Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Ƙara Aure 32: Kafar Sadarwa


Wani sa'in ko unguwarku ɗaya da mace ba dole ba ne ka san ainihin haƙiƙanin kalar jikinta, bare kuma a ce ba gari guda ba. Matan na kallon ma'aunin da muke auna su da shi ne. Da a ce muna kallon kyawun hali ne sama da hasken jiki, to da ba yadda za a yi su riƙa kashe kuɗinsu wajen gyaran jiki. Na taɓa jin wanda ya ce Allah ya ba shi farar mace ko ya take. Ganin irin wannan fahimtar ya sa mata suke ƙoƙarin komawa farare, ko da kuwa duk mazan baƙaƙe ne. Duk wani aure da za a ɗaura ka kalli mijin da matar....


Zan Ƙara Aure 32: Kafar Sadarwa

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Za mu iya cewa hanyar salula hanya ce ta ƙarin aure amma ba ta isa ta zama ingantacciyar hanya ita kaɗai ba. Akwai abubuwa guda biyu da ake la'akari da su wurin zabin mace, wato kyawun ɓoye da na sarari. Kowa na fatar na ɓoyen ne. Su kuma suna iya nuna na sararin ne kawai. Shi ma ɗin duk an yi coge a ciki. Duk kyakkyawar da za ka gani a kafofin sadarwa rabi ba gaskiya ba ne. Maɗi ake wa talla ba zuma ba. Wannan ya sa maza suka fara ɗari-ɗari da zaɓin mace a kallo ɗaya, masamman na ranar salla ko wani biki ko suna. Idan mace ta sami dilka mai kyau irin na mutanen Borno ɗin nan sai ka rantse da Allah fara ce sal, ashe a-cuci maza ta yi.

Wani sa'in ko unguwarku ɗaya da mace ba dole ba ne ka san ainihin haƙiƙanin kalar jikinta, bare kuma a ce ba gari guda ba. Matan na kallon ma'aunin da muke auna su da shi ne. Da a ce muna kallon kyawun hali ne sama da hasken jiki, to da ba yadda za a yi su riƙa kashe kuɗinsu wajen gyaran jiki. Na taɓa jin wanda ya ce Allah ya ba shi farar mace ko ya take. Ganin irin wannan fahimtar ya sa mata suke ƙoƙarin komawa farare, ko da kuwa duk mazan baƙaƙe ne. Duk wani aure da za a ɗaura ka kalli mijin da matar.

To ya batun hotunan da ake liƙawa a kafofin sadarwa na zamani don neman dace da wanda za a aura? A nan akwai mahangu guda biyu waɗanda galibi su aka saba da su:

a) Mahangar addini wacce ita kullum laluɓen abubuwan da sharia ta gindaya take yi. Ta halasta na ƙwarai ta haramta na banza ko da kuwa yawacimmu muna jin daɗinsa ko kuma muna ganin kyawunsa, masamman bayyana ado na ƙarshe har ta kai ga nuna abubuwan da za su tayar da sha'awa ba tare da damuwa da abin da zai biyo baya ba.

b) Mahangar al'ada, wacce ita kuma ta fi karkata ne zuwa ga abubuwan da aka saba tun tale-tale ko aka gada iyaye da kakanni har zuwa yanzu. Galibi ana auna kyawun abin ne ko muninsa da al'ada da kuma hankali. In bai saɓa musu ba to yana da kyau. Mu Hausawa waɗanda galibimmu Musulmai ne al'adarmu na tafiya da addini ne. In ta saɓa masa to dole ne a yi watsi da ita a riƙi addinin. Shin za mu ce neman aure a kafofin sadarwa ya dace? In muka duba bayanan sama za mu fahimci cewa in dai ba za a yi bincike ba, to za a iya zaɓo tumun dare. Hakan kuma bai dace ba.

Na yi zamani da wacce ta ce min ta san wani da ke hanyar gidansu wanda ya fara nemanta. Sai da suka saba da juna ta san cewa manemin mata ne. Wata ma ana dab da ɗaura aure ta fahimci cewa ba namiji ba ne. Ta fasa auren. Ta yi bincike ke nan. Wata kuwa an ɗaura auren amma makonta guda ta fito. Ita ma matsalar rashin mazantaka ce. Wata ta ce baƙin mugu ne. Ba za ta iya zama da shi ba. Wata tana so ne ta sani in za ta iya rabuwa da shi, ƙazami ne. Wata tana kukar fitina ne a shinfida. Duka dai za ka taras matsalar rashin bincike ce.

To kamar wanda zai ga hoton mace a WhatsApp ko Facebook ya ji kawai ya kamu da sonta, har ma ya gaya mata cewa shi fa wallahi yana jin in bai aure ta ba rayuwarsa sam ba ta da amfani... Irin wannan in ta yarda gaskiya ta ga dama ne, domin sha'awarta yake ji. Bai ga surarta a zahiri ba. Wato lafiyarta lau ko tana da naƙasu, haskenta na shafe-shafe ko ma na'ura ce ta ƙara mata? Wata ma ƙila ta yi gyarar fata ne! Sannan ɗabi'u da addini waɗanda tun asali su ne manyan dalilan da suke sa mutum ya so mace za ka taras ba abin da ya sani a ciki. Ta yaya za ki karɓi cewa ƙaunar gaskiya ce ba sha'awa ba?

Sha'awa lokaci ɗaya tal take shiga, kuma mutum kan iya yin komai a dalilinta. Kafofin sadarwa kaf ɗinsu tallanta ta suke yi. Mu maza sai su tallata mana kyau. Mata kuma a tallata musu wadata. In na sha shadda mai mugun tsada ta sha aiki sai na jingina da babbar mota a gaban wani tsararren gida ga waya mai mugun tsada a hannuna na ɗauki hoto na turo kafofin sadarwa. Da mace ta gani sai ta ce wannan wankan na manya ne. Cikin sauƙi abubuwa za su gyaru.

An yi haka barkatai! Ina son na ce kafofin sadarwa a yau su ne a sahun farko wajen sada ma'aurata masu ƙoƙarin yin auren fari ko ƙarawa. A nan ba cewa muke halas ko haram ba. Muna nuna cewa sun zama hanyar da ma'aurata suke bi a yau wajen tabbatar da aurensu ya ɗauru. Na san ma'aurata da dama waɗanda kafofin sadarwa suka haɗa su. Wasu daga nisan duniya, wasu a kusa. Akwai wata Ba'amurkiya da ta so ɗan Somaliya kuma ta aure shi ta wannan hanyar. Akwai kuma wani Ba'amurke da ya haɗu da wata a Iraƙi ta hanyar kuma ya aure ta. To bare a Nijeria daga Borno zuwa Legas!

Post a Comment

0 Comments