Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Ƙara Aure 35: Mutuwa Kan Zama Dalili

Na ga wani da ya auri wata mace Allah ya yi mata rasuwa. Bayan wasu 'yan shekaru sai ga ƙanwarta ta fito. Har ya yi niyyar ƙarawa da ita saboda tuna tsohuwar matarsa amma Allah bai yi ba. Ban dai san waye a cikinsu ransa bai gama natsuwa da ɗayan ba. Sai dai na sha jin mamaci na cewa ko bayan ba ni a ba wane...

Zan Ƙara Aure 35: Mutuwa Kan Zama Dalili

Baban Manar Alƙasamin
Zauren Markazus Sunnah

Mutum bai yi niyyar ƙara aure ba amma a dalilin mutuwar matarsa sai ka ga dalilin ƙarin auren ya samu, ko dai saboda ba zai iya zama ba mace ba, ko kuma yana ma da wata matar amma ba zai iya zama da ita ita kadai ba, dole ya ƙaro wata matar da za ta maye makwafin wace ya rasa, galibin mazan da suka saba da mata biyu ba sa iya zama da guda ɗaya saboda sirrin dake tattare da haka, wanda galibin waɗanda ba su hada mata biyu a lokaci guda ba ba su san da shi ba.
.
Da farko dai na sami labarin wata mace da aka san mai kishi ce ta matsa wa mijinta ya auro wata tsohuwar budurwarsa da ya taɓa nema, kuma ta tsaya a kan haka har jama'ar dake gefe suka san abin da ke faruwa, ashe ta yi bincike ta gano cewa har zuwa wannan lokacin akwai soyayya a tsakaninsu, amma matar ta lashi takobi ne cewa ba za ta aure shi ba matuƙar yana tare da uwargidansa, ita kuma uwargidan ta sami labarin cewa matar ba za ta taɓa haihuwa ba, kamar yadda likitoci suka bayyana ko meye dalili oho.
.
To ita kuma tana da yara biyu mace da namiji, shi ne take ƙoƙarin Alhajin ya auro matar yadda hankalinsa a ƙarshe zai ƙare ne a kan yaransa, ita dai likitoci sun bayyana cewa ba za ta jima a duniya ba, saboda mummunar  cutar"Cancer" da take dauke da shi, ta yi nasarar hada soyayyan amma ta mutu kafin auren, kuma Alhaji ya cika mata alkawarinta, sai auren da ya ƙara ya zama abin da kowa ke ƙauna a tsakaninsu su uku, kai har da marayun yaran ma da uwarsu ta bar su.
.
Da farko dai na ga yarinyar da aka sanya mata ranar aure, kafin lokacin da 'yan kwanaki Allah ya yi mata wafati, da yake uwayenta tsayayyu ne irin mutanen farkonnan haka suka jawo ƙanwar suka jefa ta a lallai a kan alƙawarin farko ba tare da sun ƙara koda kwana guda ba, ka ji Allah ba? Al-Wahhabu! Yanzu haka tana da yaranta a gaba, maganar da nake so na yi ta wani bawan Allah ne da ya auri diyar maƙwabcinsa, ba a jima ba ta rasu nan take aka ƙara ba shi ƙanwar don ta mantar da shi radaɗin rasuwar matarsa ta farko.
.
Wannan kam ba gare shi ne farau ba don kuwa diyar ma'aikin Allah SAW, wato Ruƙayya na rasuwa a dakin Usman RA, aka aura masa ƙanwarta da take shaƙiƙiyarta, ita ɗin ma da ta rasu Annabi SAW ya ce da akwai wata da ya ƙara masa, in dai zancen babba ta rasu mijinta ya auro ƙanwar ne ni na ga haka da dama, wanda yakan faru amma ba kasafai ba shi ne mutum ya mutu ƙaninsa ko wansa ya aure matar ta ci gaba da zama a gidan saboda a hana yaran jin kadaici ko maraici.

.
Shi ma ɗin dai yana da asali, don Abu-Salama RA ya rasu kuma Annabi SAW ya auri matarsa wato Ummu-Salama ya janyo 'ya'yan gaba yadda ba za su taɓa jin zafin maraici ba, uwa dai uwarsu ce, abin da duk za ta ba su daga dukiyar dan uwan mijinta ba za ta yi wani haufi ba don ba agololi ne ba, irin wannan al'ummarmu ya kamata a ce suna yi don taimaka wa karkasuwar marayun barkatai, abin takaici hakan ba ya faruwa a matattararmu in ba ga masu arziƙi ba, su ma ƙoƙarin tare dukiyar a wuri guda ya sa ake yin auren ba don tausayin yara ba.
.
Babban misali shi ne auren da na gani a wasu 'yan shekaru na kusa waɗanda kafinsu wata mata ta zuba wa maigidanta 'ya'ya manya-manya. Rana tsaka sai ta ce ga garinku nan! A daidai lokacin da ƙanwarta ita ma ta dawo gida a matsayin bazawara, ai kawai bayan karbar gaisuwar sai ta ci gaba da riƙe 'ya'yan yayarta, zuwa wani lokaci aka shigar musu da ra'ayin aure suka yarda aka ɗaura, wannan ba wata tantama ya fi sauƙi da a ce ya je waje nemo wani auren ko ya samu ko ya rasa, ƙila kuma yaran su yi ta samun rashin jituwa tsakaninsu da matar babansu tunda sun girma.
.
Na ga wani da ya auri wata mace Allah ya yi mata rasuwa. Bayan wasu 'yan shekaru sai ga ƙanwarta ta fito. Har ya yi niyyar ƙarawa da ita saboda tuna tsohuwar matarsa amma Allah bai yi ba. Ban dai san waye a cikinsu ransa bai gama natsuwa da ɗayan ba. Sai dai na sha jin mamaci na cewa ko bayan ba ni a ba wane wance, to in yarinyar ta girma sai ka ga ya ƙara da ita don cika wasiyar mamacin, yadda mutuwa take raba masoya wani sa'in tabbas takan ƙulla wata soyayyar da ba a shirya mata ba.

Post a Comment

0 Comments