Haihuwa ko samar da ‘ya’ya shi ne babban manufar yin aure
ga al’ummar Hausawa, kamar yadda yake a mafi yawan al’ummun duniya. Shi kuwa
lamarin haihuwa yana samuwa ne ta hanyar yin aure, kuma ta hanyar haihuwa ne ake samun wanzuwar al’umma tun daga
farkon wannan duniyar har zuwa ƙarshenta.
Mai yiwuwa dangane da hakan ne al’ummar Hausawa ke faɗi-tashi
wajen yin aure domin neman haihuwa. Ba sai an faɗa ba, ana
iya ganin irin darajar da Bahaushe ya ba wa lamarin
haihuwa idan aka dubi irin damuwar da yake nunawa idan ya yi aure bai sami
haihuwa ba. Bisa ga wannan matsayi na haihuwa ne, a wannan maƙala
za a yi taƙaitaccen bayani a kan nason zamananci a cikin al’adun
haihuwar Bahaushe. Za a yi ƙoƙarin kawo yadda nason wasu baƙin al’adu
ya haifar da taɓarɓarewar waɗannan al’adu na haihuwa. Daga cikin abubuwan da muƙalar
za ta yi nazari a kansu sun haɗa da:
goyon ciki da kayan ƙauri da zanen suna da wankan jego da gara da reno.
Jiya Ba Yau Ba : Takaitaccen Nazari A Kan Bikin Haihuwa A Al’adarHausawa.
Rabiu Aliyu Rambo
Sashen Koyar Da Harsunan Najeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo; Sakkwato.
Email: rabiualiyurambo@yahoo.com
GSM:08125507991
1.0 Gabatarwa
Haihuwa na ɗaya daga cikin
manya-manyan ginshiƙan dalilan yin aure a cikin al’ummar Hausawa. Duk da yake
lamarin haihuwa lamari ne da ya bambanta daga wannan al’umma zuwa waccan. Domin
wasu al’ummu ba su buƙatar haihuwa kamar yadda wasu suke da. A ƙasar Hausa ɗa
(mace ko namiji) baiwa ce da kowa ke burin ya samu. A al’ada, yaro ko ba kai ka
haife shi ba muddin ka girme shi zai yi maka ladabi (C N H N . 1981 :16) Wannan
ya nuna ‘ya’ya suna da muhimmanci a cikin al’ummar Hausawa.
A al’adance, a duk lokacin da
aka sami ƙaruwa ta haihuwa a ƙasar Hausa, ana aiwatar da wasu al’adu waɗanda
ke nuna murna ko farin cikin ƙaruwar da aka samu. Don haka , wannan maƙala za
ta yi ƙoƙarin nazarin wasu daga cikin al’adun da ake aiwatarwa a lokacin
gudanar da bikin haihuwa a ƙasar Hausa. Daga cikin abubuwan da za a yi nazari
sun haɗa da al’adar goyon ciki da ta kayan ƙauri da ta zanen suna da ta wankan
jego da ta kayan gara da ta shayarwa.
Bisa haka ne a wannan maƙalar
za a yi ƙoƙarin kawo irin yadda zamananci ya yi tasiri a cikin al’adun haihuwar
bahaushe a yanzu . Ma’ana, za a dubi yadda nason baƙin al’adu ya taimaka
wajen taɓarɓarewar al’adun haihuwa na Bahaushe. A ƙarshe maƙalar ta
yi ƙoƙarin ba da shawarwari yadda za a tsare a kuma inganta waɗannan
al’adu musammam a cikin al’ummar Hausawa domin muhimmamcinsu.
2.0 Ma’anar Haihuwa
Dangane da abin ya shafi
ma’anar haihuwa kuwa, a nan ana iya cewa akwai ra’ayoyi daba-daban dangane da
ma’anar haihuwa . Domin wasu sun ɗauki ma’anar ne ta fuskar samun da wani
ya yi na wani abu. Misali a ce ‘yawan dariya barkatai na haifar da
hauka’ A nan haihuwa na matsayin musabbabi. Amma idan muka ce ‘Aisha ta haifi
Musa’ A nan wannan na nuna a sanadiyyar saduwa da Aisha ta yi da mijinta ta ɗauki
ciki har ta haifi Musa.
Ta wannan fuska, ana iya
cewa haihuwa tana nufin samuwar ɗa namiji ko mace da mutane kan yi ta hanyar
saduwa tsakanin namiji da mace musammam ta hanyar aure. Ga kaɗan daga cikin
abin da masana suka tofa dangane da ma’anar haihuwa. Abdullahi ya rawaito
Alhassan da wasu suna cewa ‘-----yayin da miji da mata suka ƙaru da samun ɗa
ko’ya ‘ (Abdullahi 2008:225)
A ma’anar ƙamussan Hausa na C N
H N an bayyana ma’anar haihuwa da cewa: ‘samun ɗa ko ‘ya bayan mace ta yi
ciki wata tara’ (kamussan Hausa C N H N .2006:189) Haka kuma a wani ra’ayin
cewa aka yi:
Ƙaruwa ce ta hanyar fitowar
wani abu mai rai daga jikin wata halitta jincin mace
wanda ya ɓoyu
a wani wuri na musammam na wani ƙayyadadden lokaci don samun kamanni ko
siffa kwatankwacin na zuriyarsu,wanda ke
aukuwa a sakamakon saduwa da jinsin namiji na wani
halittar.
(Abdullahi, 2008:228)
Bisa ga waɗannan ma’anoni, ana
iya fahintar haihuwa a wannan muhalli tana nufin irin ƙaruwar da matan Bahaushe
kan samu na ‘ya’ya musamman bayan sun yi aure. Domin a al’adar Bahaushe ana iya
samun ƙaruwa ta haihuwa amma maimakon a yi farin ciki sai ya zama na baƙin
ciki,wannan kuwa a fili yake idan aka dubi irin ƙyamar da ake nuna wa
matar da ta haihu ba tare da miji ba, ma’ana samun ɗan da aka Haifa ba tare da
aure ba.
3.0 Wasu Al’adun Haihuwa a Al’ummar
Hausawa
Idan ana maganar ƙasar
Hausa, ana nufin wata farfajiya wadda take shimfiɗe, tare da gulabe da duwatsu
da tsaunuka da suka ratsa ta jefi-jefi. Ƙasar Hausa tana da manyan birane da ƙananan
ƙauyuka da suka haɗa da Kano da Katsina da Daura da Gobir da Zazzau da Rano da
Garun gabas da Gaya da sauransu.
Ta fuskar harshe kuwa, Yahaya
da wasu (2001:95) sun ce:
Harshen Hausa shi ne wanda Hausawa suke amfani da shi,
kuma shi ne babban jigo wanda ya haɗa
dangantaka
da kasuwanci tsakanin waɗannan
garuruwa, sai kuma
harakokin kasuwanci da ciniki da saye da sayarwa
Don haka, mazauna ƙasar Hausa
kamar sauran ƙabilun duniya, suna da ɗabi’unsu da al’adunsu da suka keɓanta da
su, wasu daga cikin al’adun suna tattare ne da wasu bukukuwa da suke aiwatarwa
a tsakanin su. Waɗannan bukukuwa suna ƙara danƙon zumunci da kawo annashawa a
tsakanin su. Kuma waɗannan bukukuwan su ne ƙashin bayan jin daɗin zaman
al’ummar Hausawa. Waɗannan bukukuwa sun haɗa da; haihuwa da aure da
sallah da kalankuwa da shan kabewa da sauransu.
A wannan muƙalar za a yi
bayani ne a kan wasu al’adu da ake aiwatarwa lokacin bukin haihuwa a cikin
al’ummar Hausawa.
3.1 Al’adar Goyon Ciki
A ƙasar Hausa, ana da al’adar
mayar da yarinya haihuwa a gidansu idan cikin ya kai wata bakwai, kuma galibi
wannan na faruwa ne ga mace mai haihuwar fari. Wannan al’ada ana yin ta ne
domin mai ciki ta sami kulawa na musammam a gidansu .A wannan lokacin ana kula
da lafiyarta, kuma ana sanya mata wasu sharuɗa na hani ko horo ga aikata wasu
ayyuka ko cin wani abu musammam waɗanda za su taimaka mata sauka lafiya.
Haka za ta ci gaba da zama
gidansu har lokacin da naƙuda ta taso mata. Naƙuda ita ce wata alama da mai
haihuwa za ta fara ji ko gani kamar ciwon mara da baya da fitar ruwa fari
a gabanta . Lamarin naƙuda wani abu ne mai matuƙar wahala .Wannan ya sa har waƙa
aka yi mata kamar haka:
Wayyo naƙuda ta tashi
Ciwon naƙuda ya tashi
Kuma ciwon naƙuda ya motsa
Yau kam babu zama zaure
Wayyo Inna ki cece ni
Wayyo naƙuda ‘yar ziza
Ciwon naƙuda bori ne
Ko ko naƙuda hauka ce
Amshi ki ɗan kurɓa
Ba toka ce ba rubutu ne
Ko Allah nai maki sauƙin ta
(Yahaya da wasu 2001:99)
Ga al’ada, da zarar mace ta je
goyon ciki iyayenta za su rinƙa tanadin wasu kayan goyo. Haka kuma shi ma miji
zai tanadi nasa kayan ,wani lokaci ana kai mace ne gidansu, wani lokaci kuwa
iyayenta ne ke zuwa su ɗauke ta. (CNHN. 1981:17)
Kamar yadda aka ambata a baya,
idan naƙuda ta fara ana kiran wata tsohuwa a unguwa mai ɗaukar biƙi (ungozoma).
Ita ungozoma tana da masaniyar dabarun karɓar haihuwa. Bayan an sauka lafiya
ungozoma za ta yanke cibiyar abin da aka haifa, ta wanke jinjiri ta kuma
taimaka wurin gyaran ɗakin mai haihuwa. Tana kuma taimakawa da wasu ‘yan saƙe-saƙi
wadanda za a ba jariri da uwarsa domin gyaran jiki da kariya ga wasu
cututtuka. Kuma za ta ci gaba da yi wa jariri da uwar jaririn hidima har sai
bayan uwar ta gama wankan jego.
3.2 Kayan Ƙauri
A al’ada ana kai kayan ƙauri ne
bayan an yi kwana huɗu da haihuwa . Kuma mafi yawa ana amfani da ƙafafun sa ko
kai haɗe da kayan yaji kamar citta da kanunfuri da masoro da barkono da kanwa
da hatsi da sauransu. A kwana na biyar za a yi rabon ƙaurin bayan an cire wa
mai jego nata, inda za a ba maƙwabta da sauran dangi da abokan arziki. A
lokacin wannan rabon ƙaurin, ana haɗawa da kunun kanwa duk a raba wa maƙwabta.
Kuma a al’ada, duk namijin da matarsa ta haihu ba a yi bikin shan ƙauri ba, to
wannan ya yi abin kunya a cikin al’umma.
3.3 Bikin Suna
Kamar yadda sunan ya nuna ,
bikin suna wani yanayi ne da ake haɗa ’yan uwa da abokan arziki a ci a sha,
kuma a yi annashuwa da raha. Ana aiwatar da bikin suna ne idan ranar da aka
haifi jaririn ta zagayo; ma’ana bayan mako guda. Ranar suna, rana ce da za a raɗa
wa jaririn da aka haifa sunan da za a riƙa kiran sa da shi. Galibi a ƙasar
Hausa ana sanar da ‘yan ‘uwa da abokan arziki su haɗu musammmam da safe lokacin
kalaci domin gudanar da wannan al’ada.
A ranar suna, ana yanka rago a
raba goro, liman ya yi wa jariri huɗuba galibi bayan kwana bakwai da haihuwa,
duk da yake ana iya huɗuba tun ranar da aka haifi jinjiri a raɗa wa yaro suna
sai dai ba za a bayyana sunan ba sai ranar suna. Kuma galibi da yake Hausawa
mabiya addinin Musulunci ne, don haka, ana zaɓen sunan ne daga cikin sunayen
addinin Musulunci.
Ranar raɗin
suna ,za a taru tsakanin dangin mai
haihuwa da mijinta .Idan waɗanda
duk ake jira ya
taho, za a raba goro ga jama’a inda za a fara fitar da
na malamai da wanzamai da mata . Daga nan sai
liman ya yi wa abin haihuwar addu’a da ita kanta
mahaifiyar da uban da sauran
jama’a baki ɗaya
(Yahaya da wasu . 2001:99)
Shi kuwa (Gusau, 2012:42) Yana
da ra’ayin cewa:
Zanen suna ko raɗin
suna ana gudanar
da shi ga abin da aka haifa, bayan mako
ɗaya da haihuwa. Zanen suna
ko raɗin
suna ya kasu kashi biyu, akwai zanen
suna a gargajiyance, akwai kuma zanen
suna a addinance.
Ta kowace fuska dai za a
fahinci bikin zanen suna yana haddasa haɗuwar dangin mace da na namiji wuri ɗaya
domin taya juna murnar samun ƙaruwa ta haihuwar da aka samu.
3.4 Wankan Jego
Wankan jego wanka ne da mace
mai haihuwa kan yi da tafasassun ruwa har na tsawon a ƙalla kwana arba’in bayan
ta haihu safe da marece. Daga nan sai ta ci gaba da yi da safe ko da yamma
kawai zuwa kwana sittin ko ma fiye. A lokacin wannan wankan, ana yin amfani
ganyen sabara ko na doka ko na geza ko darbejiya ko sanga-sanga. Ana
amfani da waɗannan ganyayyaki ne saboda muhimmancinsu wajen samar da waraka
daga cututtuka daban-daban. A al’adance mace mai haihuwa tana fara wankan jego
ne tun daga ranar da ta haihu. Wannan wankan yana matsayin wata hanya ta jinyar
raunin da ta samu lokacin haihuwa. A wannan lokacin ne ake ba jinjiri dauri
domin kula da lafiyarsa.
A al’adance idan mai jego ta yi
aƙalla kwana arba’in tana yin wankan, har ɗan ƙwarya-ƙwary an biki
ake yi, inda za a toya waina a ci a yi sadaka. Bayan wannan lakacin ne
mace za ta fara kwalliya.
3.5 Kayan Gara
A ƙamussan Hausa, an bayyana
ma’anar gara da cewa:
Kaya, musamman na abinci da
iyayen
amarya kan kai wa ‘yarsu bayan an
gama bikin aure ko haihuwa.
(CNHN.2006;157.)
A zahiri ana iya fahintar ana
amfani da wannan kalmar ta gara a muhalli biyu ne lokacin bikin aure da
haihuwa. Ana kai garar haihuwa a ranar suna , wato kayan toye-toye wani
lokaci har da kuɗi . Sannan ana kai gara lokacin da mai haihuwa za ta koma ɗakinta
bayan ta ƙare wankan jego. A nan ana haɗa mata kayan abinci irin su shinkafa da
dawa da mai da daddawa da gishiri gwargwadon ƙarfin iyayenta. Wani lokaci
har makaɗi ake kira ya raka su, ana tafe ana waƙe-waƙe kamar sabuwar
amarya.
3.6 Renon Abin da aka
Haifa
Bayan an raɗa wa jinjiri suna
da sauran hidimomin al’ada kamar wankan jego da gara, al’ada ta gaba mai
muhimmanci ita ce renon shi abin da aka haifa. Reno shi ne ci gaba da
kulawa da shi, ta hanyar ba shi dauri da nono sau da yawa wannan yana faruwa
har tsawon wata shida . Daga nan ne za a fara ba shi kunun hatsi yana
sha, duk da yake ana yi mashi ɗure ne. A lokacin da jariri ya kai wata takwas
zuwa tara ne za a fara bashi abinci , sannu a hankali har ya fara ci da
kansa.
Haka a wannan lokacin ne ake
koya wa jinjiri zama daga nan sai rarraife da ta-ta-ta (koyon tashi tsaye) daga
nan ya fara koyon tafiya . Abin lura a nan shi ne, kusantar da jinjiri yake yi
da uwarsa a lokacin reno. Wannan kuwa yana taimakawa wajen samun shaƙuwa da
soyayya a tsakanin jinjiri da uwarsa. Duk da yake, a ƙasar Hausa akwai al’adar ɗan
reno, inda uwar jinjiri tare da amincewar mai gidanta za su samo wata ‘yar
yarinya domin ta taimaka wa uwar wajen renon jinjiri musamman lokacin da take
aiwatar da wasu ayyuka na gida. Bayan reno, abu na gaba ga abin da aka haifa
shi ne yaye. za a cire jinjiri ne daga shan nonon mahaifiyarsa. Galibi
ana kai yaron ne wajen kakanninsa zuwa wani lokacin da zai manta da nono. Daga
baya sai a dawo da shi wurin iyayensa.
4.0 Nason Baƙin al’adu a Cikin Al’adun
haihuwar Hausawa
Tarihi ya nuna cewa dukkan inda aka sami wata al’umma
ta shigar
wa wata al’umma, waɗanda
yake tilas ne ya zamana al’adunsu
sun sha bamban, to za ka taras al’adar al’ummar da ta fi ƙarfi
ta yi
tasiri a kan rarraunar. Im ma ba a mayar da hankali ba sai a
wayi gari a tarar ƙaƙƙarfar
ta mamaye rarraunar baki ɗaya.
(CNHN, 1981:32)
Kasancewar ƙasar Hausa ƙasa
ce mai daɗaɗɗen tarihi wadda ta sha faɗi-tashi da sauran al’ummu
daban-daban na kusa da na nesa wannan ya taimaka wajen kawo wasu sauye-sauye a
cikin al’adun haihuwar Bahaushe. Kasancewarya kullum duniya a cikin sauyi
take, wannan shi ya haifar da sauyi a cikin al’adun haihuwar
Bahaushe. Don haka, ci gaban zamani (wayewar kai) ya taimaka wajen sauya
tunanin Bahaushe shi kansa. Haka lalurar kwaikwayon baƙin al’adu shi ma sun
taimaka wajen taɓarɓarewar al’adun haihuwar Bahaushe. Don haka, akwai dalilai
da dama da suka taimaka wajen taɓarɓarewar al’adun haihuwa a yau, wanda inda an
tsaya tsayin daka aka riƙi waɗancan al’adu na gargajiya da sun
taimaka ainun wajen wanzar da rayuwa mai nagarta fiye da yadda ake a yau.
4.1 Taɓarɓarewar Al’adar Goyon
Ciki
Kamar yadda bayani ya gabata ,
goyon ciki shi ne zuwa gida da mai haihuwa kan yi gidan iyayenta,
musammam a lokacin haihuwar fari, yawanci tun cikin na wata bakwai. Idan
aka lura wannan al’adar an kusan mantawa da ita duk kuwa da irin muhimmancinta
ga al’ummar Hausawa. A yanzu za a taras zuwa goyon ciki ya yi ƙaranci
sosai a cikin al’ummar Hausawa. Masu ɓarɓashin wannan al’adar su ne waɗanda ke
bari sai matar ta haihu a mai da ita gida tare da jinjirinta. A nan za a ga
irin kulawar da za ta samu idan tana gidan iyayenta ba za ta same ta ba a gidan
mijinta musamman ga mazauna birane.
A nan, za a fahinci mai
haihuwar ta yi hasarar irin shawarwarin da iyayenta kan ba ta na hani ko horo
ga aikata wani abu, musammam wanda zai taimaka mata inganta lafiyarta da samun
sauƙin haihuwa. Don haka, al’adar komawa gida goyon ciki ta ci baya ainun a
cikin al’ummar Hausawa a yau. Hakan na faruwa ne saboda nason baƙin al’adu da
nuna wayewar kai na zamani.
Bugu da ƙari, idan aka dubi
irin hidimar da ungozoma ke aiwatarwa na kula da jinjiri ta hanyar yi masa
wanka safe da maraice na tsawon kwana arba’in da ba shi dauri wanda zai taimaka
wa lafiyarsa da kula da lafiyar uwarsa duk waɗannan an yi watsi da su. A yanzu
an mai da haihuwa asibiti, su kuwa asibiti babu rowan su da dauri.
4.2 Taɓarɓarewar
Al’adar Kayan ƙauri
Kayan ƙauri abu ne mai
muhummanci ga uwar jinjiri , domin suna taimaka mata wajen kulawa da lafiyarta
. A halin yanzu wannan al’adar ta yi rauni ainun a cikin al’ummar
Hausawa. Zai yiwu saboda matsalar tattalin arziki ko kuma wayewa ta
zamani, ta yadda a yanzu kowa yana zaune a gidansa ne babu wanda ya damu da
wani.
Baya ga ƙarin lafiya ga mai
haihuwa , rabon ƙaurin da akan yi yana ƙara danƙon zumunci a cikin al’ummar
Hausawa. Don haka, rashin aiwatar da wannan al’ada ya haifar da wani giɓi a
cikin lamarin zumuncin bahaushe. Haka ma, ana iya cewa a yanzu a
tsakanin al’umma babu jinkai da tausayin juna, uwa-uba sai tsabar rowa,
domin a yanzu maƙwabci na iya ci ya hana maƙwabcinsa ba tare da wata
damuwa ba.
4.3 Taɓarɓarewar Al’adar Bikin
Suna
Kamar yadda bayani ya gabata,
Hausawa sun ba bikin suna muhimmanci ƙwarai da gaske, musammam idan aka
dubi irin kai –komo da gidan uba da na uwar jinjirin kan yi na shirye –shiryen
suna. A al’adance za a ga ranar suna rana ce da ake tara dangin uwa da na uba
da ‘yan uwa da abokan arziki domin taya ɗan uwa murnar samun ƙaruwa. Wannan na
zaman wata kafa ta ƙara haɗa danƙon zumunci a tsakanin al’umma, inda za a haɗu
da wanda aka daɗe ba a haɗu ba . Wata fa’ida ta taron zanen suna ita ce wani
bagire ne da ake tattauna wasu matsaloli na al’umma.
Amma a yau, zai yiwu ko dai
saboda fahintar addini ya sauƙaƙa abubuwa. Wannan ya sa al’ummar Hausawa
sun yi saku-saku da wannan al’ada. Ta wata fuskar, ya yiwu matsatsin
tattalin arziki da al’umma ke fuskanta ya sa aka yi saku-saku da wannan
al’ada. Babu shakka, idan aka yi karatun-ta -natsu, za a ga wannan al’ada
ta taɓarɓare.
4.4 Taɓarɓarewar Al’adar Wankan
Jego
Hausawa na cewa, ‘Zamani riga
ce, tana daidai da wuyan kowa’. Duk da yake a al’adance an sani wankan
jego ko biƙi abu ne mai muhimmanci musamman ga mace mai haihuwa, a yanzu
al’ummar Hausawa na son ta yi watsi da shi. A zahiri a yanzu ta ci
baya ainun. Wannan kuwa ba zai rasa nasaba da wayewar kai ba, musamman ganin
yadda wasu matan Hausawa suke cewa wai amfani da ruwan zafi yana dafe masu
jiki. Wasu kuwa suna jin tsoron amfani da ruwan zafin ne saboda zafinsu. A
yanzu saboda yawaitar haihuwa da ake yi a asibiti ba a cika wankan jego ba.
Wannan kuwa yana faruwa ne saboda a yanzu akwai ƙwayoyin magunguna
da allurai da ake yi wa mai haihuwa a asibiti da zarar ta sauka maimakon
wankan jegon. Sai dai abin lura a nan shi ne, duk da waɗannan allurai bai
kamata a bar wankan jego ba saboda irin muhimmancinsa a al’ummar Hausawa.
4.5 Taɓarɓarewar Al’adar Kayan
Gara
Kayan gara kamar yadda bayani
ya gabata, ‘yan kayayyaki ne da ake kawo wa uban jinjiri a lokacin suna ko
lokacin da za a dawo da mai haihuwa daga gidansu zuwa ɗakinta. Wannan al’ada
ana yin ta ne domin a ɗan taimaka wa miji da wani abu, ganin ya yi ɗawainiyar
biki. Duk da irin wannan manufa ta kayan gara, a yanzu al’adar ta taɓarɓare
sosai a cikin al’ummar Hausawa. Wannan kuwa ba zai rasa nasaba da nason baƙin
al’adu ba. Domin a tsarin zamantakewar Bature kowa tashi ta fisshe shi ne, in
ba ka yi ba ni wuri. Zamantakewa irin wannan kuwa ba ta buƙatar taimakon juna,
sai dai kowa ya yi ta kansa. Zai yiwu kuma, saboda yanzu akwai matsin
tattalin arziki, musamman a Arewacin Najeriya wanda shi ya taimaka wajen
raguwar aiwatar da wannan al’ada.
4.6 Taɓarɓarewar Al’adar Reno A
Al’ummar Hausawa
A yanzu idan aka lura, za a ga
al’adar reno ta taɓarɓare ainun a cikin al’ummar Hausawa, musamman saboda nason
wasu baƙin al’adu a cikinta A zamanance ana ganin wannan a matsayin ci
gaba; Amma a zahiri ci baya ne . Misali idan aka dubi tsawon lokacin da
uwa kan samu tana goye da ɗanta ko rungume da shi, Wannan yana ƙara danƙon
zumunci da soyayya da jinƙai a tsakanin jinjirin da uwarsa. Haka kuma, nonon da
take ba shi yana matsayin kariya ga wasu cututtuka gare shi. Don haka, uwa kan ɗauki
ɗan reno domin ya rinƙa taimaka mata da renon.
A yanzu lalurar ɗan reno ya
kusa zama tarihi, domin yanzu zamani ya zo da cibiyoyin reno na musamman, inda
za a kai jinjiri reno, uwar kuwa ta wuce wurin aikinta. Bugu da ƙari , a
yanzu an samar da magunguna waɗanda suke ƙumshe da abinci. Wannan kuwa na
taimakawa sosai wurin rage shan nonon jinjiri. Wata matsala ta zamani da kawo
cikas ga harkar reno ita ce rashin gaskiya a cikin al’umma, inda sau da yawa za
a tarar an haɗa kai da ‘yar reno an cutar da jinjiri domin wasu buƙatu na
duniya.
5.0 Shawarwari
Domin tabbatar da wanzuwar
al’adun haihuwar Hausawa da aka ɗan yi bayanin su a wannan maƙalar, za a ga ta
la’akari da muhimmancinsu a cikin al’ummar Hausawa bai kamata a bari waɗannan
al’adu su salwanta ba wai don kawai nason baƙin al’adu da ya shige mu. Domin
duk al’ummar da take watsi da nata al’ada tana kwaikwayon na wasu, to
kul-a jima za ta manta da nata. Bisa ga wannan ne ake kira ga al’ummar Hausawa
da mu yi riƙo da kyawawan al’adunmu na haihuwa babu kama hannun yaro.
Ta fuskar amfani da kayan
zamani kuwa musamman kayan kallace-kallace, a yanzu sun maye gurbin hirar da
ake yi da dangi a lokacin bikin haihuwa. Domin a yanzu sai dai a shiga
kallace-kallacen fina-finan zamani. Don haka akwai buƙatar a yi watsi da wannan
al’adar ta kallace-kallace a yi amfani da dandalin suna wanda yakan zama
zauren tattauna matsalolin da suka shafi rayuwar al’umma.
Bayan haka, shigowar hukuma
cikin lamarin yana iya taimakawa wajen kauce wa taɓarɓarewar al’adun haihuwa a
al’ummar Hausawa. Domin wasu al’adun aiwatar da su na buƙatar kuɗi. A yanzu
saboda matsin tattalin arziki mafi yawan Hausawa suna fama da wannan
matsala ta kuɗi. Don haka, hukuma na iya taimaka wa al’umma da bashi ba tare
ruwa ba . Hukuma na iya ƙirƙiro wasu dokoki waɗanda za su taimaka wajen
wanzar da al’adun haihuwa. Yin haka, zai taimaka wajen maganin taɓarɓarewar waɗannan
al’adu.
Bugu da ƙari, wannan maƙalar na
ganin ya kamata a sami wasu ƙungiyoyi na maza da mata da za su taimaka wajen
wayar ma jama’a da kai dangane da muhimmancin waɗannan al’adu. Al’adun kuwa sun
haɗa da na goyon ciki, da na bikin suna, da na reno, da sauransu. Kuma su waɗannan
ƙungiyoyi su zama a ƙarƙashin kulawar shugabannin kowace al’umma waɗanda suka
san darajar al’adun.
Shawara ta gaba ita ce,
matsawar ana son kauce wa taɓarɓarewar waɗannan al’adun haihuwa, to akwai buƙatar
a ɗan yi ma wasu gyaran fuska ta yadda za su dace da zamani . Misali al’adar
yankan rago . Tun da an fahinci ba dole ba ne, to ya kamata jama’a su fahinci
rashin rago ba ya hana suna. Domin a yanzu, sau da yawa za a tarar saboda
rashin rago an daɗe ba a yi suna ba. Haka idan aka dubi al’adar shan-ƙauri
da gara, sun so su ɗan yi tsauri musamman ga marasa abin hannun su, domin wani
ba ya da ƙarfin aiwatar da wannan al’ada. Amma kuma sai al’umma ta zarge shi a
kan ya kasa. Maimakon haka, kamata ya yi a ba mai gida shawara ya riƙa
yin haƙuri da duk abin da Allah ya ba shi.
A ƙarshe, bisa ga shawarwarin
da aka bayar a sama , za a ga al’adun haihuwa sun taimaka musamman wajen
adana da kuma haɓaka zumunci a tsakanin al’ummar Hausawa duk kuwa da irin
barazanar da nason baƙin al’adu yake yi a kansu.
6.0 Kammalawa
Al’amarin haihuwa, al’amari ne
mai matuƙar muhimmanci a wurin al’ummar Hausawa. Hasali ma, haihuwa ita ce ƙashin
bayan yawaitar kowace al’umma a duniya. Shi kuwa lamarin haihuwa yana samuwa ne
sanadiyyar yin aure a tsakanin namiji da mace. Buƙatar wannan haihuwa ya sa
al’ummar Hausawa ta ba wa aure muhimmanci domin samun haihuwa.
A wannan maƙala an yi ƙoƙarin
nazarin wasu al’adu ne da suka keɓanta ga al’adun haihuwa a al’ummar Hausawa.
Daga cikin su akwai al’adar goyon ciki da ta naƙuda da ta kayan ƙauri da ta
bikin suna da ta gara da ta reno da sauransu. A nan maƙalar ta yi ƙ
oƙarin bayanin yadda suke a da, da kuma yadda suke a yanzu bayan an sami nason
baƙin al’adu a cikin su. Haka kuma, bisa ga binciken da aka gudanar an fahinci
a yanzu waɗannan al’adu sun taɓarɓare a cikin al’ummar Hausawa. Don haka,
an kawo shawarwari yadda ake ganin za a iya kare al’adun daga ƙara taɓarɓarewa.
Ko shakka babu, waɗannan al’adun haihuwa sun taimaka wa al’ummar Hausawa wajen
wanzar da zamantakewa mai nagarta a tsakanin al’ummar Hausawa tare da inganta
kiwon lafiya.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.