Shi
ma É—ayan ya so a ce an É—auke shi don kuwa ya
iya aikin kamar wancan, amma ana ƙimanta mutum ne da
abin da...
Hanyoyin Cin Nasara a
Rayuwa 32: Mutane Kala Biyu Ne
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
Dangane da aiki ko sana'a
mutane sun kasu zuwa gida biyu:-
a) Mai jin dadin aikinsa:
Wannan kam yana son aikinsa kuma yana jin dadin ganin abinda yake yi, kullum
alla-alla yake yi gari ya waye ya kama hanya, don ko kamin ya bar aikin ya dawo
gida sai da ya tabbatar ya kammala aikin yau gaba daya, kuma ya shirya abinda
zai taras gobe, yakan bar aikin ne cikin zaƙuwar
dawowa ya taras da shi, wannan ya sa wani zai gama da na yau har ya dan rage na
gobe ma yadda in ya zo aikin zai yi masa sauƙi.
.
Irin waÉ—annan
mutanen ba su da wani tunani na rabuwa da aikin don suna jin dadinsa, koda kuwa
wurin aikin nasu ne, ko nawani ne sukan yi ne a biya su, wani ma sai ka rantse
da Allah wurin nasa ne saboda ƙaunar
aikin da yake yi, na ga wani Basakkwace da ya riƙe wa
wani Bakano shago da amana, na yi zaton yaron wancan ne, ashe bariki ce kawai
ta hada su, har dai Bakanonnan ya yi ƙarfi
ya sayi wani shagon kusa da wannan ya maƙare
shi da kaya, koda ya tashi tarewa sai ya ce ya bar wa yaronnan nasa tsohon shi
ya koma sabon, lamarin ya ba ni sha'awa matuƙa,
bai yi haka ba sai don ganin gaskiya da amanar yaron da kuma jajurcewarsa, na
ga wuraren aiki da dama amma ban ga rabuwar da ta ba ni sha'awa kamar wannan
ba.
.
Wanda duk yake ƙaunar aikinsa za ka taras kullum neman
ci-gaban aikin yake yi, yana ta nemo hikima ta kowani bangare yadda zai habbaka
aikin nasa, ko ya sauwaƙe
shi, ko ya inganta shi, ko kuma ya ƙawata
shi ga idon jama'a, tunaninsa a kullum shi ne ci gaba, bai damu da cewa aikin
nasa ne ko na ubangidansa ba, irin wannan ne sai ka ga a ƙarshe ubangidan nasa ya kyautata masa
sanadiyyar aikinsa, na san wani da ya je koyon aiki a wurin wani abokina ko
shekara cikakka bai yi ba har ya fara tunani da fadin cewa ogan nasa bai kai
shi sanin kan aikin ba, wannan a ganina butulci ne da rashin sanin ya kamata, ƙila kuma zaman ba zai wani dade sosai
ba, saboda raini ya fara shigowa tsakiya, duk inda aka fara samun irin wannan
to kuwa akwai matsala.
.
b) Yana aikin ba don yana so
ba: Wannan za ka taras don dole yake yi, irin bai sami wanda ya fi shi ba, ko
an matsa masa ne a gida, ko kuma bai son zaman banza dole ya fara, ko shi dan
na kashewa kawai yake nema bai É—auke shi a matsayin sana'a
ba, a irin wannan yana yi ba dole ne ya je aiki ba, a kullum yana neman dan
dalili ne wanda zai maƙale
da shi ya ƙi zuwa aikin, ko in
ya je din ya dawo gida ko ya wuce yawonsa, ko bai yi aikin komai ba za ka taras
da shi a gajiye yake, in damina ta zo ko hadari ya gani ba zai fita aiki ba to
bare a ce an dan yi yayyafi, na ga wanda ya ƙi
zuwa aiki da aka tambaye shi dalili sai ya ce wai mai gadin abokinsa ne ya
karye kuma abokin ya yi tafiya shi ne ya je ya dan zauna masa.
.
Shi abokin ya tafi aiki,
koda shi ne ya karye bai da 'yan uwa ne da za su zauna masa bare kuma mai
gadinsa? Abin gwanin ban mamaki, irin waÉ—annan
mutanen ba yadda za a yi su yi tunanin bunƙasa
aikin bare har su yi tunanin kawo ci-gabansa, za ka iya kwatanta dalibai biyu
da suka je yi wa ƙasa
hidima a wani kamfani, daya daga cikinsu ya dage yana ta aiki tuƙuru, a cewarsa yana ƙoƙarin
sanin madafan aiki ne, wanda tabbas haka abin yake, na biyun kuwa yana ganin
shi yi wa ƙasa hidima yake, bai
ga dalilin da zai riƙa ƙarar da ƙarfinsa
a kan wani ƙaton banza ba, yau in
ya zo aiki gobe ya ƙi,
wani lokacin ma ya ce bai da lafiya ya yi tafiyarsa sai bayan mako guda ya
dawo, a ƙarshe kamfanin suka dauki wancan aiki
yana kammala hidimarsa.
.
Shi ma É—ayan
ya so a ce an É—auke shi don kuwa ya iya aikin kamar
wancan, amma ana ƙimanta
mutum ne da abin da
yake aiwatarwa. Wanda
bai sha'awar aiki in ka je wurin za ka gan shi da wayarsa yana lallatsawa, ko wasa da yara
ko kallon talabijin, bai da wani lokaci da zai bata don ganin ci-gaban wuri,
wani ma bai damu da a kore shi ba, kamar wani mai aski da na ga yana ba yaronsa
kashi, wai ya bude shagon ya je yana yi wa maƙwanmbcinsa
mai nama aiki don a ba shi kudin da bai wuce Naira 50 ba, ubangidan nasa ya zane
shi ya ce "Duk tsiyar da za ka yi wallahi ba zan kore ka ba, kuma sai ka
yi aikinnan" ya kwaso ashar dinsa ya watsa, wai ashe uwarsa ta kawo shi
shi kuma ya fi son inda zai yi aiki ne a biya shi wahalarsa ba wai wurin wani
koyon sana'a ba, ka ga wannan da wahala ya yi wani abin azo a gani.
.
Ina ganin akwai bambanci
tsakanin ƙwadugo da sana'a,
duka aiki ne kowa kuma da hanyar cin abincinsa, amma galibi 'yan ƙwadugo sukan fita ne ba tare da sanin
ina za su ko wani irin aiki za su yi ba, kamar leburorin da na sani, ma'aikatan
gini ne, amma ba ƙananan
ayyuka da ba su iya ba, su ne gini, fenti, ginan rami kamar masai da rijiya,
sanya wuta a daki, tabbatar da masai na korawa da ruwa da sauransu, wata rana a
samu da yawa wata rana a rasa gaba daya, akan sami ranar da babu ma gaba daya,
irin wannan za ka taras hatta aikin akwai yanayin lokacin da aka fi samu, akwai
lokacin da ba a samun komai ma, yadda mutum ya fita haka zai dawo hannu Rabbana.
.
Amma in ka koyi aiki mai
wuri tabbatacce kamar fawa, ƙira,
shago, kanikanci da sauransu kana da matabbata, in kai mai himma ne cikin dan
lokaci ƙarami mutum zai yi nasa, sai ka ga ya
zama wani abu, a ƙarshe
sai dai shi ma ya sami yaron da zai zauna masa, in ya yi dace shi ma ya zama
babba kenan, a lokacin zai ga amfanin ƙoƙarin da ya yi, in ya sami yaro mai ƙwazo tabbas zai sami cikakken lokacin da
zai huta, a wannan lokacin zai fara tunanin yanzu ya za a yi ya sake samun wani
wurin ya zama yana wuri biyu tunda wannan ya sami mai riƙe masa? Amfanin dagewa kenan a aiki.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.