Ticker

6/recent/ticker-posts

Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 23: Ɗabi’un Wasu

Kai oga a kamfani ko kanti ko gidan haya ka sani fa cewa wanda yake kawo maka  kuɗin nan ba wani ƙarfin da kake da shi wanda ba shi da shi, amma Allah ya ba ka nasara a hannunka wanda shi bai da ita. Kasancewarta a hannunka...


Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 23: Ɗabi’un Wasu

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
Haka Allah ke yin wasu sai dai ka yi haƙuri da su ba za ka iya canja su ba, amma kai da jinsu ka san akwai matsala, ba za mu ce ba za su ci nasara a rayuwarsu ba, amma tsakani da Allah ba sa jin dadin nasarar koda sun same ta, misali: In mutum ya shiga neman aure zai taras da wasu ko cimmasa, wanda Allah ya ba wa nasara shi zai aura kansu, ƙalu-balen ya rage ga yadda za a zauna da matar, in suka zauna shiru cikin son juna ya yi nasara, in gidan ya koma fagen yaƙin basasa to bai yi nasara a auren ba tun da har lokacin zuciyarta na wani wuri akwai yuwuwar koma masa, kuma kwanciyar hankalin da ake nema ba zai samu ba.
.
Kai oga a kamfani ko kanti ko gidan haya ka sani fa cewa wanda yake kawo maka  kuɗin nan ba wani ƙarfin da kake da shi wanda ba shi da shi, amma Allah ya ba ka nasara a hannunka wanda shi bai da ita. Kasancewarta a hannunka shi ya sa komai ya samu zai ba ka, sai dai ka gutsura ka ba shi, don haka ka lura da hidimar da yake yi maka ka yi haƙuri, na ga wani yaro sai bude wa wani tsoho wuta yake yi, yana ta zage-zage, amma tsohon ya sunkuyar da kai ƙasa ya kasa cewa komai, laifinsa ya yi barci a wurin aiki matar gida ta dawo ta yi ta horn bai sani ba.
.
Sai da suka wuce sannan baba ya fara magana a hankali yana cewa "Sai haƙuri Alhaji, wallah barcinnan bai jima da ɗauke ni ba, ba ma iya runtsawa da daddare saboda gudun sakaci a aiki" a ganina zai iya jawo hankakin baba ba tare da ya bude masa wuta ba, nan gaba ko dai ya kori shi a dalilin bacin rai ko baban ya haƙura, amma saboda sanin dabi'arsa baba ya ja bakinsa, yanzu nasara ake nema har a wurin aiki, musayar yawu ko ban haƙuri zai iya sawa a kore shi.
.
Kar ka taba azawa cewa masu irin wannan bala'in ransu na yi musu dadi ne a lokacin da suke zage-zage, ai ba sa iyawa sai hankali ya tashi rai ya baci, kenan zafin da za ka ji a lokacin da suke wulaƙanta ka su ma fa suna ji, sai dai ƙila nasu yakan ɗan yi saurin sauka kafin su ƙara yi da wani, duk wanda hakan ta zama masa dabi'a ba ka da yadda za ka yi da shi, sanya nasara a gabanka, ka mai da ƙalu-bale baya, ka yi ƙoƙari cimma burinka, ba wani amfani ga yin fada da maigida ko musayar yawu.
.
Shi ma maigidan ya yi ƙoƙari ya duba al'amarinsa, in ya ga ya saki mace daya, ya ƙara sakin wata, ko in maigida ya kori ma'aikaci daya, ya sake iza ƙeyar wani lallai ya gane cewa ko bera na da sata to fa daddawa ma na da wari, da wahala a ce sam shi ba ya laifi sai wani, a kullum shi ne mai gaskiya, akwai mazan da ba su taba rabuwa da matansu ba, kullum cikin soyayya, kamar yadda yadda ake samun ogogin da ba su taba korar kowa ba, ma'aikaci ko masu zaman haya kullum yabonsu suke yi.
.
Wanda ya ga ya mallaki komai amma koda yaushe yana cikin ƙunci sai fada da mutane to ya yi ƙoƙarin yaƙar abin da ke damunsa kar ya hana shi cin nasara, na taba barin gidan haya saboda masifar maigidar, kana gidan haya ne amma ba ka da ikon ka yi baƙi, kuma matarka ba ta isa ta yi hurda da wata matar ba, mutum uku sun bar gidan a gabana, ni ma a dole na haƙura na nade kayana na ƙara gaba, ban jima da barin gidan ba aka ce wasu mutum 3 su ma sun ƙara gaba, cikinsu har da wanda ya zauna a dakina, watansa biyu kacal, mai gida na ta fuskantar matsaloli a lamuran sana'arta ta kasa gyarawa.
.
                 KAI MA ZA KA IYA
Me ke kawo mutuwar zuciya? Ko na ce shekararka nawa kana karen mota, 10? Me ya hana ka zama direba? A shekarun da ka bata dinnan ka mallaki motar kanka kuwa? Amsar dai karen mota ne har yanzu, kuma bai ma gwanance a tuƙin ba, bai kuma roƙi wani ya koya masa ba, kenan bai yi tunanin zai iya zama direban ba, ya yanke ƙauna da cin nasara a rayuwa, in ba haka ba, akwai makarantun koyon tuƙi mai zai hana ya shiga wata makaranta? Ko yana jira ne ogansa ya koya masa, to in kuma ogan ya fi jin dadin aiki tare da shi zai yi wahala ya so rabuwarsu, ya gwammace ya yi ta ƙara masa kudi don ya riƙe shi.
.
Ni gaskiya na fi ganin laifin direban saboda rashin motsawa, in kana haya ne  ai kana son ci-gaba me kake yi ba ka hau kan hanya ba? In haya kake yi me ka yi don ganin ka mallaki gidanka na kanka, wata ƙila ma ka gina wasu ka zuba masu hayan? Akan sami masu karbar mota a wurin direba su farauto masa fasinjoji su kawo masa, shi mai nemo fasinjojin mai ya hana shi samun motar da zai riƙa daukar fasinjojin da kansa? Meye bai sani ba? Masu ba da motocin a yi musu haya ko tuƙin, ko garuruwan da za a riƙa kai fasinjoji? Jiya ake gaya min wani shahararren likitan fida a Kano wanda aikinsa na farko shi ne miƙa wa likita kayan fidar, amma yanzu ya zama babba.
.
A daidai wannan lokacin na tuna wani babban hakimi wanda na san shi lokacin da yake masinja, yanzu ga shi ya zama babba, duk wani da ka sani ya ci nasara a rayuwarsa akwai hanyoyin da ya bi, akwai wanda ya ce min yana sha'awar siyar da filaye ne, na ce ba zai iya ba, ya ce don me? Na ce ko masu sana'ar bai sani ba bare ya san ta inda zai bullo mata, nan take ya lissafo min kusan mutum biyar, na ce ka taba zama ko hira da ɗayansu? Ya ce a'a, na ce wurina za ka zo kana hirar bayan kana sane da cewa banda wata masaniya da mai sana'ar ma bare na ba ka shawarar da za ta taimake ka? Abin da zan iya kenan na karya maka gwiwa kuma na kusa yi din.

Post a Comment

0 Comments