Ticker

6/recent/ticker-posts

Salon Kinaya a Cikin Kirarin ‘Yan Tauri


Haka nan kuma wasu ‘yan Taurin a yayin da suke kirarin, suna  siffanta kawunansu da Sa. Kamar  yadda  aka...


Salon Kinaya a Cikin Kirarin ‘Yan Tauri

ABUBAKAR SANI SAYAYA.
SASHEN WATSA LABARAI DA ƊAB’I
MAJALISAR DOKOKI TA JIHAR KATSINA.
08022671839

1.0 GABATARWA.
Tauri wata hanya ce da mutune ke amfani da wasu sunadarai da ake samu daga wasu itace, ko tsirrai ko sassan jikin wasu halittu misali ƙwari, ko dabbobi, ko kuma wasu ayoyi daga cikin Alƙur’ani mai tsarki, su sarrafa su ta hanyoyi daban daban domin kare jikinsu daga rauni, ko cutarwar da wani makami ka iya yi masu. Irin wannan kariya da jiki ke samu shi ne ake kira tauri. Duk  wanda ya ci maganin tauri ya kasance  ya buwaya to za a samu yana da wasu lafuzza da yake amfani da su a yayin da ya ke ƙoƙarin bayyana  irin  ƙarfin maganinsa, ko buwayar da yake da ita musamman yayin da makaɗansu ke  garza su. A ƙoƙarinsu na gina irin waɗannan lafuzza sukan yi la’akari da ɗabi’u ko halayen wasu abubuwa su siffanta kawunansu da su. Ire-iren waɗannan lafuzza ko maganganu su ne aka fi sani da kirari kamar yadda za mu gani. Irin wannan salo kuwa, shi ake kira salon kinaya.
1.1 MA’ANAR TAURI.
                Sayaya,(2009) ya bayyana ma‘anar Tauri da cewa “Kalma ce wadda ke nufin gagara’ ko ƙin sarrafuwar wani abu a sakamakon wasu dalilai na musamman da suke bambanta yanayin  abubuwa. Ire-iren waɗannan dalilai sun haɗa da sinadarai da mutum ke samu daga wasu itace, ko tsirrai, ko wasu abubuwa da ya yi amfani da su domin kare kansa daga rauni da wani makami ka iya yi masa. Wannan gagara ko ƙin sarrafuwa da jiki ke yi wa makami shi ake nufi da Tauri’.  Shi kuma wanda ya ci maganin ana kiransa da suna  Ɗan Tauri”. Shi kuwa Bunza,(1995) bayyana “Tauri” ya yi da cewa “Asalin kalmar Tauri daga “Tauri take mai nufin abu ya ƙi bari a sarrafa shi ta yadda ake so. Ko mutum ya faye ƙin karɓar shawara a kan ce wane taurin kai ke  gare shi. Mai irin wannan asiri na maganin ƙarfe ana kautata zaton wuƙa, da takobi, da mashi da duk wani makami na ƙarfe ba su fasa jikinsa. Haka kuma yana iya sarrafa ƙarfe yadda yake so, ba tare da wata wahala ba”.
1.2 MA’ANAR KIRARI.
Kalmar kirari kalma ce wadda ta samo asali daga kalmar ‘Kira’. Wato makaɗi ne zai sa ganga ya kira gwarzonsa ko kuma wani lokaci a busa masa ƙaho. Wato a busa ƙaho a kira shi. Bunza, (2009). Ya bayyana kirari da cewa “Asalin Kalmar daga KIRA take  a sa kalangu ko ganga ko murya a kira wani da ƙarfi dan ya fito a ɗebe tababan abin da ake faɗa a kansa”. Shi kuwa Danfawa,(2004) cewa ya yi “Kirari shi ne jera jimlolin adabi masu amfani da kalmomi waɗanda, ko dai su kasance masu kaifin  ma’ana  ko masu zurfin ma’ana. Kuma waɗanda aka tsara cikin salon siffantawa domin wasa, ko kumbura, ko ingiza mutum, ko wani abu”. Junaidu da Yar’aduwa, (2007). Sun bayyana kirari da cewa “wani rukuni ne na salon sarrafa harshe da Hausawa  kan yi anfani da shi wajen nuna gwaninta da kimar harshe ___________ , ta hanyar tsara kalmomi da suka dace da halayen abubuwa a cikin lugga mai ban sha’awa.
‘Yan Tauri sun kasance suna amfani da wasu zaɓaɓɓun kalmomi da suke gina irin Kirare-kiraren da su ke yi. Wato suna  siffanta  kawunansu da wasu abubuwa ta hanyar la’akari da yanayi, ko martaba, ko daraja, ko kuma halayen waɗannan abubuwa. Irin wannan zaɓi na abubuwa ne wannan takarda za ta mayar da hankali a kai, tare da kawo misalai da aka samo daga cikin waɗansu waƙoƙi da su makaɗan ‘yan Taurin ke yi ma mazajen nasu. Haka nan kuma waɗansu misalan an samo su ne kai tsaye daga bakunan su ‘yan Taurin.
A ƙoƙarin fito da irin wannan salo, za a gabatar da misalai na irin kalmomin da akan yi amfani da su a cikin ire-iren  kirare-kiraren da na ci karo da su a yayin da ni ke gudanar da bincikena. Kamar  yadda  za mu gani,  akwai  salon  Kinaya  inda  za  a  yi  la’akari da halaye, ko kwarjinin waɗansu dabbobi ko ababe  a kamanta su da wani ɗan Tauri.
2.0  MA’ANAR SALO.
Amfani da wasu zaɓaɓɓun kalmomi waɗanda za su yi ma Magana kwalliya domin jan hankalin mai saurare shi ake nufi da salo. Kuma shi salo yana iya kasancewa cikin waƙa ko kirari da makamantansu. Bayero,( 2001) ya bayyana salo da cewa “Yana nufin duk wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda ake bi domin isar da saƙo. Ita wannan dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya ta yadda saƙon waƙar zai isa ga mai saurare ko karatun waƙar”. Salo ba baƙon abu ba ne a cikin kirari kamar yadda zamu gani. Daga cikin ire-iren salo akwai salon siffantawa wanda ya ƙunshi nau’o’i da dama waɗanda daga cikinsu akwai kamance, da jinsarwa, da zayyana, da alamtarwa, da kuma na kinaya wanda akan shi ne wannan takarda zata yi bayani.
2.1 MA’ANAR  KINAYA.
“Kiran abu, musamman mutum, da sunan da ba shi ne nasa da aka san shi da shi ba, domin wannan suna ya bayar da ma’anarsa da kuma tunanin da ma’anar za ta kawo zuwa ga wanda aka kira da wannan suna; wannan shi ake kira salon kinaya. Salo ne wanda ake amfani da kalma ko kalmomi domin tunanin da suke sa mutum ya yi game da ma’anoninsu ya nashe ko ya lulluɓe wani abu ko mutumin da aka danganta kalmomin gare shi”.Bayero,(2001).
2.1.1 KINAYA  TA  HANYAR  LA’AKARI  DA HALAYEN  WAƊANSU  DABBOBI.
A cikin irin wannan salo, akan ɗauki hali, ko kwarjini, ko kamanni, ko ƙarfin wata dabba a ba wani domin a tsorata abokanen adawarsa. Misali inda Ibrahim Ɗantariya ya kamanta kansa da Gatan Biri. Yana cewa “Sai ni Gata dawa kora”. A nan yana nuna cewa shi fa tamkar namijin Biri ne, kuma wanda ya kasaita, ya zama jigo a cikin garken Birai. Duk Birin da ya riƙa har ya kai irin wannan munzali to da wuya a samu Karen farautar da zai iya korarsa. Ke nan Ɗantariya na gwada cewa shi fa ya giga a cikin harkar Tauri  inda har ya wuce gudu a daji, wato ba ya koruwa. Komi bajintar abokan gaba ba zai guje masu ba. Ire-iren waɗannan misalai su ne wannan takarda ta ƙunsa, kamar yadda za mu gani.
                Lawan S. Kila a cikin waƙar Bashiru Badagawa ya kamanta Audun Gayya da Birin, amma shi ga yadda yake cewa:
Allah Ka ji ƙan Audun Gayya
Samarin Biri mai gayyar tsiya
Uban ɗan ƙauye 1
A nan mamadin Lawal ya kira Audu gatan  Biri domin ya nuna irin ƙarfi da rashin tsoron gwarzon nasa, sai ya yi  la’akari da halin ban haushi da shi Audun yake da shi  ya kamanta shi da ɓarna da Biri ke yi ma mai gona. Wato duk irin Taurin ka, to Audun na iya ɓata  shi har shi yi abin da ba a so.
              Shi ma Ugu mai Kare, Lawan S-Kila ya siffanta shi da Tunkiya  wadda aka sani da sangarcewa da kiɗima da kuma hali na wauta. Ya yi irin wannan sifantawa ne domin ya gwada irin ɗanyen kai da mai Kare yake da shi. Ga yadda yake cewa:
                              Ugu mai Kare ɗan Tarko
                              Kazganyar Tunkiya uwar ɗanyen kai  2
Abdu Sarkin Taurin  Zakka a cikin kirarinsa sai ya siffanta kansa da Kura, wadda idan ta samu nama ba ta tsayawa wata-wata  sai ta kai bakinta kawai. A nan yana nuna cewa duk wanda ya tare shi to ba zai sha da daɗi ba. Yana cewa:
Dambu ni ke sai da gunari
Ƙodago sha murza
Kura ni ke mai  wawar rida 3


 Haka nan kuma wasu ‘yan Taurin a yayin da suke kirarin, suna  siffanta kawunansu da Sa. Kamar  yadda  aka  sani, ba ka raba  Sa da ɓarna, dole sai ana tare shi. Ga shi kuma da fushi, wanda a koda yaushe  kamar  cikin fushi yake, wato murtuk. Kuma ba ta sha wari  ba idan ya ci karo da mutum ya taka shi, ko ya sa ƙaho ya soke shi. Idan ma mutum ya faye fushi har ana kiransa “Mai fuskar mazan shanu”. Tur-ƙa-shi! Dubi yadda ake kiran  wani barden Tauri, wato Ɗan Iya na Bala. Ana ce da shi.
             
              Baƙin Sa mai taka mutane
              Mijin Yag Gambo 4
Wato shi idan dai batun  faɗa ne bai raga ma kowa ba,babu wanda zai haye masa bai takaita shi ba.
               Shi kuwa Garba na Zakka cewa ya yi:-
Kai Tunau! kai Tunau!Kai Tunau!      Babbaƙu  nike Iyalin Ahmed
              Shanun Nomau ni ke sai an tarbe
               In ba a tarbe ba, sai iyakar gona 5
A nan manufar Garba it ace, idan ya yo ɗauki zuwa ga abokanan gaba sai fa an tarbe shi. Muddin ba a tarbe shi ba, sai ya aikata abin da ba a so.
A cikin kirarinsa, Musa na Kirtawa ya siffanta kansa da baƙin Sa ne, inda ya ke cewa:
Baƙin sa nike mai rurin banza 6
Daga nan kuma ya ci gaba inda ya ke nuna irin haƙuri da juriya da ya ke da su, cewa babu batun gudu a gare shi duk irin gumurzun da za a yi da shi. Ko da kuwa wuta aka sa ma shi. Don haka ne ya kamanta kansa da Jaki. Yadda shi ne za a sa ƙarfe a cikin wuta sai ya yi ja, sannan a darza masa a jiki da sunan magani, amma bai damu ba. Yana cewa:
                        Kai Tunau! Kai Tunau!
                                      Manya gareni ba ni gasuwa,
                                     Jure kwaram sai Goga
                                     Haƙurin Wuta sai Jaki

Shi kuwa Alhaji Kassu Zurmi a cikin waƙar ɗan Jijji, domin ya nuna irin yadda ya gagari abokanen adawa har sun kai ga sun ƙare, amma shi bai kasa ba, sannan kuma shi bai damu da ya sare kan duk wani wanda ya far masa ba. Don haka ne shi Kassun ya siffanta shi da tsohon Doki da kuma baƙin Jaki, kamar haka:
                 
               Ka ji ɗan Bunu
Karen Magaji tsohon Doki 
Bai gaji da gudu ba karakara taƙ ƙare
                            Baƙin Jaki mai tuma da kayan Allah
Haka nan ma, Kassu ya sake siffanta  na Ali da Dokin inda ya ke cewa:-
Don na Ali babban baƙo
Mahaukacin  Doki 
                              Mai kiwo da lizzami nai

Lalle wannan ba ƙaramin hauka ba ne, a ce irin yadda Doki ke jin linzami, duk irin hauka da kuma ƙarfin da ya ke da shi, da an ja linzami dole ya ladafta, to amma sai ga shi an ce yana kiwo da linzamin da ke cikin bakinsa. Lalle hauka ya kai inda ya kai.
             Alhaji Goje Kofar Kaura a cikin irin kirarin da ya ke yi, ya siffanta kansa da Raƙumi. Kowa ya san halin raƙumi, wanda duk inda ya sa kai nai, sai an taro shi. Idan ba haka ba to mai shi kuwa ya sha biɗa. Shi dai ɗan Tauri abu biyu ne ya fi mayar da kai a gare su, wato shiga daji wurin farauta ko kuma neman magani. Bari mu ji yadda Gojen ke cewa:
Kai! Shuru dakanta! Mai hwara
Ka ga Raƙumi uban gararamba,
                Ai ka ga Raƙumi na Sarki Usumanu                Yanzu ko na Sarki Kabiru Magajin Usman7
Wannan ya tuno da wani zance da Bahaushe ke cewa  Raƙumi uban gararamba, Kowas sake ka sai ya nemo ka.”
               Kowa ya san basarake da son kyauta ta alfarma, kuma komai ƙanƙantar abu, in dai mai ban sha’awa ne to murna ya ke in an ba shi. Haka kuma duk wanda ya tashi yi ma sarki kyauta to ba shi ɗaukar abun banza ya kai fada. Don haka shi Duna uban Zayyana don ya nuna irin buwayarsa, sai ya ke gwada cewa shi fa ya fi ƙarfin duk wani raku-rakun ɗan Tauri. Sai dai sarakan Tauri. Don haka sai yake nuna cewa shi fa daidai yake da irin wanda ya dace a tura wurin sarakan Tauri. Amma ba ƙaramin ɗan Tauri ba. Don haka sai ya siffanta kansa da  jan Bunsuru tunda kowa ya san ba a tashi kai ma Sarki Bunsuru a kai masa baƙi dole sai ja, saboda akwai irin tasirin da kowanen su ya ke da shi ga al ‘adar malam Bahaushe. Yana cewa:
                             Sai ni jan Bunsuru abun ba Sarki
Kamar  yadda S-kila ya kira Audun gayya da “Samarin Biri” shi kuwa Ɗan kazagi Sanawa, sai ya siffanta Rabe a cikin waƙarsa da ɗan kuikuiyon kare. Yana cewa:-
                    Wake-waken malam
    Rabe, kara da kiyashi
                    Rabe ɗaukar maras sani
                 ‘Ya’yan karnuka maɗauka Magana
Amfani da irin wannan salon bai tsaya ga manyan dabbobi kaɗai ba, har ma da ƙanana da ma wasu tsuntsaye. Irin wannan ya fito a cikin kirarin Garba na Zakka inda ya siffanta kansa da wani nau’i na ƙadangare mai faɗa, ga cizo. Kuma idan ya ciji mutum yana sa masa dafi har ya kai ga kisa. Irin wannan ƙadangare shi ake kira Damatsiri. Garba yana kirari yana cewa”-
                           
                             Kai Tunau! Kai Tunau!                            
                              Tahe ni ke ban fasa ba
                            Damatsiri ni ke mai ganin maza kaikaice

Shi kuwa Garu-garu na Mande, Kassu zurmi siffanta shi ya yi da wani ƙaton tsuntsu da ake kira Burtu. Shi Burtun ya kasance ɗaya daga cikin ire-iren tsuntsayen da ‘yan Tauri ke farautarsu. Saboda yana da nama mai yawa ba kamar kananan tsuntsaye ba. Don haka ne Kassu ya siffanta girman Garu-garu a cikin  abokanensa domin ya nuna irin karfi da buwayarsa. Yan a cewa:
                           
                            Katakoro zakaran Burtu 
                            A bugeka ka maida faɗa sabo
                          Namijn jiya ba wani ba kai ba
Shi ma Barau na Umma mai Lahore an yi mashi irin wannan siffantarwar inda Lawal S. Kila ya kira shi kamar haka:-
                          
                           Zakaran gwajin dafin Ya-da-kwarawa
                           Dunya ba figar yaro ba
Dunya wata tsuntsuwa ce mai kama da agwagwa wanda ake samu a bakin ruwa. Girmanta ya ɗara na agwagwa. Sannan kuma gashinta tauri ke gare shi don haka fige shi ba ƙaramin aiki ba ne, bare kuma ga yaro. Shi ne Lawal S. Kila ya siffanta Mai Lahore da wannan tsuntsuwa da nufin cewa gwarzon nasa fa ya fi karfin duk wani raku-rakun ɗan Tauri.
A cikin waƙar Bakwai na Kande, Kassu ya siffanta shi da wani gawurtaccen Kare wanda ya kasance yana kashe Kura. Sannan kuma shi Bakwan ba raggo  ba ne domin ya siffanta shi da Doki kuma ƙarfafa. Ga yadda yake cewa:-
                          Na Katuka ƙarhwandamin Kare mai kashaKkura
                          Mahaukaci na Kufur hana noma na Kande
                          Doki ba sakarai ka ɗaukar Lihidi ba.
2.1.2 AMFANI DA HALAYE KO FASALIN WASU ABUBUWA DA BA DABBOBI BA.
A wnnan sashen kuwa an fito da wasu abubuwa ne waɗanda ya-Allah sun kasance masu rai ko ba masu rai ba. Amma su ire-iren waɗannan abubuwa ba dabbobi ba ne, ba kuma tsuntsaye ba ne ba. Wato wasu abubuwa ne da ka iya kasancewa sassan jikin dabba, ko  wani tsiro, ko dutsi ko wani abu makamancin hakan. Shi ma irin wannan salo, hanya ce da ‘yan tauri ke la’akari da halaye, ko ɗabi’u, ko kwarjini, ko martaba, ko isa, da makamantansu, su siffanta kawunansu da su. Su kan yi hakan ne domin su tsorata abokan gogayya, ko su kansu a tunzura su domin su kawar da tsoro, ko shakku, su kasance suna iya tunkarar duk  wata accakwama. Aiki sai mai shi. Bari mu garzaya fagegen nasu domin mu ga ko mu samu ɗan abin guzuri.
A cikin irn wannan  salo ne Alhaji Goje ya siffanta kansa da Gulbi wanda a bisa ga fasali ya fi duk wani matarin ruwa girma a ƙasar Hausa. Ya kuma ce shi fa Moɗa ne, Moɗa kuwa asali ludayi ne na duma da maɗaukinsa ya lanƙwasa, shi ne ake yanke saman ana ɗibar ruwa da shi ana sha. Kuma yadda ƙwarya ko gora suka kasance ba su da nauyi to haka ita ma Moɗa take. Duk wanda zai ɗebi ruwa da ita sai ya tausa saboda ba ta nutsa cikin ruwa da kan ta. Daga nan kuma ya ci gaba da cewa shi fa tamkar Gatari ya ke don haka in dai kana son ka ga wallen Alhaji Goje to dole fa sai ka tashi tsaye ka nemi tambaya, ka buwaya kafin ka faɗa masa. Ga yadda ya ke cewa:-
                                A gaishe ka, na gaishe ka
                                Ai gaya ma Arna Gulbi
                               Ai Gulbi nike babu jira sai ɗiba,
                               Ni am moɗa ko Kuwara sai an tausa
                               Gatari ni ke a sara ni tsaye
                               Arna kowas sara ni kwance shi ɗau ɓotar.
Shi ko Galadiman Tauri, abokin Alhaji Goje a cikin nasa kirarin sai ya siffanta kansa da tsakin Tama.‘Tsakin Tama gagara tauna’ A nan sai Galadima  ya na cewa shi gurorin Tama ne a yayin da Mai Hwara ke kaɗa takensa. Yana cewa:
                               
                              Kai mai Hwara!
                               Na ji ka kira gurori-gurorin Tama
                              Wallahi ni ag gurori-gurorin Tama
                               Na Alhaji Goje 8
Shi kuwa na Amadu sai yana siffanta kansa da wasu abubuwa da suka haɗa da Gangare  wanda idan mutum ya na bisa tudu zai sauko ƙasa to dole sai ya ƙara sauri, manufa sai ya yi gudu. Da Wahala wadda babu mai son ta. Haka nan kuma don ya nuna cewa shi fa iyakar Tauri ne, da an zo gare shi to ta ƙare. Don haka ne ya siffanta kansa da sallar Isha’i  wadda ita ce sallar farilla ta ƙarshe a kowace rana. Shi kuwa  Kisko wani tsiro ne mai tauri wanda kafin mai sara ya sare shi sai gatarinsa ya dakushe idan ma bai hankali ba sai ya kare. Wannan ya nuna cewa na Amadu ɗan Tauri ne wanda ƙarfe ba abin da zai yi masa, ko ka sare shi sai dai ƙarfen ya lalace. Ba ƙaramin aiki ba ne ga na Aamdu cewa duk wanda ya yi gigi ya far mai to yana iya rasa ransa a banza. Don haka sai ya gwada cewa, shi fa baƙin Ruwa ne wato mai guba duk wanda ya sha su to mutuwa zai yi. Duba ka ga yadda ya kawo su cikin kirari inda ya ke cewa:-
                            
                             Kowa ya san kowa ‘yan Tauri
                             Gangare ni ke mai sa mutum ya ruga da gudu
                             In kau ya tsaya a ɗauke mai rai
                             Wahala ni ke wadda da ba daɗi
                             Isha’I  ni ke sallar kwana
                             Dag gare ki sai rufe ɗaki
                             Kisko ni ke ɗata ƙaruffa
                             Dutsin ni am mugun abu
                             Babbaƙun  Ruwa mu ke, na Malkatu
                             Kowas sha mu ba ya kai labari 9
A cikin waƙar na Amadu shi kan sa Alhaji Kassu Zurmi yi ma na Amadun kirari inda ya ke siffanta shi da abubuwa da suka haɗa da Hayaƙi da Hurun-hurumi da Cira (Tsinkewa) da Ruwan dare da kuma Ruwan zafi. Kassu zurmi na cewa:-

                         
                                Hayaki tuƙaƙau
                               Tilas kun ka hid da na kogo
  Hurun-hurma maganin masu kara (karanbani)
                              Cira ɓata kayan Jaki
                              Ruwan dare ɓata kayan bako
                              Ya ɗora faɗin dan ba gari nai ne ba
                              Na Magaji Ruwazafi maganin mai zari
                              Ko dai an gumtse ku ba a haɗewa.
                            Ga hwaru can na Magaji ba ni hwaɗanku 10
Alhaji Kassu Zurmi ya kasance Bakandame a cikin mawaƙan da ke yi ma ‘yan Tauri waƙa. Don haka idan muka ci gaba da leƙe a cikin fagen nasa to ba za mu rasa ganin irin wannan salo ba. A cikin waƙar Mai dabo na gidan Duwa ya siffanta shi da Fatar Kura mai sa a razana, sannan kuma shi Mai dabo, buwayarsa a cikin ‘yan Tauri ba ƙarama  ba ce, don haka duk ɗan Taurin da ya kwan duniya a zamanin su to yana tunawa da shi. Saboda  buwayarsa sai Kassu ya ce ai Mai dabo shi sautun Doki ne. A nan ne ya ke cewa:-
                                
                                 Wo jikan Bawa Buzun Kura
                                 Gajere mazajen Duniya
                                 Sautin Doki ka hi mantuwa
                                 Yaro ƙarya ya kai 11
Shi kuwa Shehu Ɓuraguji a yayin da Kassu Zurmi ya fara kaɗa takensa, fitowa ya yi yana cewa:-
                                
                                  Kassu wallahi ta yi daren Taure
                                  Ka ga manya- manya sashen Gamji
                                 Yaro zaɓi a goge ma kaihi ko tsini13

Abin da ke sashe shi ne busasshen ganye wanda ake tanadar sa domin buƙatar gaba. Galibi an fi amfani da Kalmar sashe ga ganyen kwaɗo, misali ganyen Zogala, ko na Yaɗiya, da aka shanya shi ya bushe shi ake kira sashe. To amma domin Shehu ya gwada irin girmansa a cikin ‘yan Tauri, sai ya siffanta kansa da busasshen ganyen itacen Gamji. Shi ganyen Gamji babu wani ganye daga itacen ƙasar Hausa da ke yin girma kamar na Gamji.
A cikin waƙar Iro na Labbo kuwa sai Kassu Zurmi ya siffanta Iron da abubuwan da suka haɗa da Gobara da kuma Aradu wato (tsawa). Kassu ya na cewa;
                                  Iro uban na Kasake
                                 Baƙaw wuta ma ci littafi
                                 In an bari ga Malam tay yi
                                 Aradu ka horon Kurrma
                                 In ba ya ji ta tattartce shi14

Shi ma Jikan Bagwariya a cikin waƙoƙinsa ya kawo misalan irin wannan salo na kinaya. Misali a cikin waƙar ɗan Magaji inda ya siffanta shi da Cushe. Cushe wata hanya ce da ake ba da abinci inda za a riƙa cura abinci ana cusa ma yaro wanda ke kin cin abinci. Haka kuma akan yi ma dabbobi, musamman Doki domin ya yi ƙiba da ƙarfi. Ga yadda Jika ya yi amfani da Kalmar ya siffanta gwarzon nasa:
     
Wo ɗan Magaji cushen wake ɗan Mamman
                             Wo ɗan Magaji Dujal
                             Gagara dako goron Giwa 12

Shi kuwa ɗan Mamu sai aka siffanta shi da abubuwa guda uku a cikin waƙar da Jika ya yi masa. Abubuwan kuwa sun haɗa da Duka (bugu) da cinyar Sa, da kuma Sanho. Tir-ka-shi duba ka ga yadda batun ya kasance:
                                 
                                   Duka mai sa Ƙirgi laushi
                                   Gajere na Malam Audu
                                  Jakki mai shan bugu
                                  Cinyar Sa maganin mai haɗama
                                  Sanho mai wuyar kaya ɗan Dije
                                  Yaro ya cika ya kasa ɗauka
                                  In bai cika ba yai mai Malhwa15

A cikin waƙar ɗan Kazagi Sanawa kuwa siffantar da wani wanda ake kira Ali Buji mawaƙin ya yi da Saje ta hanyar la’akari da matsayin Sajen da darajarsa ga alumar Hausawa. Sannan kuma ya nuna cewa shi fa Ali yana maganin masu kuri, kuma shi dai Ali Bujin nan fa sandar Kanya ne, mai maganin mai gigi ko hauka, tab –ɗi, wurin da ba ƙasa nan ake gardamar kokawa duba ka gani.
                                
                                 Wai am mashi suna Ali mai Rake
                                 Ni na ce Ali Buji
                                 Saje  mai cika huska
                                 Sandar Kanya magani mu gamu
                                 Bugu da Ƙaya maganin Mahaukaci16

Ibrahim Ɗantanya kuwa a yayin da ɗan Kazagi ya fara zuga shi tasowa yayi yana cewa shi fa jar- ƙasa ne (Ƙabari) mai sa mutum ya razana dole da mutum ya ga Ƙabari sai ya tuna da Allah. A wani wurin kuma sai ya nuna cewa shi fa babban Yatsa ne, wato madugu uban tafiya dole a harkar Tauri sai da su ake yin ta ga yadda ya ke faɗa:
                                 Sai ni  mai  farin Kare uban ɗan Abu
                                 Sai ni Gata dawa kora
                                Jaƙ ƙasa ta bayan ɗaki
                                Kowag  gane ki ya tuna Allah
                                Babban ɗan yatsa
                               Abun kaɗi  abun yin ɗinki
                               in ba ka, ba kaɗi ba ɗinki17

Masu mura aka ce su ke da majina, domin shi kuwa Yusufu Kunu a cikin kirarinsa cewa ya yi:
                                
                                 Sai ni kunun Kuɗi kunun Kukkuki
                                 Kunu da ba a ba mai  jego
                                 Dakuskus- dakusari Gallar dutse
                                Yaro bai sha ba Gatarin uban shi ya ɓace
                                Sai ni Ttsinken tsikarin tsiya abokin ka Sule18

A cikin wannan karari Yusufu ya siffanta kansa da abubuwa guda uku. Da frarko dai shi kunun Kukkuki ne. Kukkuki wani icce ne da ake haɗa maganin jini da shi. Da zaran an dama shi an ba mai jego ta sha to tana iya cin karo da matsala inda ya ke nufin shi ya fi ƙarfi wani rubabin ɗan Tauri sai manya. Ya kuma siffanta kansa da Galla wanda wani ƙwaro ne wanda ke samar da wani ruwa mai zaƙi wanda ake sha. Shi ne sai  Yusufu kunu ya gwada cewa shi galla ne ga shi da zaƙi to amma cikin dutsi ya ke dole sai an fa sara dutsin kafin a kai gare shi. Wanda ko duk  ya sara dutse ya san gatarin nasa caɓewa za ya yi. Kai  daga ƙarshe sai ma ya ke cewa shi tsinke da ake  tsokano tsiya ne ɗungurumgum.
 A can cikin waƙar Ƙaura Galadi Ɗankanjiba, Lawan S- Kila ya kawo irin wannan salo inda ya siffanta shi da abubuwan da suka haɗa da Dafuwa da  Duka da kuma Barandami  ya na cewa:     
                       
                        Babbad dahuwa mai ƙare itacen yaro
                        Duka mai hana kai gayya
                       Barandami mugun makami
                      Yana wuya yana hannu
                      Ai saukarsa ce abun jin tsoro19

A cikin wakar Alu Mijin Husai sai mawaƙin nasa, wato Ummaru  Ɗan Umma ya siffanta barden nasa da wuya (wahala) wadda ake gudu tun da ba ta da daɗi. Ga yadda ya ke cewa.
                         
                       Wuya mai sa maza wuce mata20

A yayin da shi kuma Ummaru Hassan  Ɗan  Burunje  ya  siffanta nashi gwarzon do ‘Bori’. Wato ya nuna cewa Mainasara na sarkin Taurin Dange fa shi mugun Bori ne. Yana cewa:
                     
                       Ina mugun Bori, ka buwayi mai girkarka21


KAMMALAWA.
Wannan  bayani  da ya gabata ya ƙara jaddada ire-iren hikimomi da Hausawa suke da su waɗanda suke tabbatar da irin tanadin da harshen ya ke da shi na gamsar da kansa da wadatattun hikimomi da dabarun maganganu da suka kasance gajeru, amma  kuma suna ƙunshe da ma’anoni  masu yawa. Wannan ya tabbatar da cewa kirari daidai yake da Karin Magana, da Zambo da Habaici da  makamantansu  wurin  isar da saƙo daga mai magana zuwa ga mai sauraro. Al’adar  Bahaushe  ta Tauri  ba ta tsaya  ga  mawaƙa  da ‘ yan Taurin da na ambata a cikin  wannan  ɗan  bayani  da  aka  gabatar  ba. Saboda  haka  na  ke ganin  zai kyautu a samu wasu da za su ƙara yin tsokaci daga inda na tsaya.

Post a Comment

0 Comments