Kundin Ma’aurata 33: Ka Yi Addu’a Kawai


    Na ga wata da take yi wa mijin duk laɗabin da yake buƙata, kuma sam ba za ka ga wani nata a gidan ba bare ka ce kaza da kaza. Ana yaba mata rashin kwaɗayi da kamun kai, sai dai ba nan gizo yake saƙarsa ba. Yaran nata kab ɗinsu ba mai ɗabi'u na ƙwarai. Tun suna ƙanana ba wanda ya isa ya taɓe su ko ya ce zai aike su. A taƙaice dai ba tsayayyiyar uwa ba ce. Yaran nan kowa da ɗabi'unsa. Sam ba su biyo halin uban ba. Duk da haka lalacewar na gaban bai sa ta yi la'asar ta gane inda ake fuskanta ba. Ba a je ko'ina ba uban yaran yana ji yana gani sun fi ƙarfinsa...


    Kundin Ma’aurata 33: Ka Yi Addu’a Kawai

    Baban Manar Alƙasim
    Zauren Markazus Sunna

    Aure wata jami'a ce, kamar yadda muka sani a baya, mai rassa daban-daban, kowani reshe da abin da yake koyarwa, ka ga matannan da za ka auro, ka roƙi Allah SW kawai ya ba ka ikon mallakarta gaba daya, amma ba wayonka ko iya zabinka ba, na ga wani dattijo da ya auro wata matashiya, kullum wani fegi na bala'i ake budewa a cikin gidansa, har sai da zaman gidan ya gagare shi, banda baƙaƙen maganganu da muguwar fata gami da raina masa hankali da arziƙi a gaban sauran 'ya'yansa ba abin take yi, abin da ban sani ba muguwar ƙauna ce ta maƙure shi ko tsabagen haƙuri ne, Allah ne masani, ba abin da yake yi sai dai ya fito ƙofar gida ya kama ƙofar ya yi jungum kamar wanda aka yi masa mutuwa.
    .
    Na ga waɗanda suna cikin zaman-zamansu da  iyalinsu allurar ƙara aure ta soke su, suka ta shi suka yo amare, wallahi sai da suka sayar da kadarorinsu ciki har da gidajensu suka kama haya da kudin, duk dai a dalilin matansu, akwai wace ta sa aka kori mijin a wajen aiki, kuma ba ta da niyyar rabuwa da shi, wata kuwa raba shi da 'yan uwansa ta yi gaba daya, don yana da dan abin hannunsa, ta damƙa masa nata ya riƙe su hannu bibbiyu, kullum sai ya yi musu goma na arziƙi, a ƙarshe ta kwaso 'yan uwanta da danginta suka tare a gidansa, ba wani dan uwansa da ya isa ya tafi gidan, ta yanke duk wata alaƙa a tsakaninsu.
    .
    Wata kuwa ba ta shiga gidan ba sai da ta saka shi ya rabu da uwar 'ya'yansa, ta raba shi da abokansa, a ƙarshe ta dauke shi daga gaban uwayensa ta yi kudu da shi, sai yadda ta so za a yi, wai kuma shi ne maigidan, abin takaicin a duk waɗannan jarabawoyin da nake gaya maka ba kwadayi ya kai mazajen ba, wallahi ƙaddara ce kawai, don sun fi matan nasu komai da ka sani amma sai yadda matan suka yi da su, ka ga kenan akwai buƙatar roƙon Allah SW ya ba ka mata ta gari kawai.
    .
    Na ga wata da take yi wa mijin duk laɗabin da yake buƙata, kuma sam ba za ka ga wani nata a gidan ba bare ka ce kaza da kaza. Ana yaba mata rashin kwaɗayi da kamun kai, sai dai ba nan gizo yake saƙarsa ba. Yaran nata kab ɗinsu ba mai ɗabi'u na ƙwarai. Tun suna ƙanana ba wanda ya isa ya taɓe su ko ya ce zai aike su. A taƙaice dai ba tsayayyiyar uwa ba ce. Yaran nan kowa da ɗabi'unsa. Sam ba su biyo halin uban ba. Duk da haka lalacewar na gaban bai sa ta yi la'asar ta gane inda ake fuskanta ba. Ba a je ko'ina ba uban yaran yana ji yana gani sun fi ƙarfinsa.
    .
    Wata kuwa tausayi ne ba ta da shi. Zai yi wahala ka ga ta adana wani abin da maigidan zai shigo da shi, ba kwashewa take yi ta kai wani wuri ba, amma sam ba ta damu ne da tattali da adani ba, komai ya shigo da shi sai an lalata, ba za ta tsawata ba, in wani abinci ya kawo wanda in aka ririta shi zai iya kai su wata guda suna gurzarsa, to a kwana uku za su gama da shi, in ya ba da shawarar a gwada yin amfani da wani abu sai ta ce matsayinsu ya wucenan, kuma ba za a yi ɗin ba bare ya samu ya huta.
    .
    Akwai ballagaza, tana da mijinta na aure wanda ya aure ta tana budurwa, amma 'ya'yanta hudu kowa ubansa daban, abin da zai ba ka mamaki mijin nata yana sane da duk abin da take yi, amma bai rabu da ita ba, a lokacin da nake magana da maƙwabtansa na ce "Amma fa duk da haka in ya san cewa yarannan ba nasa ba ne zai iya koranta a gidan" suka ce "Wallahi yana sane da haka" na ce "Kamar ya?" Suka ce ai an sha tabka rikici akan haka, kuma shi ɗin ya san uban kowa in ba wanda Inyamuri ya yi cikinsa ba" kai hatta hanyar da kwartayen suke shiga gidan ya sani, amma yana zaune da matar, na ce zuciyarsa ta mutu.
    .
    Wata kuwa tana da halayenta na ƙwarai sai dai ba ta zaman gida, ba zinace-zinace take yi ba, amma ba za ta taba zama a dakinta ba, kullum cikin nemo masa rigima, yana fita za ta sa ƙafa ita ma ta shiga maƙwabta, bai da aiki sai yi mata kashedi, amma bai iya tsinana komai ba, in 'yan uwansa sun janyo hankakinsa ya yi kamar zai dauki mataki, yana komawa gida suka yi ido hudu da shi ba ka sake jin wani abu, tamfar an aiki bawa garinsu.
    .
    To idan ka fi mace komai ciki har da shekaru da kudi da ilimi gami da wayewa amma sai abin da ta yi, ya kake gani in ta dara ka komai? Shi ya sa muke cewa in kana da kyau ka ƙara da wanka kawai, sau nawa muke ganin malamai suna wa'azi a waje matansu suna kware musu sutura, in zama ka yi wurin matasa nan za ka ji wasu suna fadin ma-sha'an da suke yi da matan masu kudi ko milki, hatta naganganun shaye-shayennan wallahi ba a bar su a baya ba, wata fitinarma bana mafiyawancin 'yan mata sun ajiye hijabi sun dauko gyalulluka, na fadi wannan maganar wani ya ce wallahi har da matan aure, don haka bari na komo kanki kawai.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.