Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 35: Ƙananan Matsaloli


    A duk lokacin da matsala ta zo maka matuƙar ba ka son ta to kawar da ita. Kar ka yarda ta ƙara girma bare ta fasu zuwa gida biyu ko uku.


    Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 35: Ƙananan Matsaloli

    Baban Manar Alƙasim
    Zauren Markazus Sunnah

    Akwai ƙananan matsaloli da sukan faru nan da can, in mutum ya hadu da matsala a wurin aikinsa, kamar a kan kayan sana'ar, ko tsakaninsa da maigidansa, ko abokan aiki, lallai ya yi ƙoƙarin gyarawa kar ya bari lamarin ya yi girma yadda zai shiga cikin matsalar da a ƙarshe ya kasa fitar da kansa a ciki, misali daliba ce ta fadi mummunar magana game da malaminta, ba a gabansa ta fada ba, sai wasu ƙawayenta suka dauko suka gaya masa, wannan matsala ce mai sauƙi, duk da cewa ransa zai baci amma ya kamata ya mu'amalanci lamarin da hikima.
    .
    Ba a gabansa ta fada ba, ya bari sai ta fadi a gabansa din sai ya dauki matakin kaiwa gaba, wani da irin wannan ya faru sai ya sa aka yi masa kiran dalibar ya zazzage ta a ƙarshe ya mare ta yadda ta ji jiki, a gaban ƙawayenta, wannan ya sa ta ji zafi da ta bar wurin ta bankado wani sirrin da hakan ya gigita shi, mai makon ya dauki darasi a kan abinda ya faru a baya sai ya same ta ya yi mata dukan tsiya, duk jikinta ya kumbura, yarinya ta kai ƙara wurin uwayenta, su kuma suka bi kadin magana, a ƙarshe aka ƙare a kotu.
    .
    Ashe dai malam ya dan zazzagaya yarinya, shi ya sa ba ta ganin girmansa kokadan lokacin da ya yi mata ba daidai ba ta dan ladabta shi, wajen ƙoƙarin nuna mata cewa ba ta isa ba allura ta tono garma, makaranta ta kore shi, kotu ta daure shi, gashi kuma ya riga ya bata sana'arsa gaba daya, yanzu ko ya fito ba kowace makaranta za ta dauke shi ba, ba wai bai da abinda zai bayar ba ne, uwayen yaran ne za su ji wa 'ya'yansu tsoro, dole dai makaranta ta dakatar da shi, samun aiki kuma a wani wurin sai ya yi babbar sa'a, to ina nasarar da aka ci?
    .
    Akwai wata mata da take zaune a gidan aurenta, a kullum tunaninta daya wato abokiyar zamanta, ba za ka taba jin wata magana mai dadi a bakinta dangane da wancan ba, har dai dayar ta sami labari ta biyo ta jin ba'asin irin maganganun da take fadi game da ita, kamata ya yi ta yi amfani da ƙwaƙwalwa wurin warware matsalolinta, amma sai ta ƙi, a ƙarshe suka daga harshe har ta kai ga ta zargi kishiyar da karuwanci kafin maigidanta ya aure ta, ashe ita ma kishiyar tana da nata sirrin, nan fa ita ma ta ce "Na gode Allah tunda kafin aure ne na yi, kuma na tuba ina fatar Allah ya yafe min, ke ba wane yake dibarki har yanzu ba ko kina zaton ba mu sani ba ne?"
    .
    Magana kamar wasa ta nemi ta zama yaƙin badar, don an shigo da maƙwabci cikin rigima, masamman yadda danta ƙarami ya yi kama da shi sosai, kama kuwa ba 'yar ƙarama ba, a taƙaice dai tana gidansu auren zai baci, abin takaici ma makomar yaron da suke ƙoƙarin saka shi a halin ha'ula'i, kai da sauran yaran ma guda biyu, maganar gaskiya ba wata nasarar da ta ci ta zama a gidan aurenta, don an kada ta waje, 'ya'yan da ta haifa ma ana tababan na gida ne ko kawo su aka yi daga maƙwabta, asali wannan matsalar da ta bi ta a hankali da ta warware ta cikin sauƙi, yanzu ga ƙilu ta jawo balau.
    .
    A duk lokacin da matsala ta zo maka matuƙar ba ka son ta to kawar da ita. Kar ka yarda ta ƙara girma bare ta fasu zuwa gida biyu ko uku. Ko mutum guda kake da matsala da shi a wurin aiki yi ƙoƙari ku daidaita, kar ka yarda ya sami wanda zai goya masa baya su zama su biyu a kanka, yin hakan zai taimake ka wurin kaiwa ga nasara ba tare da ka ji jiki ba, ba yadda za a yi mutum ya rayu a wuri ba tare da matsaloli ba, sai dai wasu suna da dabarun taka wa matsalolinsu ne burki wasu kuma sukan bar su ne har su shanye su, a ƙarshe a koma gidan jiya.
    .
    Da farko in akwai matsaloli a gabanka kar ka yi musu kudin goro, bi kowanne ka warware shi cikin sauƙi, wani kudi yake buƙata, wani ban haƙuri, wani bai buƙatar ka je masa kai tsaye sai ka nemi taimakon mai shiga tsakani, zai yi kyau ka iyakance kowace iriyar matsala, maibuƙatar ban haƙuri ko kai ke da gaskiya same shi ka ba shi haƙuri a wuce wurin, ka dai rufe bakin tsanya, wanda yake binka bashi yi ƙoƙari ka biya shi, ko ka gamsar da shi, gobe in ka nema zai ba ka, in ka bata masa rai daga lokacin an gama kenan, zai ƙara ba ka.
    .
    Wanda ka ga zama da shi ba zai taba yuwuwa ba yi ƙoƙari ka guje masa gaba daya, in kuma dole sai an zauna a wurin to ka yi ƙoƙari wasu su san irin zaman doya da manjan da kuke yi, kuma ka nemi su yi muku sulhu, in ya ƙi to za su kasance tare da kai, ko ya so yi maka sharri za su taimake ka don sun san matsalar, in ka fahimci cewa mayar da bashi yana yi maka wahala to kar ka karba, in ma ya zama dole to ka san irin waɗanda za ka karba a wurinsu, da gwargwadon da za ka karba din, in ana zarginka da wani abu kar kullum ka tsaya kan cewa ba ka da shi, yi ƙoƙari ka yi maganinsa.
    .
    Sannan mai son cin nasara kar ya gina wa kansa kurkuku ya shiga ya kulle kansa, bare a kai ga sabawa mahallici, yadda mutum zai fara gaya wa kansa "To ni ya Allah ya halicce ni haka ne?" Ko "Ya saka ni a wannan matsayin" a kullum ka kalli matsalolinka ka yi ƙoƙarin warware su, in ana zarginka da yawan surutu kar ka ce ba ka da shi, amma ya za a yi ka kawar da abinda ake zarginka da shi? Shin maganar ce ratata, ko daukar maganar wannan da wancan ka fadi a wasu wuraren, ko ƙarairayi? Duk abubuwa ne masu alaƙa da juna, in ka fahimci kanka za ka iya gyarawa.

    ✍🏼Baban Manar Alƙasim
    [7:23 PM, 2/22/2020] SALIHI: HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA //
                               {036}
    .
                    IN KA CIZA KA HURA
    Duk wani mai bidar nasara a rayuwarsa ya san sai ya dage, amma wace iriyar dagewa? Hausawa kan fadi "Rai dangin goro, ban iska yake so" ba yadda mutun zai ce kullum aiki ba hutu, ka je wurin aikinka amma ka sami lokacin da za ka dan huta da iyali, gobe sai ka ji dadin fitowa da ƙarfi, idan kai dan kasuwa ne ka ga kiristoci ba sa fitowa sana'a ranar lahadi saboda addininsu, in ka fito sai ka fi samun ciniki don shagunansu a kukkulle, ƙila ma su kansu in suna buƙatar wasu abubuwan su zo wurinka su saya.
    .
    Nemi wata rana ka fito aiki amma ka tashi da wuri, saboda ka koma wurin iyali, kodai ku yi wasa a gida ko ku je ziyara wasu wuraren, za ka dan huta kuma yaranka za su gan ka, ko ba komai ranar za a sauya baki ta wurin cin wani abincin, bare kuma za ka rage mata yawan bari-bari da ƙiriniyar yara, ko dai su zo wurinka su yi wasa, ko in kananan su natsu, ƙila ma ka sayo musu wasu ƙananan abubuwa da suke buƙata, duk dai a dalilin kasancewarka a gida, ba yadda za ka hada farin cikin mace a lokacin da maigidanta yakenan da lokacin da bayanan.
    .
    Na dan fita wasu matattarar sai na ga wasu in suka so shan iska sukan dauki matansu ne su bar ƙasar da su, su je Dubai ko Saudia da sauran wurare, na ce masu kudi ne, wasu kuma sukan dibi iyalin ne su je bakin kogi suna kallon ruwa suna shan shayi, na san wannan ma ba za mu iya ba, wasu sukan debi iyalin ne su shiga kasuwa a sayi abinda rai ke so, shi ma yana da alaƙa da wadata, talaka ba zai iya ba, wasu sukan kwashi matansu ne da yara su leƙa gidanjen shan iska, shi ma din addini da ala'ada ba zai daga mana ƙafa ba, hatta fita unguwa da iyali gaskiya ba kowa zai iya ba, ƙila sai dai zama da iyalin a yi wasa da dariya, wannan kam sai dai mutum ya ƙi yi.
    .
    In ya zauna a cikinsu ana dan wasa da dariya koda sau daya kawai a mako abin zai yi kyau, yaranka za su sami cikakkiyar sakewa da tambayarka abinda suke so, ko su kawo maka kukan abinda yake damunsu, ko ka faranta musu rai kamar dai yadda suke buƙata, kai ma ka sami natsuwa ga lada tsagwagwa daga mahalicci, in ba ka yi hakan ba to zai kasance jikinka na son hutu, dole ya buƙaci waɗanda za su riƙa debe maka kewa koda ba iyalin naka ba, haka su ma iyalin in ta ƙure musu su buƙaci wanda zai debe musu kewa koda ba kai din ba, ka ga daukar mataki tun wuri ya zama dole kenan.
    .
    Kwanaki aka kawo hirar wata matar talaka, malama ce a makarantun boko, ta ga ƙoƙarin yaron ajinta kullum sai baya-baya yake yi, a ƙarshe ta daure ta sami mahaifiyarsa da take kawo shi kullum ta gaya mata abinda yake faruwa, sai uwar ta ce "Wallahi ko ni in zan gaya miki irin zaman ƙuncin da muke yi za ki san muna cikin damuwa, ba ma yaron ba" malamar ta so ji ko za ta iya taimakawa da shawarwari yadda dai za a ƙwato jin dadin rayuwar a dawo da shi, ta ce "To! Allah masani, amma ga ku bulbul, fesfes, kullum a manyan motoci cikin fara'a da walwala anya akwai damuwa anan?"
    .
    Matar ta ce "Wallahi in da ina tare da maigidana a gidan haya, kullum sai ya fita mu sami abinda za mu ci ya fi min wannan bala'in da muke ciki, mace da mijinta sai kwana biyu ko 3 za ta ganshi, in ya zo da ayyuka sai ta hada wata biyu ba ta gan shi ba, to in za ta ci abinci mai kyau bayan ta ƙoshi me kike tsammani?" Malama ta dan ba da shawarwari matar ta tabbatar mata da cewa wallahi za ta kashe auren kuma ba ta ma damu ko wa za ta aura ba matuƙar yana gida tana ganinsa a gabansu yana sauke hakkinsa na aure.
    .
    Koke-koken mata game da rashin zaman maza a gida ya yi yawa, ya kamata mazan su fara duba lamarin, mun sami wace uwayenta suka yi ta ba ta haƙuri har dai a ƙarshe ta gudu gidan 'yan uwanta, bai iya sauke haƙƙinsa, ta yi, ta yi ya nemi magani ya ce shi ya riga ya girma bai buƙatar komai, ta nemi ya sawaƙe mata shi kuma ya ce yana ƙaunarta ba zai iya ba, wata shekaranta 8 ta fita, ita ma duk dai matsala guda ce, maigidan bai da lokacin kula da iyalinsa, bai iya yin komai in ya dawo, wata 'ya'yanta 8 tana haƙuri kuma ba ta nuna damuwa, amma yanzu kafofin sadarwa na zamani sun fito ta gano akwai abinda take rasawa, a ƙarshe ta fita.
    .
    Akwai wace mako daya tal aka yi ta ƙara gaba, wata bazawara har an sa rana ta tsare angon ta yi masa tambayoyi game da mazantakarsa, ƙarshe auren da ba a yi ba kenan, don ya fito ƙarara ya nuna mata cewa zai iya yi mata komai na rayuwa in ba haƙƙoƙinta na shimfida ba, ta ce abinda ya raba ta tsohon mijinta kenan, shi ma an fasa, don samun nasara a gidajen aurenmu ya zama dole mu kula da iyalemmu kamar yadda muke kula da ayyukammu da sana'o'immu.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.