Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 037: Mataki Wane Iri?


    Ya ce "To ka taɓa jin na ce zan sake ta?" Yaron ya...


    Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 037: Mataki Wane Iri?

    Baban Manar Alƙasim
    Zauren Markazus Sunnah

    Kar ka taba cewa sai ka sami komai dari bisa dari ko ka dauki mataki, ka dubi kanka ka gani, ba komai kake yinsa yadda kake so ba, wani sa'in da kanka za ka gane ba daidai kake tafiya ba bayan ka gajiyar da kanka, akwai wanda ya fara sana'a ko shekara bai yi ba ya ce ya ga kamar ba zai kai labari ba sai ya canja, kafin shekaru biyar ya yi sana'o'i kusan takwas, cikinsu ba ko guda daya ƙwaƙƙwara, na ce ya yi gaggawa, ko kogi da kake ganinsa cike da ruwa da yayyafi ya taru.
    .
    Banda wannan ma mutum ya leƙa irin rijiyoyimmu na dauri waɗanda aka yi musu tsarin kwakware zai ga cewa igiyar da ake jan ruwan a hankali ta ci kututturen ta raba shi biyu, har ta kai ga ƙarfen, shi ma ta yi masa illa tana ƙoƙarin raba shi biyun, kai ma ka san ba aikin kwana daya ne ko biyu ba, yau da kullum kenan, mutum bai gaza ba idan ya zabi aikin da yake ganin zai iya yi a hankali, har ya kai ga inda yake so, in ma bai kammala ba ne ya yi ƙoƙari ya sami matsaya, duk lokacin da ya dawo dorawa kawai zai yi daga inda ya tsaya, ba komawa baya zai yi ba.
    .
    Muna maganar cin nasara ne a duk bangarori na rayuwa, wata rana wani bawan Allah ya sami matsala da matarsa a gidan haya, sai ya yi Æ™oÆ™arin sakin matar, har ya ce mata ta tafi gidansu zai zo ya same ta, to Allah ya sa maigidan bai riga ya fita ba, matarsa ta gaya masa cewa mai haya a gidansu fa yana Æ™oÆ™arin sakin matarsa a kan kaza da kaza, sai maigidan ya kira shi dakinsa ya tambaye shi ko ya san ranar da ya yi aure?  Yaron ya amsa cewa bai sani ba, sai ya ce masa "Shekara kaza kenan tun baka yi wayau ba, matarka ba ta wuce sa'ar diyata ta 3 ba, amma wallahi har Yanzu fama nake da ita".
    .
    Ya ce "To ka taɓa jin na ce zan sake ta?" Yaron ya girgiza kai wato a'a, ya ce "To haka kowa ka gani yana zaune lafiya da matarsa haƙuri ya fi ka, ba wai tsabar zaman lafiya ne ya kawo haka ba, in bai yi haƙuri ba a ƙarshe sakinta zai yi, ya koma ya sake auro wata macen, sai ka ji ana yi wa mutum lissafin yawan matan da ya saka, wani mai gidan hayan ko yaushe yana cikin korar mazauna gidansa ne, haka wasu masu wuraren sana'a, yau in ka ga wannan gobe ka ga wani daban, wai yaran ba su da kyawawan dabi'u, wani kuma mota ce a gabansa, da wahala ya shekara da mota guda, kar ka yi zaton duk in ya rabu da motar zai kawo wace ta fi ta baya ne, wani sa'in gwara jiya da yau.
    .
    Wanda ya fi ban takaici ma ƙananan yara 'yan makaranta, yau ka gansu a wannan makarantar gobe a wata, a kullum cikin kai kuka ne, yaran sun kasa samun makaranta daya da za su yi karatu, ba wai yara ba hatta manyan, zan ba ka misali: Wata rana ina zaune a aji sai ga wata mata ta zo koyon Larabci take ce min ta shiga makarantu da dama, wasu da ta lissafo sun fi ƙarfin makarantarmu, saboda sanin malaman da suke koyarwa a ciki, amma na karbe ta duk da haka, sai ya kasance ba kullum take zuwa ba, in ta zo wannan makon ƙarshe wani makon za ta gaya maka cewa tana da sha'ani a wani ƙauyen, wata ƙila ma ba za ka gan ta ba samsam sai bayan mako biyu, ta ya mutum zai iya harshen bayan bai mai da hankali ya koya ba?
    .
    Can sai na ji wata na ba da labari wai wannan matar na surutu a wani wuri tana cewa ba wani bambanci tsakanimmu da saura, ta ce ga shi ta hada shekara ko kyakkyawar jumula da Larabci ba ta iya hadawa ba, amma kuma ba ta sheda musu cewa matsalar daga wurinta take ba, galibin matsalolinmu da za mu yi haƙuri mu bi tsari da komai ya yi kyau, na ga yarinyar da aka maimaita mata aji, amma uwarta ta saba gyale ta zo wurin malamar ajin ta gaya mata cewa diyarta na da ƙoƙari ba wani dalilin da zai sa a koma da ita baya, duk bayanin da malamar ta so ta yi mata ta ƙi fahimta, haka dole aka kai yarinyar gaba kuma ba abinda take fahimta, uwarta ta ja mata.
    .
    Wani abokin karatuna da muke daki guda a wata ƙasa ya gano cewa yarinyar da aka damƙa masa a hannunsa amana ba ta kwana a gida, kullum tana wurin samari, karatun ma ta bari ko an kore ta, haka ya kira ubanta ya gaya masa gaskiyar abinda yake faruwa, lokacin da uban ya gaya wa mahaifiyar a nan cibi ya zama ƙari, ta kira abokin karatun nawa ta wanke shi tas wai ya yi wa diyarta sharri, a ƙarshe ma ta zo ƙasar ta ce ya cire hannunsa a kan diyarta kar ya ƙara sanya baki a kan abinda ba a saka shi ba, anan kam ba ta taimaki diyarya ba.
    .
    Duk irin wadannan abubuwa in za a duba su da idon basira sai ka ga an yi aiki da rashin lissafi wurin neman nasara, kamar maza ne tare da iyalinsu, ga su mazaje ne amma ba mazakuta, kamar dai yadda matan suke fadi, sai dai ka ji ana tambayarsu "Har ka zo ne" shi kuma ya bata rai, in ya ji abin ya yi yawa ya fara neman maganin mazakuta, a maimakon ya ga likita, da yawan maza ba su da ƙarfi a kan ƙaramar cutar da za a iya magance ta, wallahi wasu amosani ne ya riƙe mararsu, ko mabubbugar maniyyinsu, in an ba su shawarar su ga likita don ba sa jin zafi sai su ce maka su lafiyarsu lau, bayan ba lafiyar, shi ma wannan mummunan daukar mataki ne.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.