Ba na gardamar cewa wasu
matan in suka yi arziƙi sukan nemi wani dan tagaje-tagajen namiji
don su sami damar yin abin da suke so ba tare da takura ba. Ko kuma shi kansa su riƙa juya shi yadda suke so. Sau ɗaya dai
na taɓa jin wata mata wai ta yi wa wata attajira maganar
banza. Ta kira ta da wani suna wanda bai mata daɗi ba. Don haka ta yi amfani da
kuɗinta ta aure mata miji kuma ta kore ta! Wannan bai cika faruwa ba,
amma abin da muke ƙoƙarin fitarwa anan shi ne, za a iya samun
mutum da iyalinsa bai da niyyar ƙara aure sai wata mace ta fito masa ta hanyar
da take ganin za ta ci nasara kuma ta....
Zan Ƙara Aure 28: Wata Kan Zama Dalili
Baban Manar Alƙasim
Zauren
Markazus Sunnah
Tarihi bai dauko mana cewa
Khadija RA ta yi sha'awar Annabi SAW ne ya sa ta nemi ya yi kasuwanci a cikin
dukiyarta don ta sami silar da za ta janyo shi kusa da ita ba, a zahiri mun ga
cewa amanarsa da wasu alamu da aka gaya mata cewa an gani tare da shi su suka
ja hankalinta, kuma ta yi dace da samun fiyayyen halitta, haka a yau akan sami
masu hali da suke ganin mutumin kirki sai su yi sha'awar a ce ya zama
maigidansu ba don suna sa rai da zai iya ba su wani abin duniya ba, tsabar
natsuwarsa ce da hankalinsa, ko kuma ilimi ko wata halitta da suke matuƙar buƙata kuma suka tsince ta
tare da shi.
.
Ko anan ƙasar ma na san matan da
suka ɗauki malamai don su koyar
da su a ƙarshe suka aure malaman don ganin ƙimarsu da hankalinsu,
wannan kam ya faru, na taba zuwa wurin wani mai faci ban same shi ba, nan ne
ake ba da labarin cewa wata mata kusan duk kwana biyu za ta zo faci ko ƙarin iska, a ƙarshe dai ta aure shi ta
raba shi da sana'ar, ya zama babban mutum sai fantamawarsa yake yi, ita tana
cikin farin ciki cewa ta sami mijin aure, ba kudinsa ta gani ba bare a ce tana
nadama ashe bai da komai, har wurin sana'arsa ta bi shi ta dauko shi.
.
Na kuma taba ganin wani
mutum ban san inda ya san ni ba, amma ya same ni shi da matarsa a mota, hajiya
ce, ta yaba wa hankalinsa ta aure shi, sai hayayyafa take ta yi masa, a lokacin
sun zo wurina ne wai tana son ta tura shi karatu waje, na gaya musu gaskiya ba
aikina ba ne ban ma san yadda ake yi ba, ka san mu da son jin ƙwab, na ce duk yaran da na
gani a mota nasu ne? Ya tabbatar min da cewa ita ta haifa masa, kuma tana
bala'in son sa, na ce me ya sa to take ƙoƙarin tura shi waje? Ya ce ai in ya tafi ne
zai sami dalilin da zai dauko su, Inyamura ce amma ta san abinda take yi sosai.
.
To duk irin wadannan in ka
tattara sai ka taras ƙila mutum ma yana da aure, wata ta fito masa
kuma ta ce ba ta son kowa sai shi, a ƙarshe kuma ta aure shi, kenan tsayuwarta da
amfani da damarta ya zama dalilin ƙara aure kenan, mun karanta tarihi inda wata
ta ta zo fadar Annabi SAW ta ce masa ta ba shi kanta ya aura, yana da matansa,
amma da ta tsaya ƙyam a ƙarshe dai auren an yi bayan wani dan lokaci, ta auri wani can
daban amma zuciyarta tana tare da Annabi SAW, kuma sai da ya ƙara auren da ita.
.
Na ga wace ta tsaya wa
wani ubangidanta tana masa komai, da wanda ya shafi ofis da ma wanda bai shafa
ba, kuma ta shahara da kamun kai kamar dai yadda maigidan nata yake, ashe
aurensa take so, duk wani abu da ya shafe shi sai ta yi maza ta amshe, yana da
iyalinsa da komai bai ma da tunanin aure, amma a hankali ta yi masa allura ta
wurin ƙanƙan da kai ga ladabi, ai bayan wani dan lokaci sai kawai muka ji
cewa ya yaba da hankalinta har ma ya
tafi wurin mahaifa sun amince masa da fito kawai, sai mu'amallarta da
shi ta zama dalilin ƙara aurensa.
.
Ba na gardamar cewa wasu
matan in suka yi arziƙi sukan nemi wani dan tagaje-tagajen namiji
don su sami damar yin abin da suke so ba tare da takura ba. Ko kuma shi kansa su riƙa juya shi yadda suke so. Sau ɗaya dai
na taɓa jin wata mata wai ta yi wa wata attajira maganar
banza. Ta kira ta da wani suna wanda bai mata daɗi ba. Don haka ta yi amfani da
kuɗinta ta aure mata miji kuma ta kore ta! Wannan bai cika faruwa ba,
amma abin da muke ƙoƙarin fitarwa anan shi ne, za a iya samun
mutum da iyalinsa bai da niyyar ƙara aure sai wata mace ta fito masa ta hanyar
da take ganin za ta ci nasara kuma ta aure shi din.
.
Na dai sami wasu da suke
aiki tare, kullum tana kawo masa kukan matsalolin rayuwa tsakaninta da
maigidanta, shi ne yake ƙoƙarin sulhunta su, ko me ya faru oho, auren ya
baci kuma sun auri junansu, ƙila ta amince da shi ne bisa maganganunsa da
yadda yake ƙoƙarin sulhunta su din, da tsammanin samun sauƙi sama da tsohon mijinta
wanda ya yi ta shiga tsakaninsu, da farko bai da niyyar aure, amma yanayin yadda
ta tsaya a kansa da buƙatun sai ta aure shi ɗin ya sa ya yanke hukuncin
auren nata, komai na iya zama babban dalilin da zai sa maigida ya buƙaci ƙarin aure.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.