Ticker

6/recent/ticker-posts

Gwagwarmayar Kamancen Neman Auren Hausawa Da Na Dakarkari


Aure al’ada ce wadda ta daɗe a duniya baki ɗaya. Hasali ma tushen aure ya samo asali ne tun lokacin da Allah (S W A) cikin ikonsa ya halacci mutum na farko a doron ƙasa, watau Annabi Adamu (A S). Sannan cikin ƙaddarawarsa ya halicci Hauwa’u domin ta zama matarsa. A wannan maƙala za a yi ƙoƙarin nazarin kwatance ne na wasu daga cikin al’adun neman auren Hausawa da na Dakarkari. Don haka, maƙalar ta yi tsokaci ne a kan tsarin neman auren Hausawa da na Dakarkari  musamman abin da ya shafi wasu keɓaɓtattun al’adu kamar: soyayya a tsakanin saurayi da budurwa da zance ko taɗi da matsayin ɗanrakiya da matsayin iyaye da al’adar na-gani-ina-so da dai sauransu. Da yake muƙalar ta shafi al’adun al’umma biyu ne, don haka, an yi ƙoƙarin kawo bambanci da kamancin tsarin yadda ake aiwatar da waɗannan al’adu. A ƙarshe maƙalar ta yi ƙoƙarin bayanin wasu hikimomi ko falsafar da ke tattare a cikin wannan rumbu na al’adun neman auren Hausawa da na Dakarkari.


Gwagwarmayar Kamancen Neman Auren Hausawa Da Na Dakarkari

Rabiu Aliyu Rambo
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto.
Email: Rabiualiyurambo@yahoo.com
GSM:08125507991

1.0 GABATARWA


Neman aure  a al’adar  al’umar Hausawa da na Dakarkari abu ne da ke tattare da kai-komo na iyaye da saurayi da budurwa . Wannan kila shi ya sa Hausawa ke masa kirari da cewa: Aure marmari daga nesa, ko Aure wane yaro, ko Ba neman aure ke da wuya ba shiga da fita. Wannan ya nuna muna cewa akwai gwagwarmayar da mai neman aure zai yi ta cin karo da su a lokacin neman aurensa. Don haka, mallakar mace ga al’umar Hausawa da na Dakarkari ba ƙaramin aiki ba ne, sai namijin gaske . Duk da yake, kafin zuwan addini, Hausawa na da wasu hanyoyi na mallakar mace kamar : Neman aure da yaƙi da samame da hari da cire da tsituwa da bashi da saye da kyauta da kwartanci.

Al’umar Hausawa da na Dakarkari al’uma ce da ke da daɗaɗɗiyar dangantaka da cuɗanya a tsakaninsu mai daɗaɗɗen tarihi. Don haka, wannan maƙala za ta yi ƙoƙarin nazarin wasu daga cikin al’adun neman auren Hausawa ne da na Dakarkari . Da yake al’adun aure yawa ne da su, don haka, wannan maƙalar ta taƙaita ne ga irin gwagwarmayar da ake yi a wurin aiwatar da wasu daga cikin al’adun neman auren waɗannan al’umma guda biyu (Hausawa da Dakarkari).

A ƙoƙarin nazarin waɗannan al’adu ,wannan maƙalar ta yi nazarin yadda ake aiwatar da kowace al’ada daga al’ummomin Hausawa da na Dakarkari. Bayan wannan, maƙalar za ta yi ƙoƙarin kawo irin kamance-kamance da kuma bambance-bambancen da ake samu a lokacin aiwatar da waɗannan al’adu a tsakanin waɗannan ƙabilu biyu. Haka kuma , yana daga cikin manufar wannan maƙala ita ce, zaƙulo wasu hikimomi ko falsafofin da ke tattare da aiwatar da waɗannan al’adu a tsakanin ƙabilun Hausawa da na Dakarkari

Daga cikin al’adun neman auren da za a yi nazari a wannan maƙala sun haɗa da: soyayya da zance ko taɗi da matsayin iyaye da isa gida da gaisuwar abokai da al’adar na-gani-ina-so da sauransu.

2.0 Ma’anar Aure:



A gaskiya zai yi wuya kai tsaye a ce ga ma’anar aure guda ɗaya karɓaɓɓe kuma gamsasshe ga al.uma baki ɗaya.Wannan kuwa ba zai rasa nasaba da ganin cewa kowace al’umma tana da yadda ta ɗauki aure ba .Bisa ga wannan ne masana ilimin zamantakewa da ɗaliban al’adun al’umma musammam na Hausawa da na Dakarkari suka kawo ra’ayoyinsu dangane da ma’anar aure .Misali Habibu Alhassan da wasu (1980) sun haɗa hannu suka bada ma’anar aure kamar haka:

Aure alaƙa ce ta halaccin zaman tare

tsaƙanin namiji da mace. Ana yin sa ne saboda

abin da aka haifa ya sami asali da mutunci da

kiwon iyaye. Kuma shi ne maganin zina da ‘ya’ya

marasa iyaye.

Wannan ma’anar ta nuna aure zamantakewa ce a tsakanin namiji da mace tare da amincewar juna .Amma ita kuwa Fatihiya Migdad Sa’ad (1998:196) tana da ra’ayin aure a musulunci kamar haka:

Aure shi ne halaccin zaman namiji da mace

tare da cika wasu dokoki , tare da  ba kowa nasa

hakkin zamantakewa a tsakaninsu. Wannan

yarjejeniyar ta zama tare kuma za a yi ta bisa

koyarwar addinin musulunci wanda ake samu

a cikin al’kur’ani da hadisan manzon Allah(SAW)



Haka ma M A Rauf (1970:78) ya bayyana cewa; bisa ga shari’ar musulunci aure shi ne :

Ƙulla wata yarjejeniya da za ta haifar da

halalcin saduwa da mace dasamun zuri’a.

Kuma wani bangare ne na mu’amula da ibada.


Harwayau, wasu masana zamantakewar al’umma (sociologist) sun kalli aure ta wannan fuska. Misali: Burgess da Locke (1953) sun bayyana aure da cewa:

 “  Zamantakewa ce ta amincewar mutum ɗaya ko fiye da ɗaya ko mace ɗaya ko fiye da ɗaya mai dangantakar mata da miji”.

Anan muna ganin cewa,  ga tasu fahinta ba dole bane aure ya kasance a tsakanin mace da namiji. Domin ana iya samun inda mace zata auri mace, namiji kuma ya auri namiji domin wasu al’adu ba su hana haka ba . Amma a ra’ayin wani masanin Dr Wester Mark (1984) yana cewa: “Akwai muhimmam abubuwa uku ga kowane aure, sune biyan buƙata na kwanan aure da dangantaka a tsakanin namiji da mace da kuma domin samun zuri’a (haihuwa)”                              Bisa ga waɗannan ra’ayoyi da ke sama dangane da ma’anar aure  , anan muna iya cewa aure alaƙa ce ta zamantakewa tsakanin mace da namiji bisa ga amincewar juna tare da bin wasu ƙa’idoji da addini ko al’ada ta aminta da su.

Don haka, aure a al’adar Hausawa da na Dakarkari al’ada ce mai muhimmanci tattare da wasu hikimomi na musamman a cikin al’umma. Daga cikin falsafar yin aure ga al’umar Hausawa da na Dakarkari sun haɗa da : Bunƙasar arziki da samun ‘ya’ya(ɗiya) da tushen zuri’a da nuna kamala da zumunci da biyan buƙatun aure da sauransu.

3.0 TSARIN NEMAN AUREN HAUSAWA DA NA DAKARKARI


3.1 Soyayya Tsakanin Saurayi Da Budurwa

Soyayya ita ce  ƙauna  ta wani mutum ko wani abu daban. A zahiri an fi amfani da wannan  tsakanin namiji da mace musammam saurayi da budurwa. Soyayya  a harkar aure wata aba ce mai nuhimmancin gaske ga auren Hausawa da Dakarkari. Idan babu soyaya da wuya a iya zaman aure , don haka soyayya ita ce ƙashin bayan zaman auren Hausawa da na Dakarkari. Duk da yake ana iya samun zaman aure ba tare wata soyayya ba.

3.1.1 Tsarin soyayya a al’adar Hausawa:

A al’umar Hausawa, tsarin soyayya ta taka muhimmiyar rawa a tsakanin saurayi da budurwa. Galibi wannan soyayyar ita ke ƙara danƙon zama tare wanda zai haifar da aure. Bincike ya gano cewa, al’umar Hausawa suna da soyayya iri biyu ne zuwa uku .Ga su kamar haka:
  • Soyayyar da ke haddasuwa saboda haɗuwar jinni tsakanin saurayi da budurwa. Wannan yana iya shafuwar ƙirar jikin saurayi ko budurwa.
  • Soyayya saboda hali, ma’ana ɗabi’ar mutum
  • Soyayya saboda hali (arziki) watau ana samun ginuwar soyayyar Bahaushe saboda irin arzikin gidan saurayi ko budurwa.

Duk waɗannan soyayya suna ginuwa ne yayin da saurayi zai rinƙa ganin budurwa yana yi mata wata ‘yar ƙyauta. Bincike ya gano cewa amfi samun soyayya ta zahiri a tsakanin saurayi da budurwa kafin zuwan addini. Don haka, muna iya cewa soyayya  a wannan zamani ta yi ƙaranci, don an maye ta da sha’awa . Za ta yi yu saboda rashin wannan soyayya ake samun yawaitar mutuwar aure a cikin al’umar Hausawa a yau. Domin ita sha’awa gushewa ta ke, amma soyaayya ba ta gushewa. Hasali ma soyayyya ga Bahaushe a wancan lokacin ta dogara ne a kan irin bajinta da kirkin saurayi, domin ba a duban arzikinsa balle a dubi abin da za a samu daga cikin arzikin .

Wani abin kulawa anan shi ne , ga al’adar Bahaushe saurayi ke ganin budurwa ya ce yana so,; duk da yake a al’adance Bahaushe bai yarda saurayi ya rinƙa cuɗanya da ‘yanmata a tsakaninsu ba .Don haka lamarin soyayya abu ne mai muhimmamci ga zamantakewar neman auren Hausawa.

3.1.2 Tsarin Soyayya a al’adar Dakarkari:

Kamar Hausawa , su ma Dakarkari suna da tsarin soyayya wadda ke wanzuwa a tsakanin saurayi da budurwa musamman a lokacin da samarin Dakarkari ke aiwatar da wata al’ada ta “Golmo” . Duk da yake wani lokaci ana samun auren da iyaye kan tilasta ‘ya’yansu ba tare da soyayya ba, amma galibi Dakarkari suna aurensu ne don soyayya. Duk da yake a yanzu ana samun masu auren sha’awa.

Ga al’adar Dakarkari, budurwa ce ake neman soyayyarta .A ƙoƙarin samun soyayyar yarinya saurayi kan shiga aikin “golmo” tun yana da shekaru goma sha biyar (15) zuwa sama. Yin wannan aiki na golmo yana ƙara danƙon soyayyar. Wannan kuma na faruwa saboda irin bajinta da dauriya da hanƙurin da saurayi kan nuna wajen ayyukansu na yau da kullum. Haka a soyayyar Dakarkari tana da walwala domin ba su kange cuɗanya tsakanin saurayi da budurwa ba.

3.1.3 Bambanci Da Kamancin Tsarin Soyayyar Hausawa Da Na Dakarkari:

Kamar yadda bayani ya gabata a baya , al’umar Hausawa da na Dakarkari duk suna aiwatar da wannan al’ada ta soyayya. Amma ba a rasa wasu ‘yan bambance-bambance ba, haka kuma ta wata fuska sun yi kama da juna.

Da farko dai abin da ya bambanta tsarin soyayyar Dakarkari da Hausawa ita ce walwalar soyayya. Domin a al’adar Hausawa ta hana cuɗanya tsakanin saurayi da budurwa, amma su Dakarkari ba su hana wannan ba.

Ta fuskar kamanci kuwa , Dakarkari suna gina soyayyarsu ne ta hanyar golmo inda ake gane bajinta da dauriya da hanƙurin saurayi .Ga al’ada duk saurayin  badakkaren da ya kasa yin golmo, to ya yi abin kunya ko zagi a cikin al’umma . Kuma da wuya a samu budurwar da za ta so shi . Wannan kuwa muna iya ganinsa idan muka dubi wasu al’adu na Hausawa kamar ɗauko maiki na maguzawan kwatarkwashi. Haka kuma, kamar Hausawa su ma Dakarkari ana samun sha’awa a tsakanin saurayi da budurwa,  amma wannan bai zama hujjar cewa ba su auren soyayya ba .

3.1.4 Falsafa ko Hikimar Da Ke Cikin Al’adar Soyayya

Bisa ga bayanan da aka yi na tsakuren al’adar soyayya, muna iya fahintar cewa, akwai wasu falsafa ko hikima na aiwatar da wannan al’ada ga Hausawa da Dakarkari. Za ta yiyu saboda wannan ne ya sa al’umar ba su cika yin aure ba sai an tabbatar da akwai soyayya a tsakanin saurayi da budurwa .

Da farko dai za mu  ga cewa, tana kawo sanin halin juna . Idan kuwa aka samu matsalar soyayya ,to tun a wannan lokacin ne ake rabuwa . Haka kuma cikin wannan lokacin ne ake samun gyaran halayen juna . Bayan wannan , ta wannan zaman soyayya  ne ake auna irin hanƙurin juna da dauriya da sauransu a tsakanin masoya.

3.2 Zance ko Taɗi

Wannan shi ne zuwa hira da saurayi kan yi a gidan budurwa ko wani muhalli na daban da suke haɗuwa a wani lokaci na musamman . Galibi a irin wannan hirar(zance) ana tattauna lamurran yau da kullum ne.

3.2.1 Tsarin Zance A Al’adar Hausawa

Hausawa sun ba wannan al’ada muhimmanci sosai . Don haka, sun tanadi wani tsari na musammam domin aiwatar da ita. Kuma ganin cewa, Hausawa sun fahinci irin hatsarin da ke tattare da wannan al’ada ,sai suka tanadi lokaci da wuri na aiwatar da wannan al’ada. Domin ba su yarda su bar ‘ya’yansu ba tare da sa ido da jagoranci ba. Da farko za mu ga cewa wannan al’adar sai da dare ko yamma  ake yin ta, kuma galibi gidan budurwa ake zancen, inda ake samun gidin bishiya ko zauren gida.

Haka kuma, Bahaushe na da tsarin zuwa da ‘yar rakiya, kuma al’ada ba ta yarda saurayi ya rinƙa zuwa zance kullum ba , don haka galibi an fi zuwa zance ranar kasuwar garin . Kuma Hausawa na da al’adar bada kuɗin jin-kira . Amma duk da wannan, Bahaushe na da wata al’ada ta tsarance inda saurayi zai rinƙa zance da budurwa har ta kai su kwana ɗaki ɗaya ,amma saboda gaskiya da aminci ba za su san juna ba .

3.2.2 Tsarin C’mene (Zance) A Al’adar Dakarkari

A al’adance Dakarkari ba su hana cuɗanya a tsakanin saurayi da budurwa ba ,don haka ba su keɓe wani lokaci ko wuri na musammam da za su haɗu ba . Dakarkari a wancan lokacin kafin zuwan addini suna haɗuwaa duk lokacin da suka ga dama amma wani abin kunya baya faruwa a tsakaninsu. Saboda irin wannan aminci ne ya sa Dakarkari suna wata al’ada wurin neman aure wadda ake kira “c’mene”(tsarance).A wannan lokacin zancen, saurayi da abokansa suna ƙoƙari ne su ƙara danƙon soyayya a tsakaninsu. Don haka, a al’adar Dakarkari ba su amfani da kuɗin kira; duk da yake a yanzu ana samun wannan jefi-jefi.Kuma galibi raha ne da barkwacci ake yi ma juna. Amma duk da rashin ƙangin  da ba  a yi wa saurayi ba na ganin budurwarsa duk lokacin da ya ga dama, bai hana sa ido ga iyayensu ba .

3.2.3 Bambanci Da Kamancin Tsarin Zance A Al’adar Hausawa Da Na Dakarkari

Abin da ya bambanta su ta fuskar tsari shi ne, su Dakarkari ba su kange saurayi daga zuwa wurin budurwa ba a kowani lokaci ko wuri na musammam ba. Haka kuma Dakarkari ba su kange cuɗanyar saurayi da budurwa ba a kowani lokaci.

Ta fuskar kamanci kuwa, anan za mu ga tsarin zuwan saurayi gidan budurwa da na ɗan rakiya da kuɗin jin –kira (kindin c’pogo) duk waɗannan ana samunsu a cikin al’adun zance na Hausawa da na Dakarkarkari.

3.2.4 Hikimar Da Ke Cikin Tsarin Zance A Al’adar Hausawa Da Na Dakarkari:

Akwai hikimomi da yawa da ke tattare da wannan al’ada ta zance a tsakanin Hausawa da Dakarkari. Daga cikinsu kuwa sun haɗa da; Cusa soyayya a tsakanin saurayi da budurwa,don yana basu damar fahintar juna da tattauna muhimmam zantuka a tsakaninsu .Kuma wannan shi ke nuna ma jama’a ba su da wata muguwar manufa a tsakaninsu . Domin ga al’ada, duk sauaryin da baya iya zance a gidan budurwarsa to yana da wata muguwar manufa, kuma ba auren yake nema ba. Kuma idan budurwa ba ta fita zance wata alama ce ta nuna ba ta son saurayin . Don haka zance wani ma’auni ne na soyayya.  Haka kuma idan muka dubi lokaci da wuri , wannan lokacin iyaye sun dawo gida suna ganin duk wanda zai zo gidansu. Kuma wanan lokacin an ba saurayi da budurwa damar taimaka ma iyayensu wasu ayyukka da rana. Kuma wannan na nuna kunyar surukkai.

Ta fuskar amfani da ɗan rakiya kuwa, shi ɗansanda ne mai kawo rahoton duk abin da ya faru tsakanin saurayi da budurwa .Haka kuma yana zama ɗan saƙo a lokacin zance, yana kuma kare kaɗaitar saurayi da budurwa , domin a wannan lokacin tana ɗan yin wasa da shi,don haka za ta fi ɗaukan lokaci tana zancen. Bayan waɗannan,ɗan rakiya yana taimakawa wajen kai bante.Su kuwa kuɗɗin jin- kira (kindin c’pogo) suna ƙara soyayya domin Hausawa na cewa: “Hannun da ke karɓa ba ya cewa a’a” Kuma ƙyautar tana ƙara martaba da daraja a idon budurwa da gidansu.

Bisa ga wannan dan tsokaci, za mu fahinci al’adar zance ta taka muhimmiyar rawa wajen gwagwarmayar neman auren Hausawa da na Dakarkari.

3.3 Matsayin Iyaye Wurin Neman Aure

Bisa ga tsarin neman auren Hausawa,  iyaye suna da muhimmanci. Da yake aure al’ada ce da ake yi domin zaman rayuwa baki ɗaya, don haka, al’adar Bahaushe an aza ma iyaye haƙƙin neman ma ‘ya’yansu matar aure. Don haka, iyaye suna biɗan ma ‘ya’yansu aure a gida mai asali domin su suka san tarihin gidajen, kuma suna da masaniyar halin tarbiyar gidan. Anan iyaye suna kulawa da wannan ne domin kaucewa gurɓata zuriyarsu da wani jini mai tarihin wani abin kunya. Misali sata ko wata cuta ta musamman kamar kuturta.

Haka kuma, a lokacin neman auren, iyaye suna duban inda yarinya za ta samu abinci. Domin abin kunya ne ga Bahaushe ya bada aure ga gida wanda ba ya ciyar da matarsa. Za ta yi yu domin tabbatar da wannan ne ake yin al’adun  bikin ɗauko Maiki a kwatarkwashi ta yankin Zamfara a matsayin wani ma’auni na nuna jarumtar saurayi.

Iyaye suna bada shawarwari kuma ga su da cika fuska da iya gabatar da Magana.

3.3.1 Fitowa gida (Biɗar Iyaye) A Neman Auren Hausawa

Iyaye suna fitowa biɗar aure ne idan sun tabbatar da mutuncin gidan da za su neman auren. Anan idan za su fita sukan ta fi da goro da ‘yan wasu kuɗi da za a aza sama. Kuma mafi yawa akan samu dattijai ne ‘yan uwa su kai waɗannan kaya. Duk da yake a yanzu ana samun   masu bada auren ba tare da sanin dangin uwa ba balle na uba. Bisa ga tsari, idan iyaye suka isa gidan yarinya, bayan sun gaisa sai su bayyana abin da ke tafe da su.musamman kuma ana wannan neman ne a wurin iyayen yarinya ko wani danginta na jini kuma namiji. A wannan lokacin sai iyayen yarinya suma su faɗi nasu bayani na amincewarsu ko rashin amincewarsu. Duk da haka, wani lokaci tun yarinya na ciki ko jaririya ake fara neman aurenta ta hanyar ba da zobe da za a sanya mata mai nuna an yi kammenta kenan.

3.3.2 Gaisuwar Abokai

Wannan wani mataki ne daga cikin tsarin neman auren Hausawa. Abokai su ne waɗanda mutum ke zaune da su lafiya suna yawo tare da cin abinci tare da dai sauran mu’amaloli. Ita wannan al’ada ana yin ta ne bayan saurayi da budurwa sun sasanta kansu da niyyar auren juna, kuma iyaye sun isa gida neman auren an kuma amsa saurayin ya ci gaba da neman auren. Anan ne saurayi zai samu abokansa domin su fito gaisuwa.A irin wannan lokacin ne ake tura aboakai gaisuwar sanin dangin yarinyar. A al’adance idan za a tafi wannan gaisuwar, ana zuwa da goro ne da wasu ‘yan kuɗi wanda za su rinƙa bayarwa. Kuma lokacin wannan gaisuwar, saurayin da ke  neman auren baya magana sai dai abokansa su yi. Wannan al’adar ana yin ta ne domin gabatar da saurayi ga sauran dangi domin su san sa, shi kuma ya san su.

3.3. 3 Tsarin Neman Auren (c’gai) Dakarkari

Lelna (Dakarkari) sun ba aure muhimmanci, don haka sun shimfiɗa wani tsari na neman aure tun kafin zuwan addini. Bisa ga al’ada, Dakarkari suna da hanyoyi da dama na neman aure. Daga cikin su kuwa, akwai ta hanyoar iyaye da kuma tsakanin saurayi da budurwa.

Ta hanyar iyaye: Dakarkari sun ba iyaye daraja sosai ta yadda aka bar masu ragamar neman  ma  ‘ya’yansu aure. Domin a al’adance yaro bai da iznin neman ma kansa aure. Tadurga U.,(1997) yana cewa:

Idan aka haifi yarinya a gida,

idan akwai tsohon da ke son neman

wa ɗansa, yana iya shaida wa iyayen

wannan yarinya tun tana jaririya da

cewa ya kama wa ɗansa wannan

yarinya. To wannan ya tabbata domin

ba wanda zai auri wannan yarinya

sai yaron.

Irin wannan neman auren,  ana yin sa ne ta hanyar al’ƙawali inda za a kama ma yaro mata ta hanyar kai wani jan zobe. Wannan zoben za a sanya wa yarinya shaidar cewa an yi mata kame.

Amma wasu Dakarkari nasu al’adar ta banbanta. Misali hirar da na yi da Ibrahim Wakaso Galadiman Rambo cewa ya yi:

za a kai masara goyo uku a gidan

yarinyar kame, idan wata shekara ta dawo

a kai biyar. Anan uban yarinya zai

samu kuɗi wuri uku, a samu ɗan

ƙwarya a sa a ciki, idan an kai

wannan kayan, to rannan ne aka

tabbatar da kamen auren.



Yin wannan shi ya tabbatar da cewa, iyayen suna son haɗa jini da juna. Ya ƙara da cewa, bayan an tabbatar da kamen idan yaro ya kai shekara goma sha shida zuwa ashirin ne zai shiga golmo. Daga nan sai a samu kwandon dawa a kai gidan sarukkai.

Ita wannan al’ada ta golmo wata bauta ce da saurayi yake wa surukkansa na tsawon shekara bakwai ko ƙasa da haka. A wannan lokacin golmo (nema), saurayi zai rinƙa zuwa gonar surukkai tare da takwarorinsa suna noma. Idan rani ya yi, ya yo masu hakin baibayan ɗaki. Sai dai a yanzu akwai damar idan saurayi ba zai iya cika shekarun bakwai ba, sai a yanka masa wasu kuɗi ya biya a madadin sauran shekarun da ba zai yi golmo ba.

A hirar da na yi da mai unguwar Zuttu (maigari kwai-masa) cewa ya yi:

Iyaye su ne ke biɗan ma yaransu aure,

duk da yake yanzu yara suke neman

ma kansu aure musamman a wurin bukukuwa

ko kasuwanni. Amma mai biɗa ba ya kai

komai sai iyaye sun haɗa kansu.



Ya ƙara da cewa bayan an samu haɗuwar kan iyaye za a kai wasu kaya da ake cema ‘uv-kwanta’  inda ake samun turmin Atamfa da Sabulu da Mai a samu wata tsohuwa da wasu daga cikin dangi a kai gidan yarinya. Daga nan ne saurayi zai shiga golmo bayan ya yi ‘yadato’ na ƙare samartakansa.

Amma mafi yawa a yanzu, saurayi ke fara neman wa kansa aure ta hanyar sasantawa tsakaninsa da budurwar. Daga baya a tura iyaye gidan budurwa neman auren.

Bisa ga wannna za mu fahimci Dakarkari suna da tsarin neman aure kusan bai ɗaya da na Hausawa musamman idan muka dubi matsayin Iyaye da fitowar Iyaye da gaisuwar abokai da sauransu.

3.3.3 Bambanci da kamancin tsakanin neman auren Hausawa da na Dakarkari.

Al’umar Hausawa da na Dakarkari suna da cikkaken tsari na neman aure. Kuma mafi yawan tsarin ya yi kama da juna illa wasu ‘yan wurare da ba  a rasa ba.

Ta fuskan bambanci, abin da ya shafi gaisuwar abokai; Hausawa suna zuwa da goro da wasu ‘yan kuɗi a sama. Amma su Dakarkari ba a zuwa da komai.

Ta fuskar kamanci kuwa, anan za mu ga cewa dukkan ƙabilun, iyaye sun taka muhimmiyar rawa wajen neman aure, kana sun amince a nemi yarinya aure tun ana da cikinta, wani lokaci kuwa sai bayan ta yi wayo. Haka kuma, a dukkan ƙabilun iyayen namiji ne ke zuwa wurin iyayen yarinya neman aure; kuma a wannan lokacin iyayen na zuwa da wata ‘yar kyauta ga dukkan ƙabilun. Bayan wannan kuma, a lokacin neman samari suna yi ma gidajen surukkansu wata ‘yar bauta (golmo ko gayya)  da dai sauransu. Don haka anan za mu ga cewa waɗannan al’adu sun yi kama da juna ƙwarai da gaske.

3.3.4 Falsafar Da Ke Cikin Tsarin Neman Auren Hausawa Da Na Dakarkari

Bisa ga al’ada, Hausawa da Dakarkari sun ba neman aure muhimmanci sosai. Wannan kuwa ba zai rasa nasaba da irin hikima ko falsafar da ke tattare da wannan tsari na neman auren ba.

Da farko dai za mu ga cewa, falsafan sanya iyaye wurin neman aure shi ne cewa: Su ke da tarihin kowane gida domin sun ga jiya sun ga yau. Da yake Bahaushe ko badakkare baya son haɗa jininsa da wani jini wanda ke da tarihin wani abin kunya. Kuma iyaye suna zaɓen gida mai tarbiya, domin ga al’ada ba a barin yara kara zube ba tare da jagorancin iyayensu ba. Kuma iyaye suna duban halayen yara domin gane cancantarsu ko rashin cancantarsu. Wata falsafa kuma ita ce, ƙara fahimtar juna da nuna soyayya tun kafin auren. Wannan na haifar da kyautata halayen saurayi da budurwa. Haka kuma gaisuwar abokai na tabbatar da maganar da iyaye suka yi a lokacin da suka fita nema wa ɗansu mata. Wannan gaisuwar tana nuna yaron ya amsa shi ma yana son yarinyar. Kuma a wanan lokacin yana sa iyaye su san surikinsu musamman abin da ya shafi ƙirar jikinsa, irin kaifin hankalinsa da dai sauransu.

3.4. 1 Tsarin Na-Gani-Ina-So A Al’adar Hausawa

A  al’dar Hausawa, bayan Magana tsakanin saurayi da budurwa da iyayen yaro da na yarinya ta zauna , watau an amince wa juna. Daga nan ne za a kai kayan Na-gani-ina –so, su waɗannan kayan galibi ana samun wasu dattijai maza ko mata ne su kai waɗannan kayan . zaɓen dattijai ba zai rasa nasaba da irin matsayinsu a cikin al’umma ba, domin sun fi sanin irin lafuzzan da za su yi amfani da su. kuma galibi waɗannan kaya ana haɗawa da ‘yan wasu kuɗi da goro a ciki, sauran kayan sun haɗa da tufafin sawa da na kwalliya. Anan yawan kayan ya danganta ne da irin ƙarfin arzikin gidan saurayi.

Bayan an kai waɗannan kayan ne za a dawo da bayanin da aka samo daga gidan budurwa dangane da kayan.Waɗananan kayan za a rinƙa yawo da su gida-gida ana nuna ma dangin yarinya , wani lokaci ma, goro da kuɗin da aka aza sama ana rabawa sauran dangin shaidar cewa ‘yarsu ta sami masoyi . Duk da yake kafin shigowar addini, Hausawa suna amfani da kayan gona ne da wuri a matsayin kayan na-gani-ina-so.

3.4.2 Tsarin Na-gani-Ina-so A  Al’adar Dakarkari

Dakarkari su ma suna da tsari na musammam dangane da al’adar na-gani-ina-so.  Duk da yake ana samun bambance bambance tsakanin wannan yanki na Dakarkari zuwa wancan.  Bayan saurayi da budurwa da iyayensu sun amince da juna, magana ta zauna.  Daga nan ne za a kai waɗannan  kayan riƙo . Duk da yake wani lokaci iyaye na kai kayan ba tare da sanin saurayi ko budurwa ba. Domin  a  al’adance yara ba su da ikon kansu sai abin da iyaye suka zantar a kansu.

A wani sashe na Dakarkari kuwa, iyaye suna kai kuɗi wuri ashirin da jan zobe wanda za a sanya wa yarinya a matsayin shaidar ana kamenta. A wajen Dakarkarin Rambo kuwa, ana fara kai masara goyo uku, idan wata shekara ta zagayo a kai masara goyo biyar. Haka kuma uban yarinya zai samu kuɗi wuri uku ya kai, yin wannan shi ke tabbatar da kamen yarinya . Bayan saurayi ya kai shekara ashirin sai ya kai kwandon dawa gidan surukkansa. Haka kuma, zai yi asabari biyu ya kai gidan surukkansa.Amma a yanzu bayan shigowan addini, Dakarkari suna amfani da kudi ne da wasu ‘yan kaya na sawa da na shafe-shafe a matsayin kayan na-gani-ina-so.

3.4.3 Bambanci Da Kamancin Tsarin Na-gani-Ina-so A Al’umar Hausawa Da Na Dakarkari.

Bisa ga al’ada musamman kafin shigowan addini,  bincike ya gano cewa, kusan duk tsarin aiwatar da wannan al’ada ta na-gani-ina-so ɗaya ne tsakanin Hausawa da Dakarkari sai dai ɗan abin da ba a rasa ba.

Da farko dai za mu ga cewa dukkan Hausawa da Dakarkari suna amfani da kayan gona da zobe kafin zuwan addini, kuma waɗannan kayan gona sun danganta da irin waɗanda ake nomawa a kowani yanki . Kuma dukkan ƙabilun suna sanya iyaye dattijai wurin kai kayan na-gani-ina-so. Ta fuskar lokacin kai kayan kuwa, duk tsari ɗaya suke bi, domin ba a kai su sai an tabbatar da soyayya a tsakanin iyaye da saurayi da budurwa.

Bayan haka, ɗaukan kayan yana nuna an karɓi manemin, rashin ɗauka kuwa yana nuna manemin bai samu karɓuwa ba. Wannan tsarin kuwa duk ɗaya ne a tsakanin al’umar Hausawa da Dakarkari.

3.4.4 Falsafar Al’adar Na-gani-ina-so A Al’umar Hausawa Da Dakarkari

Dangane da falsafar da ke tattare a cikin wannan al’ada kuwa , gasu kamar haka:

Da farko dai wannan wata alama ce mai tabbatar wa iyaye da sauran dangi cewa ‘yarsu ko ɗansu ya samu masoyi . Domin waɗannan kayan na-gani-ina-so su ake rabawa sauran dangi su shaida cewa an fito gida neman ‘yarsu.

Wata falsafa ita ce , karɓar wannan kayan na nuna irin karɓuwar da saurayi ya samu a gidan budurwa. Domin a al’adar Bahaushe, idan aka bada tukuici, to ya samu karɓuwa, idan kuwa aka karɓi kayan  aka ajiye ba tare da wata Magana ba , wanna yana nuna akwai shakku ga mabiɗin. Amma idan aka tsaya binciken kayan, yana nuna dama akwai wani mabiɗi. Anan za mu fahinci waɗannan kayan tamkar wani madubi ne da manemi zai kalla ya san matsayinsa.

Kayan ga Hausawa da Dakarkari, suna matsayin nizani na auna arzikin mabiɗi. Don haka, kayan suna ƙara ko rage darajjar mabiɗi a gidan yarinya ko al’umma baki ɗaya. Musammam idan muka dubi yadda ake yawo da kayan ana gwada ma dangi. Kuma waɗannan kayan suna ƙara danƙon soyayya a tsakanin saurayi da budurwa . Yawansu na sa budurwa alfahari , amma idan ba su cika ido ba, za a ji nauyin bayyana su.

A al’adance wasu na ganin ana iya auna arzikin yarinya tun daga irin kayanta na na-gani-ina-so. Domin idan ta samu kaya masu yawa , to wannan wata alama ce mai nuna budurwar tana da ƙashin arziki, idan kuwa kayan ba su cika ido ba , to wannan na nuna ba ta da ƙashin arziki.

4.0 Kammalawa


Al’adun alumma sun bambanta daga wannan al’umma zuwa waccan. Haka al’adun aure suna da yawa, kuma kowace al’ada akwai yadda kowace al’umma ke aiwatar da ita. A wasu al’adun sukan ɗauki tsari ɗaya wajen aiwatarwa, wasu kuwa ana samun wasu ‘yan bambance-bambance wajen aiwatar da su a tsakanin wannan al’umma zuwa wata al’umma.

Bisa ga abin da wannan maƙala ta yi ɗan taƙaitaccen bayani a kansu, za mu ga cewa an yi ƙoƙarin kawo wasu daga cikin gwagwarmayar da ake yi lokacin neman auren Hausawa da na Dakarkari. Don haka, an zaɓi wasu al’adu ne aka yi bayaninsu sama-sama. Daga cikin al’adun da aka duba sun haɗa da: Al’adun soyayya a tsakanin saurayi da budurwa da zance ko taɗi da matsayin ɗanrakiya da matsayin iyaye da al’adar na-gani-ina-so da sauransu.

Muƙalar ta yi ƙoƙarin kawo kamanci da bambance-bambancen da ake samu wurin aiwatar da waɗannan al’adu a tsakanin al’umar Hausawa da na Dakarkari. An yi ƙoƙarin kawo wasu hikimomi ko falsafar da ke damfare a cikin waɗannan al’adu a tsakanin waɗannan alummomi.

A ƙarshe bisa ga ɗan abin da  wannan maƙala ta yi bayani a kai , za mu fahinci cewa al’umar Hausawa da na Dakarkari suna da tsari kusan iri ɗaya da juna musamman abin da ya shafi al’adun neman aure da falsafar da ke cikin aiwatar da waɗannan al’adun a tsakanin al’ummominsu. Ba shakka, wannan nazarin zai ƙara sa fahintar juna wanda zai haifar da zamantakewa mai inganci da nagarta ba tare da kushe wa juna ba a tsakanin waɗannan al’ummomi.

MANAZARTA



Post a Comment

0 Comments