Ticker

6/recent/ticker-posts

Kundin Ma’aurata 30: Bayan Abinci

Tun da akwai masu ganin ya dace a koyar da ilimin da masu ganin cewa  ƙofar ɓarna ake so a buɗe, ina ganin ya kamata a shiga tsakiya. Kar a riƙa koyar da ilimin kamar yadda Yamma suke buƙata saboda saɓa addini da al'ada da abin ya yi. To amma in aka kusa kai ta ɗakinta, ya kamata a nuna mata baƙi da fari don ta  ƙarisa idonta a bude. A kuma sami waɗanda za su riƙa bincikar yarinya don gudun aukawa matsala. Su ma mazan in har ba su sani ba to su nema. Don in aka sami matsala suna iya yin asarar matan in har suka ce ba za su koma gidajensu ba. Gaskiya ne maganar dabbobi ma suna yi, amma ai a gaban yaransu suke yi yaran suna kallon komai, saɓanin ɗan’adam da Allah ya...


Kundin Ma’aurata 30: Bayan Abinci

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Sai kuma bayanin shimfiɗa, don ɗan’adam da zarar ya  ƙoshi kuma sai tunanin biyan bu ƙata. Babban abin da malamammu ba sa son yin magana a kai kenan. Ko dai saboda  ƙyamar yin hakan ko kuma tsoron abin da zai iya aukuwa in mutane kamarsu suna taɓa wannan batun. Sai dai tsakani da Allah jama'armu suna da bu ƙatarsa. Don kuwa ana tabka shirme ba kaɗan ba a wagga harka. Ni dai zan faɗo wasu abubuwa guda uku waɗanda a gabana abubuwan suka faru ba labari aka ba ni ba. Kowa kuma da irin abin da ya shaida.

1) Wani saurayi da muka yi aiki da shi tare na tsawon lokaci ya bayyana mana cewa shi kam zai yi aure. To bayan sha'anin bikin da kusan wata shida sai ya fara kawo min kukan cewa iyalinsa fa ko ɓatar wata ba ta taɓa yi ba... Anya za su haihu ma kuwa? Tun da na ji ya furta haka na fahimci yana bu ƙatar a lallaɓa shi don sabon shiga ne. Na ba shi labarin wani dattijo da ya faɗa min cewa sai bayan shekara 8 sannan ya sami haihuwa. Wata ɗalibata ma ta ce sai bayan shekara 15 sannan ta sami cikin 'yar 'yatta  ƙwara ɗaya jal. Amma shi ma ya yi haƙuri don wata 6 ai ba wani lokaci ne mai tsawo ba.

Da hira ta ja sai na fahimci gaskiya duk tsawon lokacinnan guga ba ta san katamaiman hanyar rijiyar ba. Irin kukan da yarinyar take masa da yadda ya sheda min na fahimci haka. Na tsaya na yi masa gamsasshen bayani da yadda kuma zai riƙa yin amfani da man Vaseline Blue Seal. To da yake ba maganar yi ba ce ba mu sake tattauna ta ba. Sai bayan wata uku yake shaida min cewa sun je gwaji an ce iyalinsa tana da juna biyu wara 3. A lokacin ne yake yi min godiyar hasken da na ba shi. A ta ƙaice dukansu biyu ba wanda ya san yadda abin yake. Alal a ƙalla abin farinciki ne tun da ba su yi lalata a waje ba, sai dai matar ta cutu na ɗan wani lokaci.

Na ce, a baya an yi wani zamani wanda har yanzu a karkara ana yi, yadda bayan yarinya ta tare da kwana ɗaya jal wata daga gidansu za ta bi ta ta ji halin da take ciki. Kuma ta san irin shawarwarin da za ta ba ta. Wata sai an yi mata gashi. Wata kuma ababan shafawa kaɗai za a ba ta gami da 'yan shawarwarin yadda za ta kula da kanta. Waɗannan abubuwa ne masu kyau. In dai uwayen yanzu za su ci gaba da irin wannan tadar da wahala a sami matsala a tsakanin ma'aurata a kan abin da ya shafi shimfiɗa. Na ce, ko wancan abokin nawa da a ce uwayen sun leƙa yarinyar da ba a kai haka tana jin jiki ba. Ga maigidanta ya kusa ya kai ta ya baro.

Na taɓa samun wasu matsaloli guda biyu waɗanda dukansu sai da aka raba auren. Su ma ɗin duk dai suna da alaƙa da rashin bincikawar uwaye, har cutuwar  ɗiyoyin nasu ta bayyana a fuskokinsu yadda suka riƙa lalacewa, suna ramewa a banza. Guda dai ashe maigidan ba namiji ne sosai ba. To da yake yarinya ce  ƙarama, ba ta san kan abin ba sai yana sanya mata babbar yatsa kamar yadda ta faɗa. Da haka infections suka yi mata kamun kazar kuku. Ganin canjawarta ne uwayen suka bincika suka gano haka. Suka tsaya sai da aka raba auren.

Ɗayar kuwa maigidan bai daga mata  ƙafa ne gaba ɗaya. Ba dare ba rana! Ga ta yarinya  ƙarama. Inda abin yake da muni shi ne; ko tana al'ada bai san haramci ba. Duk wanda yake da masaniya a kai ya san mata suna shan wahala in za a sadu da su a wannan lokacin, saboda wurin kan danyata kuma akan sami rashin ruwan yauƙi wanda yake sauƙaƙa gogayya gaba ɗaya, sannan akwai sauƙin kamuwa da infection ɗin. Haka ita ma ta fara cutar mara mai tsanani har aka san abin da take ciki. A  ƙarshe ta ce ba ta ba shi.

Ita kuwa wannan abokiyar aikina ce a wani wuri. Da yake ta girma ta san ciwon kanta, ana saura 'yan satuttuka ta same ni a keɓe ta ce na koya mata wasu abubuwan. Na ce ta tambayi mahaifiyarta. Ta ce ai mahaifiyar ta ce mata "Dabbobi ma da suke yi ba wanda ya koya musu!" Na ɗan yi mata bayani sama-sama saboda saɓanin jinsi dake tsakaninmu. Ta yi min godiya ba 'yar  ƙarama ba.

3) Ta ukun ma 'yan shawarwari na ba ta kuma ita ma bayan auren ta yi ta godiya da nuna jin daɗinta. Ta ce an yi ta ba ta tsoro, amma da na kwantar mata da hankali sai ta ga ya ma fi yadda na yi mata baya ni sauƙi. Yanzu akwai littafai amma su ma a kula da lokacin da za a karanta su.

Shawarata

Tun da akwai masu ganin ya dace a koyar da ilimin da masu ganin cewa  ƙofar ɓarna ake so a buɗe, ina ganin ya kamata a shiga tsakiya. Kar a riƙa koyar da ilimin kamar yadda Yamma suke buƙata saboda saɓa addini da al'ada da abin ya yi. To amma in aka kusa kai ta ɗakinta, ya kamata a nuna mata baƙi da fari don ta  ƙarisa idonta a bude. A kuma sami waɗanda za su riƙa bincikar yarinya don gudun aukawa matsala. Su ma mazan in har ba su sani ba to su nema. Don in aka sami matsala suna iya yin asarar matan in har suka ce ba za su koma gidajensu ba. Gaskiya ne maganar dabbobi ma suna yi, amma ai a gaban yaransu suke yi yaran suna kallon komai, saɓanin ɗan’adam da Allah ya suturta shi. Akoya wa kowa kawai. Allah ya ganar da mu daidai.

Post a Comment

0 Comments