Rayuwar Maguzawa ta yi
tanadin tsafi a kowane lungu da saƙo nata. Abdullahi (2008: 01) na cewa,
“Rayuwar Maguzawa da tsafi kamar dangantakar tsoka da jinni ce, kuma tsafi
ginshiƙi ne da ke ɗauke da rayuwarsu, wato bai keɓanta ga bauta kawai ba.” A
tunani irin na Maguzawa duk wani abu na...
Hoton Tsafin Maguzawa A Cikin Littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa
Alamuna Nuhu
Tsangayar Fasaha
Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harsuna
Jami’ar Jihar Kaduna
Alamunan@gmail.com
08030472882, 08029414085
1.0 Gabatarwa
Hausawa kan ce, “Tsafi
gaskiyar mai shi.” Hanyoyin rayuwar Maguzwa cike suke da tanade-tanade waɗanda
ke yi masu jagoranci wajen gudanar da harkokin rayuwarsu, Abdullahi (2008:01).
Rayuwar Maguzawa ta dogara ne bisa imani da tunani na gargajiya. Gargajiyar
tasu ta haɗa da addininsu, da yanayin rayuwar da suka gada iyaye da kakanni
musamman ga Maguzawan da ba su Musulunta ba.
Maƙasudin wannan nazari
shi ne fito da hoton wasu tsafe-tsafen Maguzawa da suka yi tasiri a cikin
littafin “Ƙarshen Alewa Ƙasa,” da ya ginu bisa ƙagawar Bature Gagare a matsayin
rubutaccen ƙagaggen labari. Gina labari kan Maguzawa ba zai yiwu ba a kauce wa
kawo hoton imani da tunanin rayuwarsu ta gargajiya. A taƙaice dai, nazarin ya
yi ƙoƙarin bayyana rayuwar Maguzawa ta fuskar tsafe-tsafe domin neman
biyan buƙata ta jin daɗin rayuwa, ko kawar da cuta, ko cutarwa, ko kariya da
tsaro, ko sanin gaibu da suka fito cikin wannan littafi.
2.0 Littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa
Littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa
yana ɗaya daga cikin littattafai guda bakwai na Hausa da suka sami nasara a
gasar shekarar 1980, wanda hukumar Al’adun Gargajiya ta Tarayya ta shirya
(Furniss 1996: 39-41) . Gasar an shirya ta ne domin samar da littattafan
rubutattun ƙagaggun labarai daga mawallafa ‘yan ƙasa. Marubucin littafin ya yi
rawar gani na bin ƙa’idar wannan gasa wajen rubuta littafin. Ƙa’idar ita ce, a
tsara labari domin ciyar da al’adun gargajiyar Nijeriya gaba. Shi kuwa
marubucin sai alƙalaminsa ya zaɓi Maguzawa wajen gina labarinsa. Su kuwa
Maguzawa rayuwarsu ta gargajiya ce, in kuma sun sami sauyin rayuwa akan ga
tasirin gargajiyar nan tasu a wasu ɓangarori na rayuwa.
Muhimman al’amuran
rayuwar Maguzawa da marubucin ya bayyana a littafin su ne: Farauta, da ƙira, da
noma, da bautar gargajiya, da neman aure, da shugabanci, da tsaro, da yadda ake
neman mulki, da sharholiya, da tsafi. Waɗannan suna daga cikin hoton rayuwar
Maguzawa da marubucin ya bayyana. Ko da yake ba za a ce ya fayyace komai na
rayuwarsu ba, amma dai ya kawo hoton yadda rayuwarsu take daidai iyawarsa.
3.0 Alaƙar Maguzawa da Tsafi
Rayuwar Maguzawa ta yi
tanadin tsafi a kowane lungu da saƙo nata. Abdullahi (2008: 01) na cewa,
“Rayuwar Maguzawa da tsafi kamar dangantakar tsoka da jinni ce, kuma tsafi
ginshiƙi ne da ke ɗauke da rayuwarsu, wato bai keɓanta ga bauta kawai ba.” A
tunani irin na Maguzawa duk wani abu na farin ciki idan ya faru, da taimakon
tsafinsu suka samu. Idan kuwa akasin haka ne, to akwai yiwuwar an saɓa wa
tsafi. Wannan shi ya kawo batun hidima ga tsafi domin samun amfani, da zuwa bai
wa tsafi haƙuri idan an ga mummunan abu ya faru ga wani ko al’umma gaba ɗaya.
To sai dai kowane gida ko gari ko ƙasa, da irin nasu tsafin da suke yi wa bauta
(Ibrahim 1982: 30-31) da (Bunza 2006: 39-40).
https://www.amsoshi.com/2017/11/05/falsafar-daurin-auren-maguzawa/
4.0 Hoton Tsafin Maguzawa Cikin Littafin Ƙarshen
Alewa Ƙasa
Ba za a iya cewa ga
iyakar tsafin Maguzawa ba, sai dai a yi nazarin abin da aka ji ko aka gani da
wanda wasu manazarta suka tabbatar. Hakan na faruwa ne saboda bambance-bambance
na muhalli da ake samu a tsakanin Maguzawan, amma duk aljani ake yi wa
hidima. Hanyoyin da ake bi ne suke shan bamban. Daga cikin tsafin da wannan
nazari ya hango hotonsa a littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa akwai:
4.1 Tsafin Bauta
Wannan tsafi shi ne
tsafin da aka ɗora shi kan wani abu musamman aljani a wani lokaci na musamman.
Ibrahim (1982: 30-33), da Sheshe (1989: 18-21) sun bayyana cewa irin
wannan tsafin shi ne wanda Kanawa suka yi wa Tsumburbura a dutsen Dala. Shi
kuwa Bunza (2006: 40) cewa ya yi, tsafin bauta tsafi ne wanda ake gudanarwa
wajen wasu bukukuwan ta hanyar yi wa iskoki hidima ana bautar su. Iskoki na
halarce a wurin, don haka kai tsaye za su taimaka.
Cikin littafin an
bayyana mutanen garin Tsaunin Gwano cewa Maguzawa ne. Suna yin bautar gargajiya
na neman albarkar noma, da sauran bukatun rayuwa ga wani aljani da ke cikin
suri a duk shekara. Dangane da wannan zance, ga abin da marubucin ke
cewa:
“Ita dai fadar Sarkin
Dodanni wani irin wuri ne inda yake da wani irin babban suri wanda girmansa ya
kai tsawon mutum uku dogaye. Wannan suri yana ƙarƙashin wata babbar tsamiya ce
kuma. A kowace rana Sarkin Arna yakan sanya yaranshi su share wurin nan fes.
Sarkin Arna da jama’arsa talakawa, sun yarda cewa wai a cikin wannan surin
akwai wani tsohon aljani, shi wannan aljanin an san shi a cikin sifar maciji,
ko da yake an ce kuma ba abin da ba ya rikiɗa.
Abin da kowa ya sani shi
ne, wannan maciji ba wani wanda ya san lokacin da ya fara zama a wannan suri,
amma ga shi har yanzu bai mutu ba. Ko da shi Sarkin Arna wanda shi ne kuma
limaminsu na tsafi, bai san lokacin da wannan abin mamaki ya fara ba, su dai
abin da suka ji kaka da kakanni shi ne: Wannan aljani sunansa Sarkin Dodanni.
Haka kuma shi ne abin da za su bauta ma wa. A kowace shekarar sarkin Arna yakan
zo ya yi sujada, kuma ya kawo ma sarkin Dodanni ‘yar gaisuwarsu. Dalilin wannan
shi ne wai domin a sami albarkar damina, hatsi ya yi kyau, kuma su roƙa a kare
su daga bala’in fari”. (Shafi na 11)
Tsafi gaskiyar mai shi.
Wannan bayani da aka tsakuro ya kawo hoton bautar gargajiya wadda Maguzawa ke
yi a zahiri. An bayyana suri wanda ke jikin tsamiya nan ne mazaunin aljanin da
ake wa bauta.[i] Ga shi akwai masu yin hidima
na tsaftace wurin, kuma sun yi imani da hakan kamar yadda suka gada daga iyaye
da kakanni. Bayanin ya nuna suna ta’allaƙa duk amfanin gona da za su samu daga
biyayyarsu ga wannan abin bautar. Haka ma suna nema tsari ne daga wannan aljani
dangane da bala’o’i da za su iya faɗa wa rayuwa. Ba sa yin bauta sai
shekara-shekara bisa jagorancin sarkin Arna ta hanyar kai wata gaisuwa ta
musamman domin neman biyan buƙata. Lallai wannan bayani hoto ne na bautar
Maguzawa a gargajiyance da aka bayyana cikin aikin adabi. Nazarce-Nazarcen
Maguzawa da aka yi , shaida ce domin tabbatar da wannan zance.
4.2 Hidima da Kiyaye Ƙa’idojin
Abin Bauta
Ma’anonin da aka bayar
na tsafi sun nuna cewa dole ne a yi wa aljani hidima kafin a sami biyan buƙatar
abin da ake nema. Bin ƙa’ida kuwa a lokacin aiwatar da tsafi ta zama dole.
Sabawa kuma na tattare da ganin mummunan sakamako. Irin wannan hidima ta ƙunshi
yin wani aiki, da kiyaye wasu dokoki ko ƙa’ida, da yin yanka na dabba. A ɓangaren
hidimar da kiyaye ƙa’idar tsafin bauta cikin littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa, an
bayyana cewa:
“A kowace rana Sarkin
Arna yakan sanya yaranshi su share wurin nan fes. Wani abin ban mamaki shi ne,
mu idan za mu kai gaisuwa wajen sarkinmu, to al’adarmu shi ne mu cire takalma
don ladabi. Wanda kuwa zai shiga turakar Sarkin Dodanni, ba wai takalma kurum
ba, duk har da tufafin jikinsa. Ko ‘yar shara ma idan sun zo su yi shara a
tsirara haihuwar uwarsu suke yi. Wannan abu tun kaka da kakanni haka
yake.” (Shafi na11-12).
Wannan al’amari na yin
hidima da bin wasu ƙa’idoji, tsafi ne kaɗai ake iya yi wa. Kodayake share wuri
kullum tsafta ne, to amma yin tsirara ya sa shi ma ya zama wani rukuni na
bautar. Yin haka kuwa ya tabbatar da abin da ke aukuwa a haƙiƙanin tsafin
Maguzawa. Wannan abu bai tsaya kan masu shara kaɗai ba, ga duk wanda zai
shiga wurin shi ma hakan zai yi. Daɗin daɗawa, sai an dubi irin gaisuwar da
suke yi wa wannan aljani a duk shekara. Nan ne za a tantance lallai suna yin
cikakkiyar hidima ta tsafi. Gaisuwar da ake kai wa aljanin duk shekara an yi
bayaninta da cewa:
“Irin gaisuwar da
sarkin Arna ke kawowa tana da nauyi ƙwarai. Watau kyautar da ake yi ita ce rai
guda na mutum. Idan za a bayar da mutum wajen sarkin Dodanni, sai Sarkin Arna
ya zo ya rusuna ya ce, “Damina ta kewayo ya Sarki. Muna roƙo a ci gaba da kare
mu. Bayan haka ni Sarkin Arna da sauran masu neman taimakon ka, mun ba ka
wane/wance (a nan sai a ambaci sunan wanda ake so za a bayar) gaisuwarmu ke nan
ta wannan shekarar ya Sarki. Na barka lafiya”. (Shafi na 11).
Tirƙashi! Hidimar da ake
yi wa tsafin wannan gari tana da nauyi ƙwarai. Ga shi Sarkin Arna yana ganewa
cikin kwana bakwai wanda aka bayar zai mutu. Idan kuwa bai mutun ba, to aljanin
ya yi fushi bai amshi gaisuwar ba, sai an sake wani. Babu wani saukakken addini
da ke irin wannan hidima face Maguzanci da masu tsafi[ii].
Duk addinin da ya gindaya ake wa wannan hidima, to lallai gargajiya ce ake yi.
4.3 Biyan Buƙatar Rayuwa
Hausawa kan ce, “Bayan
wuya, sai daɗi.” A duk lokacin da aka yi wata hidima, ana sa ran a ga amfanin
wahalar da aka yi. Tsafi al’amari ne da ya ƙunshi sha yanzu, magani yanzu.
Labarin da aka bayar a wannan littafi, ya nuna an sami biyan buƙata nan take a
wuraren da aka yi tsafi. Akkati wata Bokanya ce kuma matsafiya wadda burinta shi
ne ɗanta ya yi sarauta. Ta sami biyan buƙatarta a dalilin tsafi. Ga abin da
bayanin ya zo da shi daga littafin:
“A cikin garin nan
akwai wata tsohowar Majusiya, wadda don tsananin daɗewa a duniya har gemu
gareta. Tana harka da aljanu ƙwarai ainun, wanda ta kai har duk garin babu
kamarta, kuma ba wadda aka fi jima tsoro. Kowa ya san cewa wannan tsohuwa ta
kashe mutane wajen ɗari duk don saboda ɗanta ya sami sarauta. Wannan kuma ta
sami nasara domin a halin da ake ciki ɗanta ne a kan gadon sarautar Jinjin
Wawa. Wannan mace sunanta Akkati mai rauhani”. (Shafi na 20)
Neman biyan buƙata yana ɗaya
daga cikin ƙunshiyar ma’anar tsafi. A nan bayani ya tabbatar cewa, wannan mata
ta yi amfani da hanyar tsafi domin neman biyan buƙatar rayuwa, kuma ta samu
biyan bukata saboda ta yi imani da hanyar da ta yi amfani da ita.
4.4 Neman Kariyar Kai Da
Tsaro
Bauta ba ita kaɗai ce
dalili yin tsafi ba. Wasu sukan yi tsafi ne domin kariyar kai da tsaro. Masu
yin wannan nau’in tsafi suna yi ne saboda tsaron lalura ta ɓarayi ko abokan
gaba.[iii] Da yake masu yi sun yarda da tsafin
nasu, sai a ga sun sami kariya da tsaro na abin da suka yi wa tsafin. Akwai
wurin da aka yi amfani da tsafi domin kare kai cikin littafin na Ƙarshen
Alewa Ƙasa kamar haka:
“Akkati ta ce, “To,
ka ga abin da nake so. Idan ka isa gida kafin ka je wajen fadar Sarkin Dodanni,
ina so ka fara zuwa gidan Sarkin Arna tukuna. Idan ka shiga ciki, duk wani abin
tsoro da ya taso maka idan har ka barbaɗa wannan garin da na fara ba ka to kuwa
abin tsoron nan zai ɓace.” (Shafi na 22)
Wannan garin magani da
Akkati ta bayar a yi amfani da shi na tsafi ne. Dalili kuwa shi ne, matsafiya
ce ta bayar da shi. Haka kuma daga an barbaɗa garin maganin abin da ya bayyana
na tsoro zai ɓace. Irin wannan aiki na al’ajabi kuma nan take sai dai tsafi.
Matar ta sake ba Mailoma wani magani na kare kai inda aka ce:
“To yanzu ina fata ka
amince da ni. Sai ta ɗauko wani jiƙon magani ta ce amshi sha. Mailoma ya kafa
kai ya shanye ruwan magani. Akkati ta ce, “Wannan asiri na rashin tsoro ne.
Idan ka yi gaba ka yi gaba ke nan”. (Shafi na 20-21)
Abin da wanann mata ta
ba Mailoma, da kuma irin aikin da maganin zai yi idan an yi amfani da shi, shi
ake kira tsafi. Duk abin da zai yi maganin rashin tsoro, kuma ya sa mutum idan
ya yi gaba babu dawowa baya, tsafi ne mahaɗinsa ko ma tsafin ne dukansa.
A ɗaya ɓangaren kuwa,
akan sami tsafin da ake yi domin tsaro na dukiya ko makamancin haka. Fitaccen
tsafin da ke yin tsaro a al’ummar Maguzawa shi ne “Tsafin Uwar Goma.” Tsafin
Uwar Goma shi ne tsafin da Maguzawa suka yi imanin cewa yana ba su albarkar
noma, da tsare shi daga ɓarayi masu sata, (Ibrahim 1982: 32-33) da
(Sheshe 1989:17) da (Bunza 2006: 40). Cikin wannan fasali an sami wurin da aka
yi amfani da tsafi domin tsaro inda marubucin ke cewa:
“Yana nan a bisa
Katanga yana kallon gidan nan sai tsafin Sarkin Arna ya shiga aikinsa. A nan
sai wani abin mamaki ya faru. Mailoma ya ji kansa ya ba da wani abu dum. Ƙwaram
babu gafara sai ƙura ta turnuƙe gidan nan duk. Iska ya kwashi Mailoma zai
wurgar da shi ya faɗo ya karairaye. A nan gaban idon Mailoma sai kurum ya ga
duk iyakar faɗin wurin nan ya koma teku ga ruwa nan fari fat har da farin wata.
Babban abin da ya ƙara ba shi tsoro shi ne, da wata igiya ta murɗo
wajensa kamar za ta tafi da shi. A cikin igiyar ruwan kuma sai ya ga wani irin
kifi-kifi da ko labarinsa bai taɓa ji ba. Shi wannan kifi girmansa babu iyaka,
haƙoransa guda kuwa ya kusa kai tsawon Mailoma. Yana fesa ruwa ta saman kansa
kamar famfo”. (Shafi na 24-25
Duk wannan abu da ake
bayani, ya faru ne cikin ƙanƙanin lokaci. Gidan Sarkin Arna ya ɓace, ƙura ta
turniƙe. Teku ya bayyana tare da igiyar ruwa, da wani babban kifi. Wannan
al’amari tsafi ne na tsaro wanda Sarkin Arna yake da shi a gida domin tsare
gidansa, da duk abin da ke ciki. Hakan da Mailoma ya gani, tsafi ne da zai kare
Sarkin Arna daga mai son shiga gidansa domin cuta masa. Bayyanar abobuwan
al’ajabi iri daban-daban cikin ƙanƙanin lokaci domin hana baƙo shiga gidan, shi
ya tabbatar da shi tsafi na tsaro.
4.5 Tabbatar Da Ɗiyauci
Rayuwar Maguzawa ta yi
tanadi na musamman domin tabbatar da cewa yarinya Budurwa ba ta taɓa yin lalata
da ɗa namiji ba kafin ta yi aure. Akwai hanyoyi daban-daban da Maguzawa ke
amfani da su gwargwadon yadda tsarin rayuwarsu take don gudanar da wannan al’adar.[iv] Ana iya samun bambanci tsakanin Maguzawan wannan
wuri da na wancan wuri wajen yadda za a tabbatar da ɗiyauci. Cikin littafin, an
yi amfani da wannan tsafi ta wannan hanya kamar haka:
“Har ma idan dai ka
tuna, a lokacin da za ta tare gidanka, sai da Sarkin Arna ya tilasta dole sai
ta kwana a gindin kuka domin a gwada ta. Ka sani kuwa lallai wadda ta kwana
gindin kukar nan, to mutuwa za ta yi matsawar dai ta taɓa lalata da wani
namiji.” (Shafi na 21)
Ana gudanar da irin
wannan tsafi ne ga Budurwar da aka yi wa aure domin a tabbatar da ta kai ɗiyaucinta
kafin aure. Abin da ke faruwa shi ne, ita wannan bishiyar Kuka da aka ambata
(cikin rubutu mai tafiyar tsutsa) nan ne wurin da tsafin yake domin aiwatar da
wannan al’adar. Idan kuwa Budurwata kuskura ta kwana alhali ta taɓa sanin ɗa
namiji, to babu shakka za ta mutu. To amma ganin cewa Tayani ta kwana lafiya,
an yarda tsafin ya yi aiki, kuma an yarda cewa ta kare ɗiyaucinta.
4.6 Sanin Gaibu
Maguzawa sun yi imani
cewar iskar da suke yi wa bauta tana iya ba su labarin abin da zai faru kafin
faruwar lamarin. Haka kuma sun yarda cewa ta hanyar tsafi ana iya hasashen abin
da zai faru na alheri ko sharri a shekara. Hoton irin wannan tsafi na sanin
gaibu ya fito a wurin da Akkati take ba Mailoma labarinsa da abin da ya yi
dalilin mutuwar matarsa. Ga abin da take cewa:
“Mailoma za ya buɗa baki
ta ce, “ Yi shiru. A yanzu za ni ba ka labarin aka yi matar ka Tayani ta mutu.
Amma kada ka yi mamaki ko ka yi shakkar magana ta, domin gaskiya za ni ba ka ɗanyarta.”
Ta dube shi ta ce, “Sunan ka Mailoma ɗan Chiwake kuma mijin Tayani, shekarunka
sha bakwai da watanni uku da kwana uku-an haife ka da kai da ɗan’uwanka ranar
litinin, haka ne? Mailoma ya ɗaga kansa ya ce, “ E haka aka yi”. (Shafi na 20).
Waɗannan bayanai na
Akkati kai tsaye tsafi ne. Dalili kuwa, daga ganin mutun ka faɗa masa sunansa,
da wurin da ya fito, da bayanin lokacin haihuwarsa har ya zuwa lokacin da ake
magana. Daɗin daɗawa, ta faɗi shekaru da watanni da kwanakin da ya yi a duniya,
da dalilin da ya yi sanadiyyar mutuwar matarsa. Irin wannan aiki sai tsafi. Ko
da yake akwai Hausawa Musulmai da ke amfani da taurari, da ɗiyan ƙasa, da ma
wasu dabaru[v] wajen faɗin gaibu a yanzu haka.
4.7 Cutarwa
Wata hanya da ake amfani
da tsafi ita ce domin a cutar da wani ko wasu. Maguzawa sukan yi tsafi musamman
domin cutar da wani. Tana iya yiwuwa ramuwar gayya ce, ko ƙeta. A nan tsafin da
aka yi domin cutarwa an yi ne domin ƙeta. Dalili shi ne, wanda ake son yi wa
tsafin za a raba shi da ransa da kuma mulki. Haka shi ma wanda aka ba aikin,
idan ya ƙi aikatawa za a salwantar da rayuwarsa. Shi kuwa mai aikatawar, in har
ya sami sa’a burinsa ya cika. In ma wani ya yi masa wargi, to zai haɗu da ɓacin
rai. Hoton irin wannan Tsafi ya fito a cikin littafin.
“Akkati ta yi dariya ta
ce, “ Har dai idan ka kori Sarkin Dodanni daga wannan suri, to kuwa ƙaryar
Sarkin ku ta ƙare. Wannan ɗan dutsen da za ka ɗauko mani ba komi ba ne illa ran
Sarkin Arna. Idan na kashe shi sai ɗana ya gaje shi ke nan. To yanzu ka ji
gaskiya, idan kuwa ka ƙi bin umurni kai kuwa kwananka sun ƙare.” A nan kuma sai
Tayani ta sake shigo masa rai. Ya ce a ransa, bari tun da har Sarkin Arna ya
kashe mani mata, shi ma kuwa sai na kashe shi. Mts, tsiyar tsafi ke nan, ko da
an maka asiri ka mutu ba shaidu. Sai dai mutum ya rama tsafi da tsafi. Ashsha
,gashi kuwa ai duk ba wanda ya fi shegen Sarkin nan namu tsafi. Kai
ni ba za ni bari banza ta shawo ni ba, sai na rama. Idan na kashe Sarkin Dodanni
yau ɗinnan, kuma gobe sai in kashe Sarkin Arna. Har ma idan Dano ya sa baki za
ni murje shi.” (Shafi
na 22-23)
Niyyar cutarwar da
Akkati mai rauhanai da Mailoma suka shirya wa Sarkin Arna, da Sarkin Dodanni ta
hanyar tsafi ke nan. To sai dai kowannensu yana shirin ya yi cutar ne bisa wata
manufa ta daban tsakanin wanda zai yi aikin, da wanda aka sa ya yi aikin.
Bayanin ya nuna cewa akan yi tsafi a cutar da wani ba tare da an ga sheda ba.
Idan kuwa wanda aka yi wa ya san tsafi ne, shi ma yana iya ramawa ta wannan
hanya.
Kammalawa:
Nazarin hoton tsafin
Maguzawa cikin littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa, ya ƙara bayyana cewa
lungu da saƙo na rayuwar Maguzawa tsafi ne ke jagoraninsa. Haka kuma, tsafin
nasu na sha yanzu magani yanzu ne. To sai dai, nazarin ya fahinci cewa, duk
abubuwan da Maguzawa suke yi wa tsafin na neman abin duniya ne, da kare kai da
samar da tsaro, da kawar da cuta, da cutarwa. Babu wani hurumi da ke nuna samun
wani amfani a wata duniya daban da wadda ake ciki. Ke nan duk da kasancewar
tsafi hanyar rayuwar Maguzawa, suna yi ne domin amfanin rayuwar duniya. Ko da
suke yin tsafi domin bauta, ba su sa ran hidimar da suke yi ko abin da suke
bauta wa ya yi masu wata fa’ida a wata duniyar. Haka kuma, ba a iya cewa ba su
lura da hakan ba amma dai har gobe abin bai canza zani ba. Dalili shi ne,
an gaji abin ne iyaye da kakanni. Haka kuma, akwai kunya a wajen Bamaguje a ce
kowa ya saki gadon gida ba tare da samun wanda ya gaji iyaye da kakanni ba.
[i] Al’adar Hausawa ta
yarda cewa Suri da Tsamiya wurare ne na zaman aljanu. Akwai gamsasshen bayani
kan mazaunin iskoki cikin Bunza, A.M. (2006) Gadon Feɗe
Al’ada. Lagos: Tiwal Nigeria LTD. Shafi na 10-14.
[ii] Mafi yawan abin
da ake yanka ma tsafin Maguzawa shi ne dabbobi, ko su ma akan faɗi irin dabbar
gwargwadon abin da aka saba yi wa tsafin.
[iii] Shi ma wannan
tsafi ana samunsa wajen Hausawa. A ra’ayin Bunza (2006) irin wannan tsafi na
buwaya da magani ne. A dubi lamba ta 1 shafi na 41-51 akwai gamsasshen bayani.
[iv]
Binciken Abdullahi, I.S.S. (2008). Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye a Kan Al’adun
Matakan Rayuwa Maguzawa na Aure da Haihuwa da Mutuwa. Kundin Digiri na Uku.
Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato ya tabbatar da
hakan a babi na uku, da kuma Abdullahi, I.S.S. (2008). Tsafe-Tsafen Maguzawa da
Suka Shafi Aure da Haihuwa. Deparmental Seminar Series, Department of Nigerian
Languages, Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto, shafi na 7-8.
[v] Kundin
digirin Adamu, M. T. (1983). Asalin Tsibbu Yaɗuwarsa da Tasirinsa
ga Al’umar Hausawa. Kundin Digiri na Ɗaya. Sashen Harsunan Nijeriya, Kano:
Jami’ar Bayero ya yi faffaɗan bayani kan haka. Haka ma littafinsa Adamu, M.
T. (1995). Duba da Kanki. Kano: Salma Yaasin Publication
LTD.
[…] Hoton Tsafin Maguzawa A Cikin Littafin K’arshen Alewa K’asa […]
ReplyDelete