Ticker

6/recent/ticker-posts

Siddabaru Adon Damfara: Nazarin Damfara Jiya Da Yau


Wannan bincike yana magana ne a kan yadda ake amfani da siddabaru wajen gudanar damfara wanda ya shafi kowane ɓangare na al’umma. Binciken ya fito da hanyoyin da ake amfani da su na damfara na gargajiya, wanda ya ƙunshi amfani da siddabaru wajen gudanar tafiyar da hankalin mutane, kuma wannan damfara ya taƙaita ƙwarai da gaske a kan waɗanda ake damfara da kuma abin da ake samu wajen damfarar. Sannan binciken ya fito da dabarun damfara na zamani wanda suka haɗa da amfani da Intanent da kuma wayar hannu da sauran hanyoyi wajen gudanar da damfara. Sannan kuma an fito da dabaru na zamani wajen gudanar da damfara. Wanda ya ƙusnhi hanyoyi daban-daban da kuma amfani da na’urori na zamani wajen aiwatar da damfara. Duk da cewa wasu mutane jahilci ne ya haifar da aka damfare, wasu kuma kwaɗayi ya haifar da haka. Kuma wannan damfarar ruwan dare ne game duniya, domin babu lungun da ba a yin wannan damfarar kuma babu wasu rukuni na jama’a da suka kuɓuta daga faɗawa daga cikin wannan damfarar. Domin kai na wayewa su kuma `yan damfara suna ƙara fito da hanyoyi na gudanar da damfara. Binciken ya fito da dalilan da suke haifar da damfara da kuma illolin damfara ga tattalin arzikin ƙasa da kuma ɗaiɗaikun jama’a.


Siddabaru Adon Damfara: Nazarin Damfara Jiya Da Yau

Hassan Salihu

1.0 Gabatarwa
Siddabaru da damfara ɗanjumma ne da ɗanjummai domin kuwa damfara ba ta yi yuwa a wasu lokuta sai an haɗa da siddabaru, domin ta hanyar  siddabaru ne ake tafiyar da hankali da tunanin wanda za a damfara ya amince da abin da za a gabatar masa, domin a karɓi kuɗi ko wata ƙaddara daga hannunsa. Damfara a cikin al’ummar Hausawa daɗaɗɗiyar sana’a ce wadda wasu mutane suka riƙa domin samun kuɗaɗen biyan buƙatunsu na yau da kullum. A da, akwai dabaru da `yan damfara na wancan lokaci ke amfani da su waɗanda suka yi daidai da zamaninsu. Yanzu kuwa damfara ta ɗauki sabon salo, saboda sabbin hanyoyi da aka ɓullo da su na zamani ta hanyar amfani da abubuwan da zamani ya samar domin gudanar da wannan sana’ar ta damfara. Don haka wannan takarda za ta yi tsokaci ne a kan damfara jiya da yau. Ma’ana takardar za ta dubi hanyoyi ko dabarun damfara na gargajiya da kuma na zamani waɗanda ake amfani da su wajen karɓar kuɗaɗe a hannun mutane. Domin yana da matuƙar wahala mutum ya yi farat ɗaya ya gane dabarun damfara na zamani, saboda amfani da fasahar zamani yin damfara, kamar amfani da wayar salula da kuma hanyar Intanet. Wannan damfara tana faruwa ne saboda ƙwaɗayi da son tara abin duniya cikin sauri ko kuma rashin sani. Don haka wannan bincike zai bi hanyoyin da suka dace domin tattaro bayanai kan abubuwan da `yan damfara suke amfani da su wajen yawo da hankalin mutane, don su faɗa tarkon su. Dabarun da `yan damfara suke amfani da su a wannan zamani masu sarƙaƙiya ne, waɗanda tilas sai an kwantar da hankali za a iya fahimtar su. Domin sukan laɓe ga bagaruwa su harbi karsana, wato sukan yi amfani da wani tsari ko shiri wanda hukuma ta ɓullo da shi domin aiwatar da wasu dokoki misali, BƁN da sauransu, su damfari jama’a ta hanyar saka tsoro a cikin zukatansu. Musamman a kan abin da ya shafi harkar kuɗi a bankuna. Mutane da dama sun faɗa wannan tarko a lokacin da aka fito da wannan shiri na BƁN inda za a yi amfani da wannan damar a kwashe kuɗin ajiyar da ke cikin asusun bankin mutum ba tare da saninsa ba.
1.1 Dabarun Bincike
Duk wani abin da ɗan Adam zai gudanar a rayuwarsa, to yana buƙatar a ɗora shi bisa wani mizani da zai dace da tafarki madaidaici domin cimma nasara. Nasarar kowani irin bincike ta dogara ne ga irin hanyoyin da aka bi wajen tattara bayanan da za su samar da abin da ake buƙata. Don haka an ɗora wannan bincike a kan waɗannan hanyoyi:
1.      Hanya ta farko da za a fara bi wajen gudanar da wannan bincike ita ce, nazartar wasu littattafai da aka wallafa waɗanda suka danganci dabarun damfara jiya da yau. Waɗannan littattafai ba lallai ne su yi magana kan dabarun damfara kai tsaye ba, salon da suka yi amfani da shi a wurin fito da waɗannan hanyoyi da za a iya cin karo da su, za su taimaka wa binciken.
2.      Binciken ya yi amfani da kundaye na digiri na farko da na biyu da kuma na uku, domin tsamani cin karo da waɗanda suka tsakuro wani abu daga cikin irin dabarun da `yan danfara ke amfani da su don wajen damfara na gargajiya da na zamani. Haka kuma, binciken ya waiwayi mujallu daban-daban har da waɗanda aka saka a yanar gizo. Hakan ya taimaka wa wannan bincike don cimma nasara.
3.      Binciken ba zai yi tuya ya manta da albasa ba, ya zama wajibi a tuntuɓi masu ruwa da tsaki masana da suke da masaniya a kan irin waɗannan hanyoyi na damfara na gargajiya da na zamani da kuma waɗanda suka faɗa tarkon mayaudara musamman na zamani.
1.2 Ra’in Bincike
Kasancewar ɗabi’ar son banza da cima zaune sun yi katutu a zukatan wasu Hausawa, wannan ya yi sanadiyyar samar da sana’ar damfara a cikin al’umma. Don haka an a za wannan bincike ne a kan ra’in Kwaɗayi mabuɗin wahala da wannan ra’in za a gudanar da wannan bincike, domin fito da wannan ra’i a fili a cikin wannan bincike. Saboda in babu kwaɗayi babu yadda za a yi a yi damfara.
1.3 Farfajiyar Wannnan Bincike
Wannan bincike an iyakance shi ne a kan, “Nazarin damfara jiya da yau”. Mai bincike ya tsayar da akalan wannan bincike a kan jiya da yau wato na gargajiya da na zamani saboda rashin wadatar kuɗi da kuma isasshen lokaci. Wannan ya yi wa mai bincike takunkumin fita daga muhallin binciken saboda rashin wadataccen kuɗi da ake buƙata wajen yin zirga-zirgan farautar neman sahihan bayanai. Domin abu ne mawuyaci ɗan damfara ya bayyana hanyoyi da yake amfani da su wajen gudanar da wannan sana’ar. Sannan kuma wanda aka damfara ba ya son bayanawa saboda gudun kada a raina masa wayo da hankali a cikin jama’a.
Kafin a zunduma cikin bayani za  a fayyace abin da ake nufi da siddabaru da damfara sannan kuma a nuna alaƙar da ke tsakaninsu domin a cire wa idon kwantsa.
2.0 Ma’anar Siddabaru
A hasashen Bunza, (1989) Siddabaru ba hastin bara ba ce, watao kalma ce ta Hausa tsintsa don haka ne ma masanin ya bayyana ta da waɗannan abubuwa:
                    i.            Cukurkuɗa abubuwa ko kuma rikita su tare da ɓatar da bakin zare. Idan mutum ya cika sassarƙe bayani, ana cewa ya cika siddabaru a zancensa.
                  ii.            Wayo da dabara wajen kare kai, ko kuɓutar da kai daga wani abu. Da za a koro ɓarawo ya shiga nan ya fita can, har ya dubultar da masu nemansa, a ce, ya yi masu siddabaru.
                iii.            Hikima da basira ta fuskar ƙagen wasu abubuwa. Domin kuwa yau saboda ci gaban wannan ƙarni, da an ga jirgin sama ko rediyo ko salula (wayar hannu) ko mota a kan ce siddabarun Bature ne.
A ra’ayin Adamu, (2014:38-39) siddabaru shi ne, sanin yadda za a yi wasa da hankalin mutum har ya yi mamakin yadda abubuwa ko ayyuka suka faru.
A taƙaice dai ssiddabaru yana nufin zunzurutun wayo da ɓatar da hankalin mutane a kan wani abu ko a shagaltar da mutane a aiwatar da wani abu wanda bai san yadda aka yi shi ba.
2.1.1 Ma’anar Damfara
Damfara kalma ce Bahaushiya ba hatsin bara ce, ma’ana kalma ce ta Hausawa ba aron ta suka yi daga wasu baƙin al’ummu ba. Masana da manazarta al’ada sun tofa albarkacin bakin su a kan ma’anar damfara, daga cikin akwai:
Maiyama, (2001:27) ya bayyana damfara da cewa:
“Hanya ce da wani ƙwararre ke bi ya mallaki abin mutum ta hanyar amfani da daɗi lafazi da nuna kwaɗayi zuwa ga wanda za a zalunta don ya yarda ya saki jiki har ya amince don ƙwaɗayin abin da aka yi masa nuni da shi”.

Shi kuwa Bunza, (1994:2) cewa ya yi:
“Amfani da dabara ta fuskar nuna wayo da yaudara a kaikaice domin a karɓi dukiyar mutum. Damfara ta keɓanta ga kuɗi tsabarsu ko wasu ƙaddarorin da ake iya kaɗarwa nan take a sami tsabar kuɗi. Da yawa takan samo asali ne daga kawo kuɗi in yi maka kuɗi ko alƙawarin samun kuɗin cikin sauƙaƙƙar hanya”.

Shi kuwa Doma, (2018) ya bayyana damfara da cewa:
“Damfara hanya ce ta cuta wanda ake amfani da ita wajen karɓar kuɗin mai son banza, ta hanyar kwaɗaitar da mutum a kan abin da ya ke so”.
Shi kuwa Ƙamusun Hausa (2006:92) ya bayyana damfara da yaudara ko zamba da ake yi wa wani mutum da yake zaton zai sami wata ƙaruwa. A yayin da Adamu, (2014:118-119) ya kalli damfara a matsayin wata hanya da mutum zai shirya ta wayo da ƙarya domin ya karɓi abin hannun jama’a.
A fahimtar wannan bincike, damfara hanya ce ta karɓar kuɗi a hannun mutane ta amfani da siddabaru da ƙwaɗaitar da mutum bisa samun abin duniya cikin sauƙi. Waɗannan hanyoyi sun haɗa da dabarun gargajiya da na zamani.
2.1.2 Dangatakar Siddabaru Da Damfara
Dangantakar da ke tsakanin siddabaru da damfara ta jini da tsoka ce. Domin kuwa damfara ba ta gudana sai an haɗa da siddabaru, don ta hanyar siddabaru ne ake jawo hankali mutane har a damfare su. Wannan ya yi daidai da bayanin da Bunza, (1989) ya kawo a kan yadda ake amfani da siddabaru wajen yin damfara. Misali siddabarun rubutu cikin ruwa, wanda malaman tsibbu ke yi wajen damfarar masu neman maganin zana da baduhu. Yadda suke yi shi ne za su sami wata farar takarda su saka a cikin wani kasko da wani kasko kamar sa sai su dinga rubuta wasu ayoyi a kaskon da aka rufe da farar takarda a ciki, a cikin ruwa. Idan an buɗe sai ka ga takardar da ke cikin ruwa da rubutun da aka yi a kan kasko ya fito a cikinta, cikin ruwa ɓaro-ɓaro, kuma har ka ɗauko takardar ka karanta.
Wannan siddabarun shi zai taimaka a yi damfara domin in ba a gwada wa mutum abin da hankalinsa ya kasa ganewa ba, ba zai aminta ya ba da kuɗi ba. Saboda haka, duk inda za a yi damfara to sai an fara yin siddabaru don ita ce adon damfara. Wannan ya tabbatar da maganar Adamu, (2014) inda yak e cewa hanyoyi nuna wayo da dabaru waɗanda sukan kauce hanulan mutane su ne suke ɗaukar siffa ta siddabaru a sha’ani na damfara a ƙasar Hausa.
2.1.3 `Yan Damfara
`Yan damfara kamar yadda Bunza, (1989:269) ya bayyana cewa su ne mutane masu yawo wuri-wuri ba su sayar da wani magani illa yawon damfara a birane da ƙauyuka. Sukan yi wa mutum kuɗin yabu ko su yi dabon kuɗi nan take, ko su ce za su yi wa mutum dukiya. Wasu kan shirya mota ta kara su sihirce ta su sayar wa mutum, sai ya shiga sai ya ga kara. Wasu kan tafi da mutum Makka da dai sauransu.
Wannan bayani ya yi daidai da wasu daga cikin siffofin `yan damfara domin har kamfanin ƙarya suke shiryawa su nuna wa mutum takarda na rigistar kamfani daga bisa su umurce shi da ya saka hannun jari, sannan su nuna masa irin riba mai tsoka da zai sami cikin ƙanƙanen lokaci.[1] Da zarar hakan ta faru, shi ke nan sun washe mutum domin bayan kwana biyu idan mutum ya dawo zai tarar da babu wannan kamfani kuma takardun ƙarya suka ba shi. Haka kuma a wannan zamani akwai `yan damfara masu zaunawa su yi amfani da Inatent da wayar hannu wajen aika saƙo ga mutane wanda ya shafi harkokinsu na kuɗi a banki ko shafukan sada zumunta ko Imel da sauransau
 To, a duk lokaci da za a yi damfara tilas ne sai an samu `yan kore domin su ne kanwa uwar gami. To wane ne ɗan kore?  Mene ne matsayinsa a wajen gudanar da damfara.
2.1.3 Ɗan Kore A Wajen Damfara
Ɗan kore shi ne kanwa uwar gami a wajen aiwatar da damfara. Domin duk wani abu da ya gudana ɗan kore ya shirya shi ya kuma aiwatar ta yadda hankalin mutane ba zai gano abin da ake nufi ba. Don haka Bunza, (1989) ya bayyana ɗan kore da cewa shi ne mai koro wa ɗan damfara mutane ana karɓar dukiyarsu. A hasashensa an samo wannan suna ne daga mai kiro jama’a. Wato ɗan kore yakan kasance namiji ko mace, babba ko yaro, ɗan gida ko baƙo wanda zai dinga taimaka wa ɗan damfara a kaikaice ba da sanin mutane ne ba. Kusan duk abin da ke bayan fage da sanin ɗan kore kuma duk wata damfara da za a yi a bayan fage ko abu ya faɗo daga sama ko a ji ƙarar shi da dai sauran su duk da hannun ɗan kore. Ɗan kore dole ya zama mai wayo, mai natsuwa da gaggawa ga aikata duk wani aikinsa ba da ɓata lokaci ba. Kuma an fi son ɗan kore ya zama ba sananne ba ne a idon mutanen gari. Idan so samu ne a wani lokaci an fi son baƙo, a wani lokaci ko ɗan gari sai a ƙulla da shi indai ba sananne ba ne a idon jama’a. Ɗan kore yakan yi shiga daban-daban, wani lokaci yakan yi shigar ƙauyawa, yakan kuma saka kayan Fulani, a wani lokaci yakan yi shigar yara gayu ko ya yi shiga ta siffar malamai da dai sauransu. Idan ɗan kore ya ƙware sosai babu yadda za a yi jama’a su gane cewa haɗin baki aka yi da shi a cuce su. Idan ɗan kore ya iya taka rawarsa sosai ɗan damfara zai tara kuɗi mai yawa. Bunza, (1989).
2.1.4 Matsayin Ɗan Kore A Damfara
Ɗan kore yana da muhimmancin ƙwarai da gaske wajen gudanar da damfara. Shi ne suke fara nuna wa mutane cewa abin da aka nuna masu gaskiya musamman ta hanyar siddabarun dandali.  Idan ɗan damfara ya nuna wa mutane kuɗi a bayyane yana cewa, “Ina mai naira ɗari ko ɗari biyar”, alhali a hannunsa akwai naira dubu ko dubu biyar. Cikin ɗan lokaci idan naira ɗari ce sai ka ga wani ya zo ya ce, ‘na saya naira dubu’. Bayan ya riƙe hannusa sai ya ce, “Malam ban sayar ba”. Bayan ya saki hannunsa sai ka ga naira dubu ta koma dubu biyar na take.
A ko da yaushe, irin wannan damfara mai suna, “Marmashe” duk wanda ka ga ya faye cin ta ɗan kore ne. kuma in mutum ba ɗan kore ba ne ko ya ci ana son a jawo hankalinsa ne a yaye shi sosai, shigo-shigo ba zurfi ne kawai. Kuma duk wanda ka ga ya riƙe hannunsa sai yawan kuɗin ya karu shi ma ɗan kore ne, shi ya miƙa kuɗin a yayin da yake haɗa jiki cikin ɗan lokaci (Bunza, 1989:277-278).
 Bayan wannan a wannan zamani ɗan kore yana taka rawa wajen gudanar da damfara, misali lokacin da aka shigo da shirin MMN Pozy Sheme a Nijeriya sai da suka yi amfani da `yank ore ta hanyar ba su ninika masu kuɗin da suka fara zubawa. Don haka su ne suka riƙa shiga cikin jama’a suna nuna masu irin ribar da suka samu da kuma ƙwaɗaitar da su, su shiga. Har ila yau, akan yi amfani da dabarar ‘hacking’, wato ɗan damfara aka shiga cikins wani ‘group’ ma’ana ƙungiya na wasu ma’aikata sannan ya talla hajarsa a matsayin ɗan wannan ƙungiya. Wannan kore ke nan ta amfani da na’urar zamani da sauransu.
2.2 Dalilin Yin Damfara
Hausawa sukan ce, “Banza ba ta kai zomo kasuwa”. Haka kuma, Ruwa ba sa tsami banza. Haka kuma ra’in wannan bincike shi ne, kwaɗayi mabuɗin wahala. Dangane da wannan akwai dalilai da dama da suka haifar da wanzuwar damfara a ƙasar Hausa. Dalilan kuwa su ne:
a.       Kwaɗayi: Hausawa sukan yi karin magana suna cewa, ‘kwaɗayi mabuɗin wahala’. Wannan haka yake domin dogon guri ga rayuwa kan haifar da rashin dangana da wadatar zuci wanda kan yi sanaɗiyar faɗawa tarkon damfara. Tsammanin son wani abu wanda mutum bai mallaka ba ko son karɓar abu cikin a wajen wani mutum shi ke jefa mutane cikin damfara tsundum (Adamu, 2008, Maiyama, 2001). Wannan bayani ya yi daidai da abin mawaƙi Muhammadu Ɗanƙurji yake cewa:
:Lantana jikanyar Buhari Aljannan makaɗa.
…………………………………………….
:Ɗan Malam Bawa mai mahaukaciyar biɗa,
:Ga ka da fam goma ka ga ƙwanjan sule guda,
:Har ka tsaya mai sule guda yana maka sababi

(Muhammadu Ɗanƙurji: Waƙar `yan caca).
b.       Son banza: Duk ɗan damfara yana son banza, haka shi ma wanda aka damfara son banza ya kai shi. Domin hangen abin da ke hannun wani da raina na shi shi ya kai har ka damfare shi.
c.       Neman arziki dare ɗaya: Sau da yawa mutane kan tsunduma cikin harkokin damfara saboda neman arziki cikin sauƙi babu wahala. Haka wanda aka damfara, tun da sun ga kuɗi ruwa-ruwa ana facaka, su ma sukan shiga ko sa samu nasu  (Adamu, 2008).
d.      Ƙuncin rayuwa: Ƙuncin rayuwa na ha’ula’i wanda mutum kan shiga ya rasa abin da zai ci kan haifar da tunanin shiga harkar damfara. Domin yunwa ba a ba ta sunan Allah. Don haka dole ne mutum ya yi tunanin mafita, wanda wasu kan faɗa damfarar mutane.
e.       Nuna bajinta: Nuna ta maza ko kuma aikata wani abin da duk ba kowa zai iya ba yinsa ba da son ayaba shi ke haddasa mutum ya shiga harkar damfara ta hanyar amfani da siddabaru da kuma amfani da na’urar zamani.
f.        Bushewar Zuciya: Wannan shi ne Yahya, (1994 da 1996) ya kira da rashin imani wato rashin tausayi. Rashin imani ke haifar da bushewar zuciya. Idan zuciyar mutumta bushe, wannan na iya sa mutum ya aikata duk wani abin assha da tir. Bayan kasancewar ɗan damfara mai cutarwa da rashin sanin ya kamata mutane suna masa kallon maras tausayi da guma baƙin ciki.
g.      Rashin Aikin Yi Ga Mutane: Rashin abin yi ga mutane kan haifar da zaman kashe wando. Zaman kashe wando zama ne na jiran tsammani na jiran Allah Ya ba ku mu samu. Akwai tabbacin cewa irin wannan zama na iya kai wa ga lalaci da yin damfara. Domin duk lokacin da zaman banza ya yawaita, mutuwar zuci kuwa za ta rufa baya a ƙarshe abin da zai faru shi ne rashin ɗiyauci. Matuƙa mutum bai da aikin yi, bai kuma ƙirƙiro wa kansa ba aikin da zai amfane shi ba to shi ƙarshensa damfara. Wannan ya zama tilas domin babu rayuwar da za ta iya tabbata cikin talauci da rashi, gashi kuwa tana ganin jama’a na kai kawo da harkokin kuɗi ba ta san ranta (Maiyama, 2001).
2.0 Ire-Iren Damfara
Masana da manazarta al’adun Hausawa sun raba damfara zuwa gida biyu manya, wato akwai damfarar gargajiya da kuma damfarar zamani.

2.1 Damfarar Gargajiya
Wannan ita ce nau’in damfara wadda Hausawa suke gudanar da ita ta hanyar amfani da dabarun gargajiya. Kuma wannan damfara na gudana ne a wuraren daban-daban, sannan kuma sukan yi ƙaryar ba da magani, kamar yadda Bunza, (1989) ya ce, “Ba sayar da wani magani suke yi ba illa yawon damfara, a birane da ƙauyuka”. Wannan nau’i na damfara ta kasu kashi-kashi kamar haka:
2.1.1 `Yan Wala-Wala
`Yan wala-wala mutane ne da ke amfani da wuri ko da takarda ko kati mai launin alamu, su juya su ta hanyar dabara don su yaudari idon mai kallo da taimakon `yan kore. Wala-wala caca ce wadda ake sa mai kwaɗayi ya zaɓi kati, in ya yi kuskure dole ya biya kuɗi (Alhassan da wasu, 1982:88).
`Yan wala-wala su ne `yan damfara da suka fara fitowa a ƙasar Hausa bayan bayanar Turawa a wannan ƙasa.[2] Wala-wala da kati ake yin ta, irin katin da ake caca da ita. Sukan shiga kasuwa su a je dandalinsu musamman a wuraren da ake yin ciniki sosai na awaki ko shanu ko dai wani abu mai kama da haka. Sukan nuna wa mutum kati a fili suna cewa:
                        “Wannan mai ci, wannan babu,
                        Idan ka ɗauki wannan ka ɗauki mai ci,
                        Idan ka ɗauki wannan ka ɗauki banza”.
A kan samu `yan kore masu ƙoƙarin nuna wa wanda bai sani ba, mai ci. `Yan koren nan sun san duk katin sosai da sosai. Da yawa sun sha haukata ƙauyawa musamman Fulani da ke zuwa da dukiya mai yawa kasuwa. Ana ce da su `yan wala-wala saboda yawan yawon da suke da hannuwansu wajen yin amfani da katin da lalewa da bazawa a ƙasa. Sukan ce, “Wala-wala ya ci ka” idan sun ci mutum, shi ya sa ake kiransu `yan wala-wala. (Maiyama, 2011:28)
A wasu lokuta `yan wala-wala sukan aro kuɗi hannun mutum sai su yi a ci, don ka gani wai kasa da kanka. Sun riga sun kiyaye duk katin, ko ka ga sun a je shi a gabanka ko ka ɗauka sai ka tarar ba mai ci ba ne.
2.1.2 `Yan Kalambe
Kalambe kwali ne ake yi wa zane-zane da hoton abubuwa da dama kamar kada da tsari da damo da mota da keke da shamuwa da maciji da sauransu. Za a huje tsakiyaarsa a saka icce da waya a yi mata ƙugiya a jiye a yi rami a yi mata turke. Mai buga kalamben zai zauna a kan turmi ƙafafunsa na ƙasa, yana mazaya abubuwan kalamben na gewaye kamar tayar keke da gudu. (Maiyama, 2011:28 a cikin Bunza, 1989).
Ɗan damfara kan fara sa kuɗinsa `yan korensa su sa nasu, sai ƙauyawa da masu son kuɗin banza su yi tasa nasu. Duk hoton da ƙugiyar ta nuna mai hoton ne ya ci. A irin wannan damfarar mai buga kalamben da ke zaune da ya ga hoton da ɗan kore ya zaɓa sai ya ɗaga guiwarsa ya tsayar da wayar a hankali ba da sauri ba, yadda ɗan kallo ba zai fahimta ba. Yanzu irin wannan damfarar a ƙauyuka ne kawai ta ke ci ko a cikin yaran da ba su san ciwon kansu ba. (Doma, 2018:23).
2.1.3 `Yan Marmashe
`Yar marmashe dai ita ce damfarar da ake yi a fili ƙuru-ƙuru a idon jama’a. Mai damfarar zai ɗauko yagaggun takardu ne ya ce, ina mai saya naira goma, ga kuma naira ɗari a cikin hannusa ana gani. A wasu lokuta kuɗin na ƙaruwa kamar dai a ce magani ne alhali dabaru ne kawai. Bisa gaskiya idan mutum ba ɗan korensu ba ne ba zai ci nasara samu kamar sa. Yadda suke wannan damfara shi ne idan mai damfar ya ce wa zai saya? Sai  wani ɗan kore zai zo ya ce, “na saya biyar”. Bayan ya riƙe hannunsa sai ya ce: Malam ban sayar ba. Bayan ya sake hannunsa sai ka ga kuɗin ya koma naira arba’in ko naira ɗari nan take. A koyaushe a irin wannan damfara mai suna, ‘Marmashe’ duk wanda ka ga ya faye ci to, ɗan kore ne. idan kuma mutum ba ɗan kore ba ne, ko ka ga ya ci ana so a jawo hankalinsa ne a yaye shi sosai. Shiga-shigo ba zurfi ne kawai. Kuma duk wanda ka ga ya riƙa hannunsa sai yawan kuɗin ya ƙaru shi ma ɗan kore ne, shi ya miƙa kuɗin a lokacin da suka haɗa jiki cikin ɗan lokaci ƙanƙane kuma ana yin aikin cikin hanzari da wayo sosai (Bunza, 1994).
2.1.4 Damfarar Dabo
Masu wannan damfara sukan yi kuɗi ne, ko su tono su daga cikin ƙasa, ko su karɓo su daga sama. Suna kuma iya cika wani abu da su, a gani kamar da gaske. Wato sukan yanka fararen takardu su zama kuɗi. Amma a zahiri ba haka yake ba kau da ido ne, domin yawancin lokuta da sun ba mutum kuɗi za su ɓace ko kuma su koma takarda ko ganye. Suna nuna wa mutane gawar jikinsu a cikin ruwan masaki ko kwartanniya, sannan su shawarce su a kan yadda za su yi su kuɓuta daga halaka. A kan kira masa maƙiyinsa a nuna masa a gabansa. Wasu kuma sukan saka ƙwai a cikin kwalba ya kuma yi magana. Bayan haka ana harhaɗa wasu abubuwa a tada wuta ko a fitar da ruwa, ko a fitar da wani wuri ko wani abu, kamar a fitar da zinari ko azurfa daga wani wuri ko daga jikin kowane abu, ko a yi ruwan kuɗi ko a nuna dabbobi ko wani abin hawa kamar jirgin ruwa da mota.
Haka nan kuma suna iya juyar da murya wadda ba a sanin mai ita, ko su nuna wa mutum abubuwan fake, kamar kiran sarkin Aljannu, a yi magana da shi baki da baki, ko mayar da ƙarhu ko jela ko wata igiya ta zama maciji, ko a mayar da sansami ko ganye ko wani abu kuɗi wanda ake amfani da su a wannan lokaci. Ana iya canza kamannin mutum, kamar gajere ya zama dogo, ko ramamme ya zama mai ƙiba ko marar lafiya ya ji ya warke, da sauran siddabaru da suke yi don su damfare mutane da su.
Duk wannan damfara ba yiwuwa sai da saddabaru saboda abubuwan da suke yi tsagwaron wayo ne kawai ba tsafi ba ne.  `Yan siddabaru sukan yi amfani da ƙahon rago ƙarami su sami takalman soso, su soka allurai kamar ɗari a soson, sai su saka shi a cikin ƙaho. Bayan wannan, sai su rufe ƙahon da wani marfi daban, a yi wa marfin huda gwargwadon yawan allurai da ke cikin ƙahon. Kuma za a yi saiti daidai yadda da an ɗauko ƙahon, aka jirkita kaɗan, sai a ga allurai sun turo kansu da yawa amma ba za su fito ba, domin suna ɗaure a can cikin ƙahon.
Bayan an shirya wannan ƙaho sai mai siddabaru ya shiga damfara yana karɓar kuɗin mutane. Idan ya tara kuɗin mutane da sunan ba su wani abu, sai ya ce ya fasa, can sai wani mutum ya fito ya ce, “Wallahi bai amince ba, sai an biya shi kuɗinsa, nan take sai ɗan siddabaru ya ce, “Zan harbe ka da allura”. Ya zaro ƙaho ya fito da alluran, ya yi ihu sai a ga mutumin ya faɗi yana kuka, ga allurai a rigarsa da hularsa da wandonsa a sassaƙe, ga su ko’ina a suturarsa daɓa-daɓa. Hausawa sun ce, gani ga wane ya isa wane tsoron Allah. Da zarar mutane sun ga wannan sai su riƙa cewa, “Mun yafe” a dinga suɗaɗewa ana tserewa da ɗaiɗai da ɗaiɗai. Amma a zahirin gaskiya mutumin da ya zo ya ce bai yarda ba ɗan kore ne. kuma dama kafin ya shigo fage ya sossoka allurai a suturarsa a ko’ina yadda idan mutum ya gani sai abin ya ba shi tsoro da mamaki ya kuma zaci cewa lallai mai magani ne ya harbe shi da allurai. Yana fito wa sai ɗan siddabarun ya yi hito ya ciro wani ƙahi da allurai suke ciki ya ce ya harbe shi, shi ko ɗan koren ya faɗi (Bunza, 1989).
2.1.5 Damfarar Bokaye
Tun kafin zuwan Musulunci bokaye su ne likitocin gargajiya na kowace irin cuta ko annobar da ta ɓulla a ƙasar Hausa. Sun riƙa ba da magani kuma wurinsu ne ake zuwa a karɓi magani. Don haka kafin bayyanar asibitocin zamani, bokaye ke cin Karen su babu babbaka domin ba su da abokan hamayya. (Bunza, 1989, Wushishi, 2011:51).
Idan mutum ya je wurin boka domin neman wani taimako sukan umurce shi da yin waɗansu abubuwa kamar shiga da ƙafar hagu ko shiga da baya, ko kar a yi sallama, ko su ce a yi a hankali kada a taka masu `ya`yan aljannu. Wasu sukan bayyana abin da ke tafe da mutum ta hanyar faɗi sunan mutum da iyalansa da sana’arsa da buƙatar da ke tafe ta shi. Duk wannan yana faruwa ne ta hanyar ɗan kore. Domin shi ne zai ba mai buƙata shawara da ya tafi wurin boka wane aikinsa yana ci. Dama gidan boka ƙofa biyu ne, ɗaya na boka da mutanensa aljannu da `yan kore, ƙofa ɗaya kuma na shigowar mutane. Bayan haka sai su ce Aljanni ya ce buƙarka za ta biya amma sai ka kawo baƙin bunsuru ko baƙar kaza ko ƙahon wani dabba, kamar jaki ko raƙumi, ko nonon kaza, ko bahagon ɓera da dai sauransu. Idan mutum ya ce bai iya samowa sai su ce ya kawo kuɗi a ba aljannu su samo masa waɗannan abubuwa. Saboda tsabar iya siddabaru da wayo idan mutum ya kawo kuɗin su ce ya ajiye a ƙasa ba su amsa da hannunsu sai aljannu za su ɗauka da kansu. (Ibrahim, 2012:25)
2.1.5 Damfara A Ciki Tsibbu
Tsibbu ba Bahaushiyar kalma ba ce, daga Larabci Hausawa suka aro ta. Amma an Hausance kalmar, tsibbu na nufin magani da ya keɓanta ga malamai. (Wushishi, 2011).  Malamin tsibbu yana amfani da ayoyin Alƙur’ani wajen gudanar da ayyukansa. Waɗannan malamai ba su yi karatu da yawa ba sai dai sun iya karatu baki gwargwado. Sharuɗɗan tsibbu shi tilas ne malamin ya mallakin kundi[3] wanda ciki ne ya ajiye kayan aikinsa. Bayan haka malaman tsibbu sukan yi duba ta hanyar bugun ƙasa da istihara[4]  da fassarar mafarki da duban carbi da sauransu. (Yahaya da wasu, 2001:32-34).
Ta wannan fuskar Malaman tsibbu suna da hanyoyi da suke gudanar da damfara a cikin al’ummar Hausawa ta hanyar amfani da maganin da suke kira, ‘sirri’[5] da ‘naƙali’[6] sukan yi amfani da waɗannan abubuwa wajen yin damfara ta hanyar sa dokoki masu tsanani da wuyar kiyayewa don haka sai mai biɗar magani ya nemi sauƙi ta yadda za su tsadance da shi. Malam sukan yi amfani da siddabaru wajen karɓar kuɗi a hannu mutane, wanda wannan zunzurutun wayo ne da dabara da kaifin hankali har mutum ya ɗauka cewa Rauhani ko Aljani ko Ibilis ne ke yin wannan aiki domin ya saɓa wa hankali. Daga cikin wannan siddabaru akwai bugun alƙalami da fito da hatimi a takarda a cikin ruwa da dabon hatimi a gaban idon mutum da sa ƙwai a ciki kwalba a ɗaure su da sa ƙwai ya tashi sama da sa kwalba ta kama takalmi ko kara da sauransu. (Bunza, 1989).
2.1.6 Damfarar Zamba Cikin Aminci
Alhasan, da wasu (1982) sun bayyyana wannan damfara da cewa, ita ce ake yi wa mutum idan mutum ya kawo kuɗinsa ajiya, domin zai haɗu da wani mutum mai albarka. A kan yi wa mutum dabara a nuna masa sani da sabo, inda a kan kira sunansa da na iyayensa, da garinsu, da sana’arsa da kuma buƙatar da ya sa wa gaba a ransa. A kan kuma yi wa namiji ƙifƙiftau da mace, a dibirce shi, ko a yi da mace ko da wani mai kuɗi ko sarauta ko ilimi, ta hanyar zamba cikin aminci. Wannan duk yana faruwa ne ta hanyar ɗan kore wanda zai ba da bayanin mutumin da buƙatarsa tun kafin ya zo wurin. Sannan kuma shi ne zai turo wannan mutumin zuwa wannan wurin domin biyan buƙatarsa. Misali wannan damfara shi ne kamar yadda Maiyama, (2008) ya kawo misali a cikin Littafin Ruwan Bagaja inda Alhaji Imam ya yi Malam Zulƙe wayo ya damfare shi a lokacin da suke cikin tafiya tare, sai ya kwashe labarin yadda ya samu kuɗinsa kaf ya shaida wa Alhaji Imam saboda aminci. A lokacin da Malam Zulƙe zai tsaya ratsi sai ya ba Alhaji Imam kuɗi ya riƙe mashi, amma da ya dawo ya buƙaci kuɗinsa sai Alhaji ya hana shi, ya ce, ‘kuɗinsa ne’. Haka kuma wani misali na fito da damfarar zambo-cikin-aminci a lokacin da ɓarawo ya zo yi wa Alhaji Imam sata sai Alhaji ya yi amfani da wannan dabara ta zambo ciki aminci, ga yadda abin ya kasance:
Maraba, maraba. Ga tabarma ka zauna. Ashe za ka zo ka ƙi gaya mini tun da rana da muka gamu a kasuwa. Alhaji ya ci gaba da cewa, “Na yi ta yi masa magana kamar na san shi.
Da ɓarawo ya fahimci nuna sani ya yi yawa, sai ya ce, “Ina ka san ni?’.
Shi kuma Alhaji ya ce, ‘ai tuni na san ka, bari ta kai ma duk danginka na san su, duk kuwa sun san ni’.
Da ɓarawo ya ga da gaske Alhaji yake yi sai ya ce wa Alhaji, “Kai in ka san ina sunana?’. Sai Alhaji ya ce, “Na yi ihu da ƙwarai na ce, ‘ai sunanka, ‘Ɓarawo”.

Muna iya cewa Alhaji ya yaudari wannan ɓarawo ta hanyar nuna sani wataƙila ba don ya yi amfani da wannan hanyar damfara ba da ɓarawo ya cuta masa. Don haka ana ganin Alhaji ya yi amfani da wannan hanya ce don ya kori ɓarawo.
To, haka masu yin wannan damfara ke yin amfani da nuna sani a fili domin su damfari mutum. Don haka a lura duk lokacin aka ga mutum yana ƙoƙarin nuna wa wani sani ƙarfi da yaji ya dace a tuhumi wannan mutum sannan kuma kada a yi saurin amincewa da shi domin gudun faɗawa tarkon damfar zambo cikin aminci.
2.1.7 Damfarar Ɗauki-Ka-Ba-Ni
Wannan damfara ce da ake yi wa `yan damfara, ba kowane irin mutum ake yi wa ba. Galibi bayan `yan damfara sun yi damfara sun tara abin duniya, sai mai ɗauki-ka-ba-ni ya zo dare ɗaya, ko ma rana ɗaya, ya yi masu wayo da dabara ya damfare su ya kwashe duk abin da suka tara kaf, ya tafi abinsa. Watau dai son abin duniya da ƙwaɗayi da rashin aikin yi su ke sa mutum ya tasirantu da damfara har ya yarda a damfare shi (Alhasan da wasu, 1986:89).
2.1.8 Damfarar Gada-Gada
Wannan nau’in damfara kamar yadda Maiyama, (2008) ya riwaito Bunza, (1994) cewa ita ce damfarar da ake yawo da hankalin mutum da dibirta shi wanda akasari aka fi yi wa baƙi waɗanda ba su san gari ba. Kuma masu yin wannan damfarar wasu lokuta sukan shiga rigar hukuma. Misali idan mutum baƙo ya zo yana neman wani wuri musamman mutumin karkara wasu `yan birni kan yi amfani da wannan damar wajen damfarsa. Misalin wannan shi ne lokaci da Malam Haruna da Maikuɗi suka tafi birni duba ɗan uwansu da hukuma ta kama. Ga yadda abin ya kasance:
“Malam Haruna da Maikuɗi suka yarda saurayin ya wuce gaba suka bi shi. Ya shiga wannan lungu da su ya fita wancan har dai suka gaji da tafiya. Har Malam Haruna ya ce, “Shin samari har yanzu ba mu zo wurin ba ne?”
Ga abin da ɗan banzan ya ce:
“Kada ka gaji baba, ai wurin ne da `yar tazara, amma mun kusa zuwa. To, ba don kun same ni na ɗauki ɗawainiyar kawo ku ba, da ya za ku zo nan da kanku”. Bayan `yan tafiya kaɗan suka iso wani ɗan fili sai gogan ya ce, to, sai ku tsaya nan in je in sanar da masu gadin ga ku kun zo, in yi muku iso.
Jin kaɗan saurayi ya dawo ya koma ya ce, to, na shaida masu. Amma da ƙyar da lalama daban baki suka yarda. Kun yi sa’a da cewa suka yi wai tikitin rasil ɗin shiga ya ƙare sai jibi. To, amma tunda sun yarda sai ku kawo kuɗin tikitin rasil na Naira huɗu ku biyu ke nan.
Malam Haruna ya sa hannu ya ɗauko jakarsa ya kwance ƙullin ya zazzaro Naira huɗu ya miƙa masa. Bayan ya ga ya damfari ƙauyawa sai saurayin ya koma bakin ƙofar kurku ya ɗan jima kaɗan sai ya dawo ya miƙa wa Malam Haruna da Maikuɗi waɗansu `yan guntayen jajayen takardu guda biyu ya ce, ‘To ga tikitinku na rasil. Ku je ku shiga kawai. Sai Malam Haruna suka karɓi wannan rasil suka kuma gode nasa. Ba su san cewa ɗan saurayi damfararsu ya yi ba.


2.1.9 Damfarar Gardawa
Gardawa suna nuna siddabaru da waibuwa iri-iri domin su damfari mutane. Suna gwada abubuwa kamar cin kasuwar sama, ko ƙone yaro da yanke shi, a warkar da shi, ko a ƙona tufa daga baya a fito da ita. Kuma ana iya shiga cikin wata dabba a fita wani wuri ko su shuka duma ko kabewa ya tsiro ya yi yaɗo da `ya`ya nan da nan. Ana iya kuma saka wuƙa cikin baki a fitar da ita ta hanci ko a karɓo wani abu daga sama Bunza, (1986).
2.2 Damfarar Zamani
“Zamani abokin tafiya, idan zamani ta ɗinka riga tilas ne a sa”. Damfara ta shiga cikin tafiyar zamani, domin lokacin da ake ganin an samu ilimi da wayewa ta ƙara yawa, a lokacin ne mutane suke ƙara fito da sabbin hanyoyin damfara. Sannan samuwar na’urori da ci gaba zamani su ne suka haifar da damfara zamani. Damfara ta shiga hanyoyin zamani kuma babu wanda yake tsallake wannan nau’i na damfara. Ma’ana da jahilai da masu kuɗi da masu ulimi duk suna faɗawa cikin wannan tarko.
3.2 Hanyoyin Damfara Na Zamani
Akwai hanyoyi da dama da ake amfani da su wajen gudanar da damfara ta zamani waɗannan hanyoyi su ne:
3.2.1 Ta Hanyar Satar Bayanan Sirri Na Asusun Ajiyar Kuɗi A Banki
Mutane da dama sun samu kansu cikin rigima da bankunansu ta hanyar bayar da bayyanin siiri a kan asusun ajiyar kuɗinsu na banki. Dabarar da `yan damfara ke amfani da ita, ita ce ta hanyar kiran mutum a waya, su ce daga banki ne, ana buƙatar ya ba da lambar sirri wato PIN[7] ko lambobi huɗu na ƙarshe a katin ATM. Da zarar sun sami abin da suke buƙata sai su washe asusun nan take.
A wasu lokuta sukan tura saƙo a wayar mutum cewa daga bankin da yake hulɗa da su ne, akwai matsala a asusun ajiyarsa don haka ya kira wannan lambar domin warware wannan matsalar. Idan mutum ya kira su za su buƙaci muhimman abubuwa da suka shafi asusun ajiyarsu, idan aka yi rashin sa’a suka samu nan take sukan kwashe kuɗin ajiya daga asusun. Haka kuma akasari sun fi yin wannan damfarar ranar da banki ba su aiki. Don haka kafin ranar da za a kai ƙorafi a banki sun riga sun kammala nasu aikin na damfara.
Akwai wasu mutane da kan zo su tsaya a injin na cire kuɗi wato ATM[8] suna ƙoƙarin satar lamar sirri na mai hulɗa da banki. Idan kuma sun yi sa’a wanda ya zo cire kuɗi bai iya amfani da na’urar ba kuma ya nemi taimakonsu, sannan ya nuna masu lambar sirrinsa. Daga nan shi ke nan sun dinga ɗiban kuɗinsa sai in ya je banki ya kai ƙorafi an toshe wannan asusu. Mutane da dama sun faɗa cikin wannan tarkon.[9]
3.2.2 Damfara Ta Hanyar Mutuwa Da Taimako
Wannan ita ma wata hanya ce ta damfara, a kan turo saƙon Email ko kuma a kira mutum kai tsaye daga wata ƙasa ana shaida maka cewa wani bawan Allah ya mutu kuma ba shi da mai gadonsa amma kai ake so a miƙa wa wannan dukiya ta hanyar amfani da bayanan da wannan mutumin ya bari na wasiyya cewa, akai dukiyarsa ƙasashen Afrika. Sukan yi amfani da muryar mace ko wani namiji da sunan ma’aikacin baki ko kuma manajan wannan mutumin da ya mutu. Daga ƙarshe za su buƙaci mutum ya tura wasu kuɗaɗe waɗanda za a gyara hanyoyin da kuɗaɗen za su isu wajensa. Wannan wata sabuwar hanyar damfara ce.
3.2.3 Damfara Ta Hanyar Aljannu Masu Taimako
Wannan wata hanya ce da `yan damfara ke amfani da ita da sunan taimako don cutar da jama’a. Yadda suke yin abin shi ne wani ne zai kiraka a waya ya ce, yana buƙatar ka yi wa Annabi Muhammadu (S.A.W) salati, ka karanta wasu ayoyi sai ya umurce ka da ka matsa gefe guda.  Idan mutum ya faɗa wannan tarko sai ya ce, “Shi Aljani ne”. Daga nan sai ya yabeka ya nuna ka taɓa taimakonsa ko mahifinsa ko wani abu mai Kaman haka shi ne yake so ya saka maka da dukiya mai yawa. Saboda haka zai fara faɗa maka ka yi kaza, ka yi kaza. A ƙarshe ya ce wasu irin kuɗi kake buƙata a taimaka maka da su, misali idan mutum ya ce dalar Amurka yake so, sai ya ce, ka je ka same su ka zuba cikin abu irin kaza a kai wuri kaza, a daidai loaci kaza za su mayar maka da su miliyoyi. Wani lokaci za ka ji sun ce su Aljanu ne daga Makka ka fara sayen kati ka tura masu.
To ko dai mene ne Aljanu ba su magana da mutane ta waya, kuma ba sa buƙatar layin sadarwa domin su yi magana. Hasali ma ba a ganin Aljani kuma ba yin magana da su sai ta bori ko ta Rukiyya, in ba haka ba duk wanda ya ce shi Aljani ne yana magana da mutane kai tsaye to ɗan damfara ne, a kiyaye.
3.2.4 Damfara Ta Hanyar Kwangilar Kwastam (Custom)
Wannan ya fi yaɗuwa a shafin sada zumunta na Facebook. Wani kan fito ya ce shi ne jam’in hana fasa ƙwabri mai kula da kayyakin da suka kwace waɗanda aka shigo da su ta ɓarauniyar hanya. Saboda haka gwamnati tana yin gwanjonsu sai ya lissafo kayayyakin da kuɗinsa sannan ya saka adireshin Intanet da za bi a biya kuɗin. Irin wanann damfara an daɗe ana cutar mutane da ita, kuma hukumar Kwastan ta sha fitowa tana cewa ba ta da alaƙa da irin waɗanann mutane don haka a yi hattara.
3.2.5 Damfara Ta Hanyar Buɗe Shafin Sada Zumunta da Sunan Mace
Wannan shi ma a shafin sada zumunta na Facebook da Whatsapp ake yin sa. Sukan buɗe shafin sada zumunta da Facebook ko Whatsapp da sunan mace sanann kuma su saka hoton mace kyakkyawa domin ɗaukan hankali. Daga nan sai su aiko da saƙo neman abokata dazarar ka amince har kuka fara hulɗa sai a aiko maka da hotuna na jan ra’ayi daga nan sai a fara neman wasu kuɗaɗe da zumar toshi.
Yawanci irin waɗannan shafuka na maza ne suke amfani da ita wajen damfara. Idan mutum ya matsa cewa sai ya yi magana da ita sai su nemi wata mace su ba ta ku yi magana. Da haka har su damfari mutum kuɗi mai yawa sai daga ƙarshe idan dangantaka ta ginu sai goge wannan shafin.
3.2.6 Satar Shafin Sada Zumunta Da Wani
`Yan damfarar zamani sukan yi ƙoƙari su saci shafin sada zumunta na mutum su yi amfani da shi wajen yaudarar mutane musamman abokansa da kuma makusantansa. A kan yi magana da abokan mutum a matsayin shi yake yi, sai su yi amfani da wanann damar su nemi taimako na kuɗi na wucin gadi da cewa idan sun haɗu za ya biya. Wani lokaci sukan buƙaci a aika masu da katin waya. Sukan nuna cewa suna wani wuri kuma sun samu matsala don haka suna buƙatar kati. To wanan ma wata hanya ce ta damfara.
3.2.7 Saƙon Albishir Daga Kamfanin Waya
Wata hanya ta damfara a wannan zamani ita ce ta aiko da saƙon albashir daga gidan waya na cewa mutum ya yi nasarar cin wata kyauta ko kuma lambar aka zaɓa a wajen gudanar da wannan gasa kuma ya ci naira miliyan ɗaya da sauransu. Don haka ana buƙatar ka ba da kuɗi kaza kafin a aiko maka da waɗannan kuɗaɗe. To wannan ma wata hanyar damfara ce.
3.2.8 Damfarar Kawo Kuɗi Na Ninka Maka
Wannan hanyar damfara ta shahara a Intanet da zahiri. Wanann wankiya ce tsagwaronta da ake amfani da dabarar buɗe wani kamfani. Za a faɗa cewa wanann kamfani yana harkar sayar da ɗanyan mai da gwal. Don haka idan ka saka hannun jari na naira dubu ɗaya wani mako mai zuwa za su ninika maka ya koma dubu biyu ko fiye da haka.
Haka kuam a Intanet a an ɓullo da wani tsari na kasuwanci wanda ake kira Foreɗ Trading wanda a zahiri akwai su. Amma `yan damfara suna amfani da wanann wajen cutar mutane ta hanyar ƙwaɗaitar da su cewa duk abin da mutum ya sa za a nininka ma shi. Kuma kuɗinka zai riƙa ƙaruwa dangane da yawan mutanen da ka kawo. Sukan yaudari mutane da fara ba mutanen farko domin su yi shigo-shigo ba zurfi. To duk waɗanda suka biyo bayan wannan mutum duk yaudararsu za su yi.
3.2.9 Damfarar Ta Satan Bayanan Sirri
Wannan hanya ce da ae damfara ta amfani da na’urar kwanfuta. Wanann satar bayanai sirri shi ne ake cewa, “Techincal Hacking”. Domin kowace kwanfuta tana da abin ɗaukar hoto wanda ƙwararru suke amfani da ita wajen gano bayanan sirri na mutum. Domin babu wani abu da mutum zai yi face suna ganinsa. Sukan yi amfani da wannan damar wajen samun bayanai na siiri da kuma amfani da su wajen damfara. Misali: Mutum yana zaune wata ƙasa yana shiga yanar gizo domin neman bayanan sirri ta hanyar Imail da sauransu. A irin wannan damfarar a kan samu bayanan sirri na banki a shiga cikin asusun masu ajiya a ɗebi kuɗi ba da saninsu.[10]
3.2.10 Damfara Ta Amfani Da Na’urar Kamfuta
Masana ilimin kwanfuta na amfani da ita wajen gudanar da damfara. Ana amfani da wannan na’ura a matsayin `yan koren zamani. Bokaye na sanya na’urar kamfuta a wani ɗaki da suke fara ajiye mutane kafin su gane da su. A lokacin da mutum yake wannan wuri duk abin da yake aikatawa suna ganinsa. Don haka da ya zo sai su fara ba shi labarin abin da ya aika a bayan idonsu. Wanann kan ba mutum mamaki ya ɗauka cewa wata baiwa ce ta daban. Don haka du abin da aka faɗa masa sai ya amince nan take.
Haka kuma sukan yi amfani da wannan na’ura wajen faɗa wa mutum wasu matsaloli da yake fuskanta. Wannan yana faruwa ne ta hanyar `yank ore. `Yan kore kan zauna su riƙa amfani da tsarin sadarwa na Whatsapp suna ba da bayanin abin da mutum yake aikatawa alhali bai sani ba. Don haka sai `yan damfara su kira mutum su riƙa faɗa masa abin da yake aikawa a halin yanzu. Daga sai su umurce da ya kai wasu kuɗaɗe a wani wuri ko kuma ya aikata wani abu buƙatarsa za ta biya.
3.2.11 Damfarar Neman Aiki
Wannan wani nau’in damfara ce da ake aiwatar musamman ga masu neman aikin gwamnati. A irin wannan damfara akan yi wa mai neman aiki alƙarin sama masa gurbin aiki a wata ma’aikata ko kuma wata hukuma amma sai a umurce shi da sai ya biya wasu kuɗaɗe na toshiya baki kafin a ba shi takardar ɗaukan aiki. Mafi yawa  `yan boko ne masu son samun aiki a ma’aikata mai tsoka wato NNPC ko kuma wani kamfani don haka a kan umuurce su da biyan kuɗaɗe masu tsoka kuma daga ƙarshe ba su ga tsuntsu ba su ga tarko.[11]
3.2.12 Damfara Ta Hanyar Wayar Hannu
Ana mafani da wayar hannu wajen gudanar da damfara. Masu yin wannan damfarar sukan kira mutum ne su ce daga bakinsa sannan su bayyana masa sunansa da shekarun haihuwarsa da ranar da ya buɗa asusun ajiya.  Daga nan sai su buƙaci ya ba su lambar katin ATM. Wasu kuma sukan nemi lambar sirri na ajiyar kuɗi. Haka kuma wata hanya ita ce wadda ake cewa an kawo wani tsari na taimakonn jama’a. wanda mutum zai ba da kuɗi a ninika masa.misali: MNN Ponzy Scheme wanda aka yi amfani da shi aka damfari mutane da yawa. A halin yanzu an ɓullo da wata hanyar yaudara ta waya wanda za a aiko wa mutum a umurce shi da ya shiya wani tsari wanda daga bisa za a buƙaci ya cike ta hanyar bayar da sunansa da lambar asusun ajiyarsa na banki da sauransu. Da zarar mutum ya bi umurnisu to, shi ke nan za a kwashe duk ajiyarsa a banki.
Akwai kuma hanyar aiko da saƙo da hanyar Imel wanda ake yi wa mutum albishir cewa yana daga cikin wanda gwamnati ta zaɓa da za a ba muƙamai don haka ya turo bayanansa wato CƁ da zarar ya yi sai kuma su aiko masa cewa akwai buƙatar ya aiko da wasu kuɗaɗe domin za a kama masu wurin da za a ba su horo na sanin makaman aiki. Daga ƙarshe sai akai mutane a ajiye a wani hotal wanda bai kai yawan kuɗin da suka aika ba. Kuma irin wannan damfara an fi yi masu ilimi kuma da gogaggun yan boko.
3.3 Illolin Damfara
Babu tantama, damfara ba ce mai tattare da illoli masu yawa ga al’umma. Bisa ga bayanai da aka samu ƙalatowa yayin gudanar da wannan bincike sun haɗa da:
a.       Haifar da tsiya da talauci: Mutane da yawa sun tsiyace saboda an raba su da abin da suka malla don haka suka faɗa cikin talauci. Kamar yadda Ibrahim, (1982) ya bayana cewa damfara ta haifar da talauci da jefa mutane cikin rayuwar ƙa-ƙanikayi. Wasu ma takan yi sanadiyyar rasa hankulan su ko ma rayuwa baki ɗaya.
b.      Sauya Bagirn Arziki: Idan aka damfari mutum duk abin da ya mallaka yakan sauya hannu daga wannan zuwa wancan. Don haka ɗan damfara da arziki sun riski juna ne don ba shi ya nemo shi shi ya sa ake samun lalacewa arzikin da ka samu ta hanyar damfara.
c.       Karya tattalin Arzikin Ƙasa: A duk lokacin da aka samu arzikin ƙasa na bin hanyar da bai dace ba, ma’ana haramtacciyar hanya wadda gwamnati ba ta amince da ita ba, to yakan haifar da matsalar tattalin arziki a wannan ƙasa. Domin gwamnati za ta rasa hanyar samun kuɗaɗen shiga. Haka kuma idan ɓarnar damfara ta yawaita tana iya durƙusar da ƙasa nan take musamman `yan damfara na zamani ta hanyar Intanet da ke kai kuɗi ƙasashen ƙetare suna ɓoyewa.
4.0 Sakamakon Bincike
A ƙarshe an fahimci cewa damfara, ruwan dare babu jinsin da ba su yi. Kuma babu wanda ya ƙetare karkonsu sai wanda ya cire wa kansa kwaɗayi da son abin duniya. Binciken ya fito da dabarun bincike na gargajiya da na zamani waɗanda ake amfani da su wajen karɓar kuɗi a hannun mutane. A zamanin da, `yan damfara suna amfani da hanyoyin siddabaru na gargajiya wajen aiwatar da damfara, sannan damfar da su ta danganta ne ga wanda bai san irin siddabarun da suke amfani da shi kuma taƙaita ne a wurin da suke gudanar da ita kawai. Wanda yanzu a wannan zamani damfarar ta ɗauki sabon salo, domin ana amfani da abubuwan da zamani ya shigo da su wajen yaudarar mutane. Nau’o’in damfarar zamani sun haɗa dukan rukunin jama’a da ke cikin al’umma. A damfarar zamani wasu takan rutsa da wasu mutane saboda rashin sani, wasu kuma tsananin kwaɗayi ne ke haifar da shi. Masu damfara sukan yi amfani da sabon tsarin da bankuna suka fito da su, wajen damfarar mutane. Wasu mutane ne kuma suna amfani da wayar hannu domin damfara, yayin da wasu kuma sukan shiga shafukan sadarwa na zumunta na zamani domin damfarar mutane. Sannan damfara mafi muni shi ne wanda ake yi ta hanyar Intanet domin a wannan hanyar miliyoyin daloli ake kwashe a asusun ajiya a sauya masu wuri cikin ɗan ƙananen lokaci. Akasari masu gudanar da wannan damfara ana kirasau da suna, “Yah[12]oo boys”. Haka kuma binciken ya fahimci abubuwan da ke haifar da damfara da dalilan yin damfara da illolin damfara. Daga ƙarshe bincike ya gano cewa ba wani abu ke sa a damfari mutum ba sai kwaɗayi wanda Hausawa ke yi wa kirari da mabuɗin wahala. Domin kwaɗayi ya haifar da mutane sun yi hasarar dukiyoyi masu tarin yawa. Don haka ya kamata mutane su kiyaye a duk lokacin da suka ga wani wanda ba su fahimci shi ba, ka da su yi saurin faɗawa cikin wannan lamari sai sun tuntuɓi masana.
5.0 Kammalawa
Damfara ruwan dare ne game duniya. Domin babu lokaci ko yanayin da ba a gudanar da ita. Haka kuma a wancan zamani ana amfani da siddabaru wajen aiwatar da damfara. Sannan kuma `yan kore sun taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da damfara. Domin damfara ba ta yi yuwa dole sai an samu ƙwararren ɗan kore wanda zai taimaka wajen turo mutane a damfara su. waɗannan `yan damfara sun haɗa da bokaye da malaman tsibbu da gardawa da sauransu Amma yanzu da aka samu wayewar kai sai damfara ta ɗauki sabon salo. Wato da shiga sahun amfani da abubuwan da zamani ya kawo. Waɗannan na’urorin zamani su ne suke matsayin `yan a sigar damfarar zamia, saboda ta amfani da su ne ake samun bayanai da za a yi amfani da su wajen damfara. Wannan ya ba `yan damfara damar shiga cikin rigar zamani su ci karen su babu babbaka. Waɗannan nau’o’rorin zamani sun taimaka wajen aiwatar da damfara ta yadda wanda aka damfara babu yadda zai gane sai bayan aikin gama ya gama. Damfarar zamani ta ɗauki fuskoki da dama kama daga damfarar satar sirrin banki da ta satar kuɗi a asusun banki da ta amfani da wayar hannu da sauransu.



[1]  Hira da Malam Aminu wani wanda `yan dafara suka samu sa’arsa a ranar 16/10/2018
[2] Bunza, (1994) “Damfara Da 419 A Bahaushiyar Al’ada” (Nazarin Nasonsu da Damabalarsu A Rubutattun Ƙagaggun Labaran Hausa). Takarada da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani a jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
[3] Kundi wani littafi ne wanda ya ƙunshi hatimai na zane-zane da baƙaƙen Larabci ko aƙaluna iri-iri.
[4] Wata hanya ta hango buƙatar mutumin da za a damfara
[5] Idan an ce sirri ana nufin wasu abubuwa ne da sai wanda ka yi da abinsa sai ko wanda sai ko in an nemi taimakonsa ya bayyana.
[6] Yana da alaƙa da asiri sai dai shi naƙali sai wanda aka naƙaltawa mutum kawai zai iya sarrafa shi.
[7] Lamba ta sirri da kowane bai ajiya a banki yake amfani da ita wajen cire kuɗi.
[8] Na’ura da ake liƙa wa a bango a bakin baki wanda mutane ke zuwa suna cire kuɗi. Da Turanci a cewa, Automated Teller Machine.
[9] Hira da Malam Sani wani wanda ya faɗa tarkon `yan damfara.
[10] Hira da wani masanin Kwanfuta a garin Sakkwato a ranar 18/10/2019 na ƙarfe 10 na safe
[11] Hira da Malam Munir Sidi a UDUS ranar 20/10//2019.
[12] Wasu ƙwararrun kuma masana ilimin kwanfuta da sadarwa ta zamani

Post a Comment

0 Comments