Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Qara Aure // 22: Idan ta yi Maka Kaɗan



Sau ɗaya na taɓa ganin namijin da ko zaman gidan ba ya yuwuwa masa a dalilin matar. Mabuƙaciya ce ta inna-naha, kuma ba ruwanta da dare ko safe. Da ma yaranta suna da iyaka a gidan. Sam ba ta bari su kusanci turakar mahaifin...

Zan Qara Aure // 22: Idan ta yi Maka Kaɗan
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Yadda Allah SW ya halicce mu da sifofi daban-daban, ya karkasa buƙatumu ya ba wa kowa nasa, haka ma lafiyar jiki kowa da irin tasa, gwargwadon ƙarfin halin mutum da himmarsa ke sanyawa ya ƙara aure, wani ya yi biyu wani uku, amma ba wai don ya sami abin duniya ba, domin in wadata ce ke sanya mutum ya ƙara ba shakka masu kuɗi ne ya kamata su fi kowa tara yawan mata, abin mamaki sun fi kowa auren mata guda-guda, idan ka bincika da kyau za ka taras cewa tabbas ba su da buƙatar ƙarin auren ne.

Shi kuwa mutumin karkara yana motsa jiki, ko ba aikin gona ba na sana'a zai taka a ƙafa zuwa duk inda yake so, sannan komai zai ci za ka taras abince ne nagartacce mai ƙara kuzari da lafiya, ga shi yana motsa jiki koda wani lokaci, bai yawan ta'amuli da abincin gwangwani wanda aka cika shi da sinadarai barkatai, dole ne in ya ci ya ƙoshi ya buƙaci shimfidarsa, ba kamar mutanen maraya da sanyin AC, firinji ko zaƙi ya yi musu illa ba, kar ka yi mamaki in ba su buƙaci ƙarin aure ba.

A daidai wannan gabar muna ƙoƙari ne mu nuna cewa buƙatar namiji da shimfida babban dalili ne da zai sa ya buƙaci ƙarin aure, wani mata biyu wani fiye, ina da masaniya da wasu abubuwa guda uku waɗanda dukansu a kusa da ni suka faru, kai da jin labarurrukan ka san zama da mace dayan akwai matsala, na farko a kotun ƙauyenmu na tsinci labarin, sannan ina ƙarami ban gane sahihin abinda ya faru ba sai da na girma.

Wato mace ce ta kawo mijinta ƙara kotu kan cewa yana zaga ta fiye da goma a kowace rana, ita kuma a dabi'arta ba za ta iya daukar hakan ba, alƙali ya shigo tsakiya yana rarrashi da ban-baki kamar yadda mijin ya nema, a zama na uku aka yanke  hukuncin cewa zai riƙa zagawa sau shida ne kacal a rana, mijin na ta roƙo har yana kuka a ƙara ya kai 8, ka ji abu kamar wasan kwaikwayo, aka ce ya ƙara aure, ya ce ba macen da za ta zauna da shi, gaskiya kusan hakan ne in dai ba ya yi dace da irinsa ne ba.

Na biyu kuma a Sudan ya faru, da yake wasu ƙasashen na Larabawa ko don kaciyar da ake wa mata ne da suke rede mata gabanta yadda ba za su buƙaci namiji ba oho.

Bisa nazari da wahala auren mutum biyu ya yi ƙarko, wato mai nacewa shimfida kowani lokaci da wanda bai iya ba wa shimfidar haƙƙinta, wanda duk mace ɗaya ta yi masa ƙaranci, to auren mata 4 babban riga-kafi ne na samun zama lafiya, duk ƙamari dai matansa ne, sannan in ya kwana biyu a gida ɗaya sai ya kwana 6 kafin ya sake dawowa, ka ga ƙila a daidaita, su kansu matan in suka ga ba dama da kansu za su nemi ya koma wani gidan.

Sau ɗaya na taɓa ganin namijin da ko zaman gidan ba ya yuwuwa masa a dalilin matar. Mabuƙaciya ce ta inna-naha, kuma ba ruwanta da dare ko safe. Da ma yaranta suna da iyaka a gidan. Sam ba ta bari su kusanci turakar mahaifin. A irin wannan hali shi ma dole ya ƙara aure don ya sami wurin hutawa, bai yuwawa a ce kai da gidanka amma zamansa ya gagare ka, in ya ce zai ƙara aure tabbas zai yi fama da uwargidar amma ba wata mafita in ba hakan ba.

Post a Comment

0 Comments