Kundin Ma’aurata 35: Manufar Ita Ce...


    In dai wannan ya zama shi ne a zuciyarki to duk abin da za ki yi, za ki riƙa tunanin lahira ne ba shi ba. Tabbas namiji, kamar yadda kuke cewa, yana da wuyar sha'ani, amma ki lura ba wani abu na


    Kundin Ma’aurata 35: Manufar Ita Ce...

    Baban Manar Alƙasamin
    Zauren Markazus Sunnah

    Duk wace za ta yi aure ta fahimci cewa wani fagen fama za ta shiga mai faɗin gaske wanda a cikinsa za ta ja daga tsakaninta da shedan a kan mijinta, 'ya'yanta, 'uwayen mijin da 'yan uwansa, ta fahimci cewa dalilin halittarta gaba ɗaya don bautar Allah ne sannan zaman aure, a wannan dalilin Allah SW yake cewa "Daga cikin ayoyinsa ne ya halitta muku mata don ku sami natsuwa a wurinsu" idan ya kasance namiji bai sami natsuwa a wurin matarsa ba, to ba ta yi abin da aka halicce ta dominsa ba, ki gane cewa wannan da kike zaune da shi ba ƙarfinsa ne ya jiye ki ba, bautar Allah SW ta kawo ki.
    .
    In dai wannan ya zama shi ne a zuciyarki to duk abin da za ki yi, za ki riƙa tunanin lahira ne ba shi ba. Tabbas namiji, kamar yadda kuke cewa, yana da wuyar sha'ani, amma ki lura ba wani abu na bauta wanda yake da sauƙi. Ko da a zahirinsa kuwa yana da matuƙar sauƙin sai kin ga shedan ya yi kane-kane a wurin don ya hana ki samun aljannan da kike kwadayi, don haka ki yi ƙoƙari waɗannan abubuwan guda 4 su kasance don Allah kika yi su.
    .
    1) Babbar manufarki da auren da za ki yi ita ce bautar Allah SW, ba wani abin duniya kika yi niyyar tarawa ba, ba baƙin cikinki kika tara wanda in kin je za a yaye miki shi gaba ɗaya ba, ba nauyin uwayenki mai gidan zai dauke ba, don haka kin shirya fuskantar duk wani ƙalu-bale in dai saboda Allah ne.

    2) Wahalhalun da za ki sha a cikin gidan, na wanki da wanke-wanke, dafa abinci da tsaftace gida kacokan ɗinsa, da dawainiyar yara daga ciki zuwa tarbiyya duk saboda Allah kike yi, wani wajibi ne da ya dora a kanki kuma za ki sauke a dalilinsa ba don wani mahaluki ba, in wannan ya tabbata a zuciyarki to ba wanda zai iya hana ki isar da wajibin, koda kuwa msigidan ne.
    .
    3) Haƙurinki da kiyoshi, 'yan uwan maigida da uwayensa, maƙwabta da sauran waɗanda aure kawai ya hadaku duk saboda Allah kike yi, ba wai don maigidan yana ba ki wani abu ko zai ba ki ba duk irin wannan ƙudurin yakan sa mace ta rage tunanin cewa don maigida take yi kuma in bai gode ba ko bai nuna damuwarsa ba tana iya bari gaba daya, ba shakka a wannan gabar shedan yake tarewa har sai ya shiga tsakanin ma'aurata, mace tana da abubuwan koyi ba kadan ba a rayuwar magabata.
    .
    Khadija bnt Khuwailid, wato matar Annabi SAW, ba ta auri Annabi SAW don dukiyarsa ko don sarauta da matsayi ba, tarihi ya nuna cewa manyan mutane sun neme ta amma ta ƙi, lokacin da ta sami labarinsa a wurin bawanta wato Maisara, sannan ne ta yi kwadayin aurensa, kuma ita ɗin ce dai ta tura cewa tana da muraɗinsa, ba wannan ne abin kula ba, yadda rayuwar ta kasance a matsayinta na diyar manyan mutane kuma mai abin hannunta daidai gwargwado.
    .
    Mun ga irin biyayyar da ta yi wa Annabi SAW, koda yake ni ban sami irin tsabar soyayyar da ta wakana tsakaninta da Annabi SAW a fili kamar yadda na gani tsakanin A'ishah RA da Annabi SAW ba, amma da na duba yadda diyarta Zainab ta yi da maigidanta wurin ba shi mafaka, yadda har sarƙar mahaifiyarta ta yi amfani da ita don ƙwatar maigidanta tare da sanin cewa tabbas sarƙar za ta yi wannan aikin, ta sami tarbiyya daga mahaifiyarta, tanan za mu fahimci irin ƙaunar dake tsakanin Annabi SAW da Khadijah RA.

    .
    Wannan ba iyakarsa kenan ba, har bayan wafatin Khadijah RA ɗin Annabi SAW ya riƙa yanka dabba yana raba wa ƙawayenta, kuma sunanta sam bai bata ba a bakinsa, shi ne ɗaya matar da aka san ƙaunar Annabi SAW gare ta ya fito fili sosai take jinjina ƙaunar da Annabi SAW yake mata duk da cewa Allah SW ya canza masa wace ta fi ta, ya tabbatar mata da cewa ba a canza masa ba, kuma Khadijah RA ba ta rasu ba sai da ta aurar da diyoyinta mata guda 4 in banda Fatima RA, su ne: Zainab, Ruƙayya, Um-Kulthum da Fatima, ba wani mahaluki da zai kawo maka wata taƙaddama da aka samu tsakanin Khadijah RA da maigidanta, duk kuwa da cewa duk zama akan sami wasu 'yan matsaloli, Ƙur'ani da Hadisai sun yi maganar rayuwar Annabi SAW da sauran matan, har da zancen zabin saki da sauransu.
    .
    Idan muka koma tarihi za mu ga irin tsabagen ƙoƙarin da Khadijah RA ta yi na taimakon mijinta wurin ganin ya isar da saƙon da Allah SW ya aiko shi da shi, wasu malamai suna  ganin ita ce mutum na farko da ya fara karbar muslunci a bayan ƙasa, ta yi matuƙar ƙoƙarin da za ta iya wajen ganin ta kwantar wa Annabi SAW da hankali a lokacin da ya fara ganin mala'ika Jibril AS, ta riƙa gaya masa maganganu masu daɗi na tabbacin cewa Allah SW ba zai wulaƙanta shi ba, ita ɗaya jal ta rayu da Annabi SAW ba kishiya har tsawon shekara Ishirin da doriya RA.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.