Ticker

6/recent/ticker-posts

Hanyoyin Cin Nasara 14: Gamuwar Ilimi da Buri


Yanzu dai komai iliminka da ƙwaƙwalwarka kana buƙatar zama kusa da masu ilimi  waɗanda za su taimake ka kan lamura. Wannan ya sa za ka ga wani kamfani babba wanda bai da alaƙa da shari'a amma yana da mai ba da shawara ta fuskar doka da oda. Wannan aikinsa ke nan nuna wa kamfanin fuskar da zai bi don guje wa aukawa cikin wata...


Hanyoyin Cin Nasara 14: Gamuwar Ilimi da Buri

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Abin da mafi yawan mutane suka sani game da ilimi ko jahilci shi ne: Mai ilimi mutum ne da ya bi tsarin karatun boko a rubuce sannan ya dan hada da turancinnan, in aka sami mutum bai bi wannan tsarin ba to jahili ne, bambancimmu da ƙasa mai tsarki ke nan, a 'yan shekarun baya an yi wasu shahararrun malaman muslunci, sun koyar da daliban jami'un ƙasar alhali ba su taba wuce makarantun sakandare ba, tunda har  waɗanda suka bi tsarin karatun daga Furamare har gaba da digiri suna daukar karatu a wurinsu, dole sai an yi wa ma'anar jahilcin gadon bawul.
.
Iya rubutu da karatu, ko bin tsarin boko ba shi ne kadai ilimi ba, a neme ka a kan abu kuma a same ka da shi shi ne manufa, duk ilimin da mutum yake da shi na kasuwanci, in zai koyar da duniyannan gaba dayanta amma ya kasa aiki da ilimin wurin zama babban dan kasuwa haƙiƙa babu alamar sifantuwa da ilimin, komai daƙiƙancin mutum ko rashin shiga makarantar boko in ya san yadda zai juya kuɗi, ya yi babban shago maƙare da kaya ya sami ma'aikata, wannan ya fi ƙarfin jahili.
.
Duk mutumin da zai shata gona, ya dibi ma'aikata ya yi lissafin kuɗin taki da na ma'aikata ya yi bankadediyar gona, in amfani ya zo gidansa ya gyara ya sayar ya ci riba ya sake shiri don gobe wannan ya fi ƙarfin a kira shi jahili, ilimi da buri a hade suke ba sa rabuwa, da yawan  waɗanda suke karanta ilimin injiniyanci don su zama injiniyoyi ne, haka ma wanda yake koyon kanikanci duk ƙoƙarinsa a ce yau ya zama bakanike, ma'ana dukansu dalibai ne, wanda ya iya isa inda yake so ya ci nasara ke nan a rayuwarsa, a taƙaice dai babu jahili kamar wanda yake ganin ya yi ilimin amma bai san yadda zai yi aiki da shi ba.
.
Yanzu dai komai iliminka da ƙwaƙwalwarka kana buƙatar zama kusa da masu ilimi  waɗanda za su taimake ka kan lamura. Wannan ya sa za ka ga wani kamfani babba wanda bai da alaƙa da shari'a amma yana da mai ba da shawara ta fuskar doka da oda. Wannan aikinsa ke nan nuna wa kamfanin fuskar da zai bi don guje wa aukawa cikin wata matsala. Idan wanda bai yi karatu ba yana da masu fuskantar da shi sai ya yi abin mamakin da wani mutumin da ya yi nisa a bokon bai yi ba, kawai abin da kowani irin mutum yake buƙata, daga kowani irin rukuni yake kuwa, shi ne: Me yake buri, yazai isa gare shi?
.
 FUSKANTAR MATSALOLI
Akwai wasu matsaloli a rayuwarmu  waɗanda duk yadda muka yi ba za mu iya kauce musu ba, wani sa'in ba ilimi ne kafai magani ba anan, abin kan faru ba mu san da shi ba shi, tabbas wasummu suna fama da matsaloli masu baƙanta rai, masu radadi a zuciya, ka ga mutum koyaushe cikin damuwa da ƙunci ka rasa me yake damunsa, wani ma takan kai ga hakan ya yi tasiri a cikin al'amuransa yadda dan abu kadan sai ka ga ya dauke shi sama da yadda ake buƙata, yana da kyau mu fahimci cewa wannan cuta ne dake buƙatar magani.
.
Koda yake hakan kan faru ne daga wani abu da aka yi wa mutum, in ya zamo bai yin shawara da kowa sai abin ya yi ta cinsa a rai har ya kai ga wannan halin, wani kuwa tsabar zato ne cewa in har wannan abin ya tabbata to shi fa ya shiga uku, daganan ya sa abin a zuciya har ta kai shi ga aika-aika a kan sana'arsa ko lamarin rayuwarsa, a ƙarshe da wahala nasarar ta samu masa kamar yadda yake zato, ka dubi mata dai yadda suke daukar kishi da kishiya, sam ba sa zaton alkhairi ga kishiyar, sai su fara wasu ayuyyukai da maganganu, hakan ta kai ga amaryar daganan ita ma ta fara shirin yadda za ta fuskanci uwargidanta.
.
In ta shigo ba za ta gasgata fara'a da haba-habar da za ta gani ba sai ta dan sami lokaci ta tabbatar gaskiya ne ba shigo-shigo ba ne, dan lokacin da za ta dauka kafin ta saki jiki in ba a kai hankali nesa ba sai ka ga uwargidan ta yanke ƙauna, ta ce ta yi kaza da kaza amma ga abin da amaryar take yi mata, in shaidanun mutane ko ragon namiji ya shiga tsakiya shike nan lamarin ya gama ragargajewa gaba da daya, babban abin da ya jawo hakan tsoro da hukunci kan abin da baka tabbatar ba.
.
Zai yuwu a sami hakan in kana da shagon sayar da takalma ka ji wani shi ma zai yi a kusa da kai, sai ka yi tsammanin cewa kai kuma taka ta ƙare ke nan za a koma wurinsa, daga lokacin ka rasa kasuwa ke nan, ko kana da burin gina gidan buredi sai aka ce akwai kusan gidaje guda uku, ba ka duba yawan maciyan ba da yawan buƙatunsa sai ka duba gidajen buredin kawai, wannan 'yar matsalar da samu in ba a yi sa'a ba shike nan komai ya tsaya ƙila ma daga lokacin ba wani abin da za ka yi tunanin yi an riga an gula maka kissafi, bayan ga lissafe-lissafennan barkatai.

Post a Comment

0 Comments