Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 33: Babban Abokin Gaba


    Akwai wata da ubanta ya yi niyyar yi mata auren dole. Ba ta son wanda za ta aura, amma ta yi alwashin cewa ubanta na mutuwa auren nan ya ƙare. Ta ƙi haihuwa kuwa, ikon Allah sai uban ya mutu. Ta fita daga gidan ta


    Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 33: Babban Abokin Gaba

    Baban Manar Alƙasim
    Zauren Markazus Sunnah

    Duk wani mahaluki da ka gani ƙoƙari yake yi ya hau kan hanyar nasara, idan kuma ya bi ta a hankali zai isa har inda take, in ya same ta kuma ya lallaba ta ya yi ta cin moriyarta har ya koma ga Allah, in ba ta sullube ko wani ya ƙwace masa ita ba kenan, sai dai duk lokacin da zai kama hanya yana da wata muguwar abokiyar gaba guda daya wace koda yaushe za ta riƙa tadiye masa ƙafa, in ya zo da tsautsayi ya fadi, an gama kenan, wato "Gaggawa" wannan abokiyar gabar daidaikun mutane ne suke iya kaiwa ga nasara matuƙar za ta saka su a gaba, kai ko ka hau kan hanyar ba ta gan ka ba in ta hango ka ba za ka ƙarisa ga nasara ba, sai dai ka sake dauko tafiyar.
    .
    1) Mutum ne ya shiga aikin gwamnati, manufarsa a koda yaushe ya tara arziƙi, yana da damar da zai tara din tunda yana aikin gwamnati kuma yana samun albashinsa mai tsoka, da zai yi manejin dan abin hannunsa ya bude wata sana'a ya yi shuka dukiyarsa a can ya jira ta yi yabanya ya girbe da ya sami tikitin zuwa ga nasara, amma sai ya sami wata shawara da aka ce ya ajiye aikin ya shiga siyasa.
    .
    Ya kuwa ajiye din, dan abinda ya tara da sauran kayan sana'ar duk ya antaya su a cikin siyasar, a ƙarshe aka kada shi tun a zaben fidda gwani, gaskiya ya yi gaggawa, da ya shiga siyasar kar ya tsaya takara, ya karanci mazabun da mutanen dake cikinsu, da abinda suke so, ya yi ƙoƙarin sabo da masu ruwa da tsaki na yankin, in suka yarda da shi za su amince masa su zabe shi tare da sakankancewar in ya samu zai dube su, amma daukar tsuraitattun mutane ba tare da tabbatar da matsayar masu zabe ba wannan gaggawa ne.
    .
    2) Abokina yake ba ni kabarin wata mata da ta sayar masa da wani takalmi a kan Naira dubu uku, alhali kudinsa bai wuce Naira dari takwas ba, tana ta jin dadin cewa ta sami riba, sai na ce masa a kaikaice -ina ƙoƙarin sanin matakin da ya dauka- "Ai nan gaba kar ka yi saurin sayen kayanta sai ka ji kudinsa a wani wurin tukun" ya ce "Allah ya kyauta! Ai daga yanzu an gama kenan, ni da sayen kayanta har abada, kai! Wallahi in ma na ga wani zai saya sai na hana shi!" A zuciyata na ce ta yi gaggawa, da ta fada masa gaskiya ko ta yi haƙuri da ƙaramar riba kullum za ta ci kudinsa, amma ta yi gaggawa.
    .
    3) Akwai wata da ubanta ya yi niyyar yi mata auren dole. Ba ta son wanda za ta aura, amma ta yi alwashin cewa ubanta na mutuwa auren nan ya ƙare. Ta ƙi haihuwa kuwa, ikon Allah sai uban ya mutu. Ta fita daga gidan ta auri wanda take so, ƙila ta ci nasara, don ta hayyafa kafin ta rasu ita ma, amma wata sai ta bazama karuwanci an yi biyu babu, wata kuwa rijiya ta fada ta mutu shi ma haka, wata mijin ta kashe ita ma aka kashe ta, duka dai sun yi gaggawa ba su auri wanda suke so ba, na ga wace ta auri saurayinta na farko bayan shekara 60, ta yi nasara.
    .
    4) Wani ne aka saka shi wurin samun kudi a wata ma'aikata, tsakani da Allah yana samun kudin nan ba kadan ba, amma shedan ya zuga shi ya hada baki da barayi aka saci kudinnan son rai, a ƙarshe aka yi bincike aka gano barayin suka tona masa asiri, aka kore shi a wurin aikin aka ƙwace wasu abubuwan da ya mallaka kuma aka tura shi gidan yari, na ce ya yi gaggawa, da ya bi a hankali ta hanyar da ta dace zai sami wannan kudin kuma ga mutuncinsa ga aikinsa, yanzu ba ko daya, galibin Samari gaggawa ce da su.
    .
    5) Akwai wani da ya fito neman auren wata yarinya, soyayyar ta jima ana yinta, har dai ta kai ga an yi aure ashe ya dirka mata ciki tun tana gida, saboda tunanin haihuwa a wata 3 bayan aure sai suka yi ƙoƙarin zubar da cikin, anan asirinsu ya tonu, na ce sun yi gaggawa ne, da sun yi haƙuri za su cimma burinsu, maganar ta 'yan watanni ce, an ma kusa gamawa, ai kuwa tana warkewa ya dauke ta suka tsere, na ce ita ma wata gaggawar ce, da in ta warke za su ci gaba da aurensu hankali a kwance don cikin shi ya yi abinsa, in ma wata mazahabar da aka ce sai an sake daura aure ne sai a yi, su ci gaba da bushasharsu, amma sun yi gaggawa.
    .
    6) Wani limami ne ya yi jinkiri wajen fitowa salla, al'adar mutanemmu koda hamsu salawati ne liman ya yi jinkiri lokaci sai dai ya ji ana yi, don in ya ƙara wani lokaci 'yan oya-oya za su nemi a tada sallar don zama cikin masallaci ba za su iya ba, bare kuma sallar idi, har an tura wani sai ga ainihin limamin ya iso, ai kuwa sai ya tunkude wanda aka nada don ya yi sallar ranar kacal, a dalilin aikin da limamin ya yi shikenan ya rasa kimancin masallacin gaba daya, na ce ya yi gaggawa ne, da ya haƙura ƙila da ba mu sami wannan labarin ba, amma tasarrufin da ya yi a ranar sai ya sure wa kowa, a dalilin haka kuma ya yi asarar matsayinsa.
    .
    7) Wani dalibi ne da ya kwashe shekara hudu yana karatu, ma'ana dai ya kammala karatunsa gaba daya, sai wani tunani na satar amsa ya zo masa a ranar ƙarshe ta jarabawar ƙarshe, ai kuwa aka kama shi, dalilin sallamarsa kenan a makarantar, duk abinda ya kwashe shekaru 4 dinnan yana yi ya sayar da su a wannnan ranar, na ce ya yi gaggawa, da ya haƙura zai ci jarabawar ranar koda ba yabo ba fallasa ne, tunda yana da ƙoƙari a wasu darussan wani sai ya tada wani, in ma faduwa ya yi wannan darasin kacal zai maimaita a shekara mai zuwa, amma ya yi gaggawa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.