Idan za a tura yaro wurin sana'a shi ma karatu zai yi, sai dai wannan ya fi karkata ne ga aiki, wato karatu ne amma a aikace. Zai san kayan aikin gaba ɗaya da yadda ake sarrafa su...


Hanyoyin Cin Nasara 11: Karatu

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
Duk wani mai son cin nasara a rayuwa dole ne ya yi karatu, kodai ya yi na takarda da biro ko kuma ya yi na rayuwa, wanda duk ka ji ya ce "Ba dole sai mutum ya yi karatun boko zai zama wani abu ba" maganarsa haka take, amma wani karatu ne ya zarce zaman duniya? Ai ita duniya gaba dayanta makaranta ce, jami'a ce da take da sassa daban-daban, duk sashin da mutum yake son ya shiga zai samu, da za ka dauki mutane guda biyu; wani ya bi layin boko, wato furamare har zuwa jami'a a ƙarshe ya sami abin kansa, za ka taras wani ya fara da ƙaramar sana'a ne, ya bari ya koma wata, ko kuma ya ƙawata ta, za ka ji ya sha wahala iri kaza kafin ya isa wuri kaza, duk  waɗannan da kake gani karatu ne bambancin hanya ne kawai.
.
Mu a zamanance muna daukar wanda ake ganin kamar ya dan fi sauƙi ne, wato shiga a ji, shi din ma ana ƙoƙarin goge ƙwaƙwalwar yaro ne tun yaranta yadda zai iya hararo abubuwan da za su amfane shi a rayuwa, babban dalilin da ya sa aka ƙirƙiro darussan dake buƙatar tunani ke nan a azuzuwan yara ƙanana, akan koyar da yaro a ba shi aiki don ya wasa ƙwaƙwalwarsa wajen nemo irin amsar da ake buƙata a rayuwa.
.
Idan za a tura yaro wurin sana'a shi ma karatu zai yi, sai dai wannan ya fi karkata ne ga aiki, wato karatu ne amma a aikace. Zai san kayan aikin gaba ɗaya da yadda ake sarrafa su. Muna da injiniyoyi irin su kanikawa, kafintoci, maƙera da magina,  waɗannan manya-manyan Injiniyoyi ne amma ba su san haka ba, sabanin  waɗanda suka je makaranta, sau da yawa za ka taras  waɗanda suka yi karatun boko ba su kai  waɗanda suka yi a aikace ba, amma da ka ce Injiniya sun san da su kake yi ba wadancan ba, sun yarda da kansu sosai koda kuwa ba abin a ƙasa, sai su fara bin hanyoyin da za su cimma burinsu, cikin ikon Allah sai ka ga sun sami biyan buƙata a dan ƙaramin lokaci.
.
 waɗanda suka faro ta sana'a sukan dauka cewa na abinci kawai suke nema, wato abin da za su ci da iyali, duk kuwa da cewa bakanike karar abin hawanka kawai zai ji ya ce maka kaza ya lalace, in ya hau ya ce maka sai ka canza kaza, in ya bude ya ce maka ba za ka jima ba za ka canza kaza, wannan in ba karatu ba meye? Sai dai babu tsari ne na mataki, babu wata takarda da ake la'akari da ita wace za ta ba da shedar cewa tabbas mutum ya ƙetare mataki na kaza don haka ya zama cikakken Injiniya, sai ya dauki kansa a kan cewa shi ba injiniyan ba ne, ko ka ce injiniya in ba an saba kiransa ne ba ba zai waiga ba, da wahala ka ga ya fadada tunaninsa a kan fannin da yake ciki har ya fara saka wa a ransa zai iya ƙera jirgin sama.
.
Galibin  waɗanda suka fara sana'a a aikace sun ta'allaƙa ne da motsa jikinsu wajen koyon abin da za su riƙe rayuwarsu da iyalinsu kawai, akwai ƙarancin tunani wurin hararo sabbin abubuwa  waɗanda za su bunƙasa sana'ar, ko ƙirƙiro wasu sabbin na'urori da kansu  waɗanda za su sauƙaƙe musu ita, shi ya sa nake ganin wanda ya kama sana'a kuma ya shiga makarantar ya fi kowa sanin kanta, kamar yaron da ya girma a cikin bariki ne daga bisani ya shiga soja.
.
Yanzu kai da ka fara kasuwanci a gaban babanka ko kantinsa dole ka san irin kayan da mutane suka fi so, ka san nau'in da suke buƙata, da lokutan da suka fi zuwa sayayya, a daya hannun dole ka iya lissafi irin na rayuwa, wato ka riƙa gamsar da su ta wurin cinikayyarsu, misali mata masu ciniki, kayan da ake sayarwa a Naira 15 sai ka bar shi 13.5 dan abin da ka rage 1.5 ne kawai, akan dan wannan ragin mace za ta iya takawa daga wuri mai nisa ta zo wurinka, to bare ƙaramin yaron da aka aika, sai ka sayar da guda 10 wanda ya ƙi rage nasa bai sayar da 4 ba, in ka duba sai ka ga ka mai da kuɗinka har ka sami ribar da shi bai samu ba.
.
Kawo irin kayan da mutane ke buƙata kowa na yi, amma lissafin sauƙaƙe kaya don jawo mutane da yawa wani abu ne da yake buƙatar lissafi bayan dogon tunani, galibi  waɗanda suka hau sana'a a sama ba su cika irin wannan lissafin ba, in aka yi rashin da ce da mai sayar da kayan gwari sai ka ga ya rube an zubar, a maimakon a sauke kuɗin ya ƙare a sake kawo wani ya ƙare a dauko wani nan da nan, ta kowani bangare ka bi karatu na ba da gudummuwa gwaggwaba wajen cin nasara a rayuwa.
.
Ba ƙoƙari muke mu ce wanda bai yi karatu ba ba ya cin nasara, manufar ita ce in aka hada bangarorin guda biyu an fi samun sauƙi wajen isa ga buƙatun mutum na cin nasara a rayuwa, nakan ga uwaye da dama sukan sa yaransu a makaranta, kuma suna tilasta su tsayuwa a wuraren aikin hannu don su sami sana'a, wani zai gaya maka cewa tun yana sakandare shi ya dauki nauyin karatunsa, na ga wani dan bumburutu kwanannan da yake gaya min cewa yana karatu ne a jami'a, yana karanta Biochemistry, yanzu yana tara kuɗin makaranta ne, irin wannan da wahala ka ga ya sadaukar da karatunsa a banza, ya fi kowa sanin irin wahalar da ya sha.