Ticker

6/recent/ticker-posts

Hanyoyin Cin Nasara 13: Karkasuwar Buri


Babban abin da ya dace a rayuwa shi ne farawa da buri mafi kusa da mutum, wanda za a iya kaiwa ga nasara ba tare da an ɓata lokaci ba, kuma za a sami...


Hanyoyin Cin Nasara 13: Karkasuwar Buri

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Ba wani dan adam da ka sani wanda bai da burin da yake so ya cimmasa a rayuwa, sai dai kamar yadda muka fada ne, wani ya san abin da yake nema, wani yana zaune ne kawai bai san abin da yake buƙata ba, wani ya san komai amma hanyar da za ta kai shi zuwa ga burin ne bai sani ba, wani ya san hanyar kuma yana kanta, amma matsalar ya kasa tsayar da abu guda da yake burin isa gare shi, ga komai a zagaye da shi amma bai san wanda zai fuskanta ba, ƙarshe sai ya zo dab da wannan ya bar shi ya koma wancan, a ƙarshe ya gaji da wahala ya koma hannu-rabbana.
.
Da za ka kasa burinka zuwa gida biyu da zai fi ba da ma'ana, wato a sami burin da yake dab da kai, wanda ba zai buƙaci aiki mai baƙar hawala ba, ba zai dauka maka lokaci ba, ba zai buƙaci kuɗi masu yawa ba, misali kana son ka zama babban Injiniya, wanna buri ne da yake nesa da kai, matuƙar baka ma shiga jami'a ba, magana ce da za ta dauki tsawon lokaci, ta buƙaci kuɗi, da juriyar karatun, wanda yake son ya gida katafaren masana'antar lemon kwalba, kuma a yanzu dan shago ne gare shi bai da cikakken jari wannan buri ne mai tsawo wanda zai iya dauke rabin rayuwarsa kafin ya sami biyan buƙata, akwai maganar tara kuɗi, sayen fegi da na'urorin aiki.
.
Babban abin da ya dace a rayuwa shi ne farawa da buri mafi kusa da mutum, wanda za a iya kaiwa ga nasara ba tare da an ɓata lokaci ba, kuma za a sami kuɗin da ake son a yi amfani da su ba tare da jiki ya jigata ba, akwai matakai har 3 da suka zama dole ga mai son cin nasara ya taka su kafin ya kai ga nau'in nasarar da yake buƙata:-

1) Tabbatar da abu guda wanda kake son ka cin masa, da yawammu muna ganin kamar baiwa ce mutum ya sami mabambantan sana'o'i, ko kwalayen digiri na farko da dama, ba mu san cewa hakan kan hana mu mu natsu a wuri guda ba, ita kuma nasarannan hanyoyi ne da dama take da shi amma ita kadai ce, in ka ce duk hanyoyinnan sai ka bi su kafin ka isa gareta babu kokwanto za ka kai a makare.
.
Domin ka kama wannan hanyar ka yi nisa ka bar ta ka dauki wata, ka faro daga farko ita ma ka bar ta ka dauki wata, kafin ka kai ka bar ta ka sake dauko wata, wanda ya dauki hanya daya tal tuni ya manta cewa ya biyo hanyar, ka yi ƙoƙari ka sami buri guda a zuciyarka ka saka shi a gaba, in ka cimmasa ka sake ƙulla wani shi ma ka yi ƙoƙarin isa gare shi, ba za ka bar shi ba sai ka tabbatar da ka isa gare shi sannan ka dauko wani, in ba haka ba tara abubuwa da yawa kan kawo tarnaƙi a lokacin da mutum yake ƙoƙarin cin nasara a cikin al'amarinsa, sai dai zai yi kyau mu fahimta, ba cewa muka yi kuskure ne ba ka ci nasara a cikin al'amuranka, amma cewa muke ka zabi abu guda tukun, in ka same shi ka sake dauko wani.
.
Wallahi na yi zamani da wani mutum wanda ya bar karatu tun yana furamare a dalilin bai gane komai, haka yake dudum ba Arabi ba boko, duk wani rubutu in ka cire sunansa da ya ci duka a makaranta a dalilinsa ba abin da ya iya, sai dai kuma maƙeri ne na wuƙaƙe kai har da bindiga mai aiki da harsashin soja, masucin kifi ne kuma ya iya farautar makware, tela ne shi, ban san lokacin da ya koyo gini ba, yana aikin gyaran kayan wuta ko sanya wa mutum wuta a daki, kafinta ne shi na sama da ƙasa, yakan dauki mashin ya zagaya express a wancan lokacin, yanzu ma mota yake hawa, yana da ƙwaƙwalwa ta ban mamaki a duk sana'ar da yake son yi, bokon ne babu, sai dai matsalar ban san wata sana'a ƙwara daya da ya shahara a kai ba wace zan ce ya yi fice kuma zai iya zama wani abu nan gaba a dalilinta, ma'ana wace ya bunƙasa ta a dalilin ƙwaƙwalwar da Allah ya ba shi, har kuma mutane za su amfana da shi, matsalar kai komon ke nan.
.
2) Tsarin isa ga burin, matuƙar ka sami burin da kake son ka cin masa sai ka natsu ka tsara hanyoyin da za bi don ganin lallai ka isa gare shi, rashin tsari shi ne babban matsalar da mafi yawan mutane suke fama da shi, na ga wani da yake son ya yi shago a kusa da makaranta, abin takaici da wahala ka ga dalibi ko malami ya zo shagon ya sami abin da yake buƙata, lokacin da muka ba shi shawarar ya fara kawo abin da muke buƙata mana, sai ya ce shi ya taba irin wannan sana'ar ba ta ba shi ribar da yake buƙata ba, na ce a zuciyata to ai abin da kake so ka sayar yanzu mu kuma ba mu da buƙatarsa, ke nan ananan dai yau kamar jiya, shi yana son ya sayar da abin da mutanen wurin ba su buƙata ne, ka ga batsari anan.
.
Komai kyawun abin da kake so ka yi in babu lafiyayyen tsari aikin banza ne, kodai a gaza yi, ko a yi din ya ƙi ƙarko, in dai kana so ka ci nasara ka nemo tsarin da farko a ƙwaƙwalwarka, in ma zai yuwu ka rubuta ko ka zana a takarda maganin mantuwa, a hankali lamarin zai fadada, ka ga sai ka janyo wasu kusa yadda ko ba kanan harkar za ta ci gaba ba za ta tsaya cak ba, za a yi tsarin ne daki-daki daga wannan sai wancan, ana bin matakan sau da ƙafa, in ma mutum bai yi boko ba ba zai rasa wanda za su yi tsarin tare ba, yadda in ya manta wani abin za a tuna masa, wannan shi ne matakin tsakiya.
.
3) Sai kuma matakin ƙarshe wato zartarwa, inda mutum zai fara bin tsarinnan amma a aikace, ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wurin ganin cewa yana bin tsarin ne kamar yadda ya dauko tun farko, ba tare da gaggawa ba, za mu yi maganar gaggawar nan gaba in sha Allah, wato kamar mai koyon aiki ya fara tunanin cewa yana shan wahala ba a ba shi komai, sai ya tara kuɗi ogansa ya kwashe duka, irin wannan kalle-kallen gaggawa ne, in mutum bai sa'a ba sai ya bar wurin kafin ya iya, saboda tunanin cewa ana cutarsa, na sha ganin  waɗanda suke fara aiki su bari saboda raina albashin da ake ba su, ba su da wani tunani na cewa nan gaba za su iya zama wani abu ta wannan hanyar kuma za su sami duk abin da suke so.

Post a Comment

0 Comments