duba mini kudu.
|
Mai riƙe da kara:
|
(zai juya ya kalli kudu) Ka ga kudu ƙasa kaza, ga raƙuma nan sun taho zuwa ɗakin Wance.
|
Mai ɗaura aure:
|
Duba mini gabas.
|
Mai riƙe da kara:
|
Daga ƙasa kaza (ya ambaci ƙasar) ga arziki nan na zinare ya taho zuwa ɗakin Wance.
|
Mai ɗaura aure:
|
Hango mini yamma.
|
Mai riƙe da kara:
|
Yamma ƙasa kaza ga shanu nan sun taho zuwa ɗakin Wance.
|
Daga nan sai mai ɗaura auren ya ɗauki kibiya da ruwan fartanya ya buga su yi ƙara kyan-kyan-kyan, ya ce:
“Ni Wane (ya ambaci sunan sa) na ɗaura auren Wane da Wance ba ɗan kutumar babakeren babban buran uban da zai raba wannan auren sai wanda ya kwana da uwarsa. A nan duniya ba ta da wani miji in ba Wane ba.”
Yana faɗar haka sai a yi ihu, a yi guɗa a goce da kiɗa, a ci gaba da shagali.
3.2.3 Amfani da Kibiya ko Ruwan Fartanya
Bayan an gama cin abinci sai dattijai su haɗu a wata inuwa don a ɗaura aure. Za a gaya wa jama’a kowa ya natsu za a ɗaura aure. Sai wani tsoho daga cikin dangin amarya ya ɗauko kibiya ya buga a jikin ruwar fartanya ko ya saka ruwan fartanya a cikin ƙota/ɓota ya ce:
“Daram! Na ɗaura auren wane da wance in ga ɗan abu kazar uwar da zai raba.”
Yana faɗar haka sai mata su rausa guɗa, makaɗa su goce da kiɗa a ci gaba da kaɗe-kaɗe har wani lokaci.
Ƙalubalantar ɗaurin Aure
Idan aka lura, dukkan lafuzzan da aka yi amfani da su a fasalin da ya gabata zagi ne na fitar arziki. Ba mahaluƙin da zai haƙura idan an ƙunduma masa zagin muddin dai yana da hankali. A wasu lokutan akan sami wanda zai tara kai ya ɗauki zagin, ya ce ya raba auren. Nan take zai gaya wa jama’a dalilansa ta hanyar ambaton wani abin kunya da ya taɓa faruwa ga ɗaya daga cikin ma’auratan ko zuri’ar da suka fito. Misalin irin wannan abin kunyar sun haɗa da tarihin sata ko kwartanci ko ragganci da dai makamantan haka. Wasu sukan yi wannan yunƙuri ne na hana auren domin su huce takaicin rashin tuntuɓar su a lokacin hidimar neman aure ko tsayar da miji a matsayin su na ’yan’uwa. Haka kuma zai iya kasancewa wata dama ce mutum ke samu na bayyana ra’ayi musamman idan al’ada ta ƙargama masa takunkumin shigowa ko bayar da shawara. Da zarar dattijai sun bincika suka tabbatar da ƙorafin nasa, ana iya fasa auren, a sallami jama’a.
HIKIMOMIN ƊAURIN AUREN MAGUZAWA
4.1 Girmama Gabaci
A ɗaurin auren Maguzawa, dattijai masu manyan shekaru ko magabata daga dangin amarya aka aminta da su ɗaura aure. Wannan ya fito da muhimmamcin tunayin fifita yawan shekaru a wajen gabatar da duk wani lamari. Akwai fahimtar cewa, babba shi ya san jiya ya san yau. Shi ya kamata a sa gaba wajen gudanar da duk wani abin alheri muddin dai ana son ganin albarkar abu. Hausawa na cewa, ɓabban yatsa ko ba ya cin tuwo, ya iya ɓara malmala.
4.2 Fa’idar Zaɓen Muhallin ɗaura Aure
Ɗaura auren Maguzawa a ƙofar gidan iyayen amarya na asali wani ɗaukaka ne ga mace da nuna wa jama’a tana da asali kuma ba shegiya ba ce. A duk lokacin da Bamaguje ya ga ana neman ko shawarar wajen ɗaura aure, zai fahimci akwai lauje cikin naɗi. A taƙaice ba tabbacin kyakkyawar nasaba ga amarya.
4.3 Gitta Ashar a Lafuzzan ɗaurin Aure
Lafuzzan ɗaurin auren Maguzawa masu ɗauke da manyan kalmomin ashar (waɗanda ba Bamagujen da ke sha’awar a ƙunduma masa su) wata kariya ce ga ɗorewar auren. Duk wanda ya yi niyyar ƙulla wani makirci na raba auren saboda wani son rai ko ra’ayi, ya tuna da zagin da aka ƙunduma ko aka gitta, sai ya yi tunanin irin kallon da al’uma za ta yi masa na ɗaukar wannan ashar. Wannan tamkar wata kariya ce ga ɗorewar aure.
4.4 Isharar Haɗa Mace da Namiji
Duk da sanin Maguzawa a matsayin mutanen da ba su karɓi saukakken addini ba, wanda hakan ya sa suke bayyana al’amari kai tsaye, wannan bai sa tunanin su na kunya ya gushe ba. Maimakon a fito da amarya da ango tsirara a bainar jama’a a haɗa su don nuna an ɗaura aure, sai suka sakaya ta hanyar soka ruwan fartanya a cikin ɓota, ko kuma haɗa abubuwa biyu da za su nuna an haɗa mace da namiji. Ana iya kwatanta wannan da kimiyyar zamani. Misali idan ana son wutar lantarkli ta maka sai an haɗa wayoyi biyu waɗanda ake ɗauka a matsayin mace da namiji. A taƙaice dai wannan ishara da aka yi tamkar wani lasin ne aka ba mace da namiji don su kusanci juna ba tare da an zarge su da yin ɓatanci ba.
4.5 Damar Fito da Aibin Ma’aurata
Yanayin ɗaurin auren Maguzawa yana ƙunshe da wata hikima da ta bayar da dama ga dangi su fito ƙarara bainar jama’a don nuna aibin ma’aurata da ƙyamar haɗa zuri’a. Kamar yadda bayani ya gabata (3.3) wannan wata hikima ce ta tsarkake zuri’a da bayar da ’yanci ga dangi su tsoma baki a kan abin day a shafi ’yan’uwa na zumunci. Haka kuma irin wannan yakan taimaka wajen Kyautata halayen mutane da tsoron barin baya da ƙura.
4.6 Yi wa Dangantaka Fatar Alheri
A al’adar ɗaurin auren da aka kira ɗamar (3.2.2) an nuna wata hikima da nuna fatar alheri ga ma’aurata. Duk da yake kowa ya san ba abubuwan da aka hango za su zo ga ma’aurata ba, albarka ce ake nema na samun arziki da zuri’a da duk wani abin alherin a zamantakewar auren. Jahilcin Maguzawa bai ƙargama musu takunkumin rashin tunanin fatar alheri ga ma’aurata ba.
4.7 Koyar da Tarbiyya
Tsarin yadda ake zama a muhallin ɗaurin auren Maguzawa, wani darasi ne da ke koyar da tarbiyya a al’uma. Kowane rukuni na mutane an tanadi su zauna da sa’o’insu. A tunanin Maguzawa, ya saɓa wa hankali mata da maza su cakuɗe ana jin shirmen da ake furtawa musamman idan giyar da aka sha ta fara aiki. Wannan ya fito da tunanin nan na Hausawa da ke nuna kowace ƙwarya da abokiyar ɓurminta.
Damar Nuna Zumunci
Irin taruwar da ake yi a muhallin ɗaurin auren Maguzawa; da hidimar da ake yi da mutane musamman na tanadar musu abinci; da damar saduwa da ake yi da juna musamman mutanen da suka fito daga wurare daban-daban wata hanya ce ta ƙara danƙon zumunci. Haka kuma irin wannan haɗuwa yana iya ba da damar ƙulla wani zumuncin na aure ko ƙawance da dai makamantan su.
5.0 NAƊEWA
Ba gurin wannan nazari ba ne ya yi ƙoƙarin zaƙulo al’adun da ke takin saƙa da rayuwar Hausawa ta yanzu ba. Tunanin kawai a nan shi ne waɗanne hikimomi ke tattare da al’adar Bamaguje na tsara hidimomin ɗaura aure kamar yadda yake a gargajiyance? Sakamakon wannan nazari ya tabbatar muna da cewa, in ban da ’yan abubuwan da ba a rasa ba na lafazi, da shan abin da ke gusar da hankali, da kuma ƙaga wa rayuwa abin da ba saukakke daga Mahalicci ba, to ana iya cewa rayuwar Maguzawa abin sha’awa ne. Haƙiƙa wannan nazari ya ƙara bayar da hujjojin da za a iya dogaro da su na dalilan saurin karɓar Musulunci ga Hausawa. Babu shakka idan da za a ɗora falsafar da aka tatso a lamarin ɗaurin auren Maguzawa a mizanin awon kyawawan ɗabi’u da suka kamata al’uma ta samu, da an ba su lambar yabo.
[…] Falsafar ‘Daurin Auren Maguzawa […]
ReplyDelete[…] Falsafar ‘Daurin Auren Maguzawa […]
ReplyDelete