Ticker

6/recent/ticker-posts

Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 25: Wasu Sharuɗɗa

Ya zama dole ka san ko kai waye, ka kuma san inda za ka tura kanka, ka tabbatar ka dace da wurin. In ba haka ba...


Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 25: Wasu Sharuɗɗa

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
Idan ka sami kanka a wani kamfani ko masana'anta, ko shagon sayar da kaya, kai ko gidan aure mace ta sami kanta, da sauran wurare waɗanda mutum zai yi aiki a ƙarƙashin wani in dai zai kiyaye wasu sharudda akwai alamun nasara tattare da shi:-

1) Kar mutum ya so kansa sosai, in sana'ar na buƙatar mutane ya ɗauke su, kuma ya yi musu farali da nafila komai nasa zai tafi daidai, za su kare masa amana, kuma su yi aiki tuƙuru don ganin an cimma abin da ake nema.
.
Cin nasara a aure kan samu ne in mace ta iya tattalin gidanta, ta gina tabbatacciyar soyayya tsakaninta da maigidanta yadda ba a jin wani labari sai wanda zai faranta rai, ba ta kanta ko jikinta ba, sai auren ya yi nasara, in ka yi niyyar aikata alkhairi ka sami damar yin ba ya nufin ka ci nasara, sai ikhlasi ya tabbata a aikin, yadda ba ka ba shedan damar kutsawa ba bare ya wargaza maka aiki, in ka nuna wa wani shi ma ya yi sai ka sami ladarka da nasa ka yi babbar nasara kenan, da ka yi rowa tabbas ladarka kai kaɗai za ka tashi da ita.
.
2) Ya zama dole ka san ko kai waye, ka kuma san inda za ka tura kanka, ka tabbatar ka dace da wurin. In ba haka ba kai da kanka za ka ga alamun rashin cin nasara, koda kuwa mutum ne mai son yin magana a kan addini amma bai tsaya ya karance shi sosai ba, zai riƙa samun matsala kuma masu abin ba za su daga masa ƙafa ba, sai a yi ta dauki ba dadi tsakaninsu, ƙarshe gaskiya ta yi halinta, to bare aiki inda gajiyawarka za ta bayyana a sarari, kodai a kore ka ko ka kori kanka, ba yadda mutum zai karanci Larabci a zo neman malaman Turanci ya kai takardunsa, sai in ya shirya jin kunya.
.
3) Dun inda za ka yi aiki ka sani cewa nan ne wurin da arziƙinka yake, anan ne za ka riƙa samun na rufin asari har ka ciyar da iyalinka ka yi zumunci, don haka ya zama maka dole ka bi doka da oda don samun zaman lafiya a tsakaninka da masu wurin, in ka ja aka kore ka shi kenan sai dai ka nemo wani wurin, misali malami ne ya nemi aikin soja, tun wajen gwaji ya fara cewa ba zai sa gajeren wando ba, ba zai tsaya yana kallon al'aurar mace ko ya mannu da ita ba bare ya riƙe hannunta inda hakan ta taso, ba zai yanke gemo ba sabon Allah ne, waɗannan duka gaskiya ne, kuma mutum zai kiyaye duk waɗannan a gidansu, in ya zamanto sojoji ba su yarda da wani ba zai ci duka ne a banza kuma dole ya yi abin da ake so, in ya bari bai ci nasarar abin da ya kawo shi ba.
.
4) Mutum ya riƙa yi wa kansa hisabi, shin ina yin wannan aiki kamar yadda ya dace kuwa ko akwai kuskure? Ya yi ƙoƙarin kallon kansa yadda yake a bara, wasu 'yan canje-canje aka samu zuwa yau? Shin tafiyar tana sauri ko tana ta-ta-ta? Ya kalli abokan aikinsa, suna tafiya tare yadda ya dace ko sun yi masa nisa? In wurin nasa ne ya lura da ribar da yake kintatowa ya samu ko da saura? In harkar ba ta sauri kamar yadda wasu da suka fara take yi musu meye matsalar? Wuri ne ko jari, ma'aikata, albashi, ko yanayi? Ko riba ya samu ya yi ƙoƙarin gano musabbabi don ya lazimce shi.
.
5) Dole ne kowani ma'aikaci ko shugaba a wuri ko mai mahallin gaba daya ya dubi alaƙarsa da kowa don samun ci-gaban wuri, in ka san siyasar wuri sai ka zauna da kowa lafiya kuma ka yi aikinka, mun taba yin wata Islamiyya a cikin arna, da muka kyautata mu'amalarmu da su an tashi yaƙi za a ƙona wurin, maƙwabtanmu su suka ba mu kariya yadda ba a ƙona ta ba, na ga mutumin da uwayen matarsa ba sa ƙaunarsa, amma kuma ba su isa su yi gulmansa a gaban 'yarsu wato matar mutumin ba, kenan ya kyautata zama da ita, hakan ta sa ya yi nasara, ko kamfani kake da shi in ka kyautata mu'amalla da ma'aikatanka su kansu za su ba ka kariya ciki da waje.
.
6) Shiga irin wace ta dace da yanayin sana'ar, shigar da malamammu na addini suke yi, in za a kwatanta ta da wace malaman makarantun boko suke yi akwai bambanci, shigar kowa kan sa aga ƙimarsa a wurin aikinsa, kamar lauyoyi, likitoci, masu kayan sarki, da sauransu, ba yadda bakanike cikin kayan aiki ya kama hanyar sakatariyar ƙaramar hukuma ya ce lallai yana son a girmama shi a matsayin babban baƙo, ba zai ci nasara ba, yanzu ko baburan haya dake yawo a kan titunanmu kana ganin direbobinsu za ka iya ganewa, saboda irin shigar da suke yi, sanya kaya irin wace ta dace da wuri takan sanya a ga ƙimar mutum, koda ba sa ba ka sha'awa daure ka kalli aikin da kake yi ka sanya su dominsa.
.
7) Idan kana son ka ci nasara a rayuwarka dole sai ka yi wa harshenka linzami, kuma ka ƙimanta na gaba, kar ka zama sabon masinja, maganar da ba taka ba kar ka shiga, in manyanka na magana ja bakinka ka tsuke, kar ka yarda a ji magana a wani wurin a ce kai ka kai ta, banda yawan kukan ba ka da kudi ko an ƙi yin albashi da sauransu, ba ka fi kowa matsala ba amma sun yi shiru mai zai sa ba za ka haƙura ba? Wasu da dama sun kasa cin nasara a rayuwarsu saboda azalbabi da shiga rigingimun da ba su zama musu dole ba, na ga matar da maigidanta ya sake ta a dalilin rigingimun da take hada masa kullum, aikinsa kenan ban haƙuri, har dai ya ga za ta kifar da ɗan sauran mutuncin da ta rage masa ya iza ƙeyarta, auren bai yi nasara ba, a kiyayi jayayya da shugaba, yakan yi saurin hana cin nasara a rayuwa.

Post a Comment

0 Comments