Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Ƙara Aure 36: Maƙwabta

Soyayya ta shiga tsakanin ma'aikata a gida guda ko ofis, wannan ba sabon abu ba ne. In dai kai na yawo sanda na yawo wata rana tabbas za a haɗu. Ina koyarwa a wata makaranta ta Mishon a shekarun baya, nan ne na ga wani abin al'ajabi wanda ban saba ganin sa a wannan wurin ba. Wani yaro ne ya yi rashin ji. Malamar ta dake shi da rula a kai. Kamar wasa sai ga yaro ya...


Zan Ƙara Aure 36: Maƙwabta

Baban Manar Alƙasamin
Zauren Markazus Sunnah

Ɗaya daga cikin manyan dalilan ƙarin aure da ya kamata a ce mun kawo shi tun a farko shi ne maƙwabtaka, ba shakka takan taka mahimmiyar rawa wurin ƙarin aure, kodai ga-gida-ga-gida, yadda yara suke tasowa tare, ko yarinya tana gilmawa har wani magidanci ya ga tarbiyyarta ya yi sha'awa, wani kan ce tsayuwar ubanta wurin tarbiyantar da ita ta sa ya ƙyasa, amma idan kullum za ta sha ado ta gilma ta gabansa, kuma ya san komai nata na hali da dabi'a a dalilin zama wuri guda, ga sanayyar uwaye da sauransu tabbas wannan zai iya shiga zuciyarsa ya ga cewa ya dace a ce ya ƙara aurennan da ita.

To ba kusantakar gida kawai ba akwai ma ta wurin aiki ko sana'a, wani sa'i in ka bincika waɗanda ke da sana'a iri guda in dai ba a gidansa ta yi karatun har ta sami aikin ba za ka taras cewa zarafin aikin ne silar haduwarsu, koda kuwa tsakanin malami ne da dalibai, ba a jima ba wata yarinya da take zuwa wurin babanta duk in ta taso aji kafin ta kama hanyar gida wani ma'aikacinsa ya ƙyasa kuma Allah ya sa da rabonsa yanzu haka tana dakinsa, kusantakarsa da mahaifin yarinyar yana ganinta kullum har ya fara karantarta har dai aka kai ga ya dan fara tuntuba ƙila ma in da rabo yanzu suna da yara.
.
Wanda duk ya fi ba ni sha'awa shi ne direban Alhaji, direban ma na manyan motoci ba ƙanana da zai riƙa kai yara makaranta ba, ban san ta yadda suka hadu ba, amma tabbas shi ya iya tsayawa nemanta ba tare da tsoron abin da zai biyowa baya ba, ko ya sami matsala a tsakiyar tafiyar ban sani ba, amma har yanzu shi yake jan daya daga cikin manyan motocinsa, kuma matarsa tana dakinsa, har ta gama karatunta ubanta yake daukar nauyinta.
.
Maƙwabtakar direba da Alhaji ta ba shi damar ganin yarinyar, to wanda ya so ƙarin aure ma da haka zai gani, don mun zauna da wani bawan Allah a shekarun baya daki guda, wata maƙwabciyarmu kullum sai ta zo gaishe shi, ko muna da yawa shi kadai take kama sunansa, wani lokacin ma har abinci take dafawa ta kawo mana amma da sunansa, kai har na ƙare na fara gaya masa cewa wance fa kyarkyara take yi, don ba ƙira ba abin da zai ci gawayi, shi kuma yana fada min irin zaman mutuncin da suka yi da uwayenta, ya ce girmamawa ce kawai, a maganar da muke yi da kai tana da yara da shi.
.
Na ga wace take son wani mutum shi kuma bai damu da ita ba, har matarsa ta san cewa lallai maƙwabciyarsu dinnan tana son mijinta, sai ta fara tura mata magana, wannan ya sa yarinyar ta fito gar da gar ta fara nemo wa kanta mafita, in ta hadu da matarsa sai ta riga ta magana "Kin san cewa ina son mijinki, wallahi duk abin da zai yi kallonsa kawai nake yi amma sai na aure shi, ki je kuma ki gaya masa" ita kuma ta mayar mata da mai zafi, duk da haka sai da ta aure shi a ƙarshe.
.
Soyayya ta shiga tsakanin ma'aikata a gida guda ko ofis, wannan ba sabon abu ba ne. In dai kai na yawo sanda na yawo wata rana tabbas za a haɗu. Ina koyarwa a wata makaranta ta Mishon a shekarun baya, nan ne na ga wani abin al'ajabi wanda ban saba ganin sa a wannan wurin ba. Wani yaro ne ya yi rashin ji. Malamar ta dake shi da rula a kai. Kamar wasa sai ga yaro ya fara zufa, sai zazzabi sai mutuwa ta nan take, ashe uban Babban alƙalan ƙasa ne, uwar kuma babbar lauya ce haka yaransu gaba daya, shi da ita wurin aiki ya hada aurensu.
.
Kafin ka ce haka lauyoyi da manyan mutane sun cika makarantar, wasu har sun fara fadin a kama malamar da shugaban makarantar, da me aka yi dukar? Duk da an gani amma suka fara fadin kisar ganganci ce tunda aka yi duka a makisa, abin dai nasu ne can, uwar ta sha alwashin sai an yi wa danta adalci, uban na shigowa ya kashe maganar, ta yadda ya tura matarsa gida da sauran yaransa gaba daya, ya sa aka tafi da mamacin a ƙarshe ya kulle maganar ya ce kar a sake dago ta, abin kula dai a ciki ya hadu da matarsa ne ta wurin haduwar wurin aiki iri guda.
.
Na sha ganin 'yan siyasa suna ƙarin aure a dalilin cin zabe, idan ya kasance matansu na gida ba za su iya shige da fice irin yadda ake buƙata a duniyar siyasar ba, sai ka ga mutum ya samo wata da ta jima tana gwagwarmaya a fagen, sai dai ka ji an ce ya ƙara aure, akwai wani tsohon gwamna, da tsohon shugaban ƙasa da muka ga irin wannan tare da su, zama wuri daya ko zarafin aiki iri daya kan zama babban dalili na ƙarin aure.

Post a Comment

0 Comments