Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Qara Aure // 10: Ka Fahimce Ta



Wannan hukuncin ko a wurinmu maza ya yi tsauri da yawa. Kowa sai guna-guni yake yi amma ba zai iya yin magana ba tunda ba da shi ake yi ba. Duk da haka macen da take kusa da ni sai da ta ce "Amma kai ma tunda ta ba ka haƙuri da ka haƙura, ko ba don komai ba akwai yara ƙanana, za a maishe su marayu ga uwayensu da rai."

Zan Qara Aure // 10: Ka Fahimce Ta
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Mace gaba ɗayanta rauni ne da ita, amma ba dukan mata suka san haka ba, da za ka tuna maganganun da muka yi a baya za ka ga ba wani abu mai mahimmanci a wurinta irin magana mai dadi da sanyaya rai, don haka take ganin kishiyar hakan ita ce maganganu masu zafi da za su bata rai, a duk lokacin da ranta ya baci za ta yi ƙoƙarin yin amfani da su wajen yanke hukunci, a gaskiya duk maganganun da za ta yi a lokacin fushi ta yi su ne kawai ba wai haka abin yake a zuciyarta ba.

In ma kana da mahaifiya a kusa ko wata babbar 'yar uwa za ta ba ka haƙuri ta ce "Bacin rai ne" ita kanta in ta huce za ka ga ta yi laushi gaba ɗaya don ba ta san yadda maganar za ta kai ba, in har za ta yi magana za ta iya yin amfani da duk kalaman da ta san za su baƙanta maka rai, kamar ta ambato abubuwan da ta san sirri ne, waɗanda ta tabbatar ba za ka ji dadinsu ba, ko ta gaya maka kai tsaye "Ni banda ƙaddara mai zai kawo ni wannan baƙin gidan? Tun da mutum ya shugo ba abin da yake gani banda baƙin ciki da bacin zuciya" da a ce ranta bai baci ba ba za ta furta waɗannan kalaman ba.

Duk da ta furta su ma in hankalinta ya kwanta za ka ji ta zo cikin natsuwa da sanyin rai "Don Allah ka yi haƙuri bacin rai ne, ni ban sam ma na faɗi waɗannan maganganun ba" in da za ka zuciya a lokacin ka yi mata fada za ka ji ta ce "Ai na ba ka haƙuri, don Allah ka yi min hanzari, ba ka ga ni mace ce ba? Ka san mu mata muna da rauni" gaskiya ta gaya maka, abin dake cikin zuciyarta na fushi kawai ta fitar, in ma za ta yi wa wata fada za ta ce mata ta san maganganun da za ta riƙa faɗi amma ba zai hana in ranta ya baci ta fado duk abin da ya yi mata dadi ba.
Abin da ya dace namiji ya fahimta anan shi ne, duk maganganun da mace za ta yi a cikin bacin rai kar ya yi hukunci da su, ya fahimci cewa wannan ita ce hanyarta ta nuna fushinta ko daukar fansar abin da take ganin muganci ne, in da hankalinta zai kwanta ba za ta so a dauko maganar ba, in ma ka dauko din za ta nuna damuwarta ko ta yi woƙarin tura maka laifin da cewa kai ka sa ta yi wannan shirmen gwargwadon yadda ta ga tasirin maganar a wurinka, misalin manyan maganganun da mace kan fado a sanadiyyar bacin rai waɗanda ba su ne azuciyarta ba kamar ta ce "In ka san ka cika da a cikin mahaifiyarka ka sake ni".

Tabbas ta haɗa ka da abin da zai iya sanya ka ka yi sakin, amma ba wai sakin take so ba, so take ranka ya baci kamar yadda nata ya baci, da za ka saketa din wata nan take za ta fashe da kuka, don ba zahirin sakin take nema ba, mai ƙarfin hali ita ce za ta iya ci gaba da magana tana yi tana buga hannu "Wallahi ya fi nono fari, ni banda ƙaddara ma mai zai sa na aure ka?! Don Allah ka dube ni ka dubi kanka? In aka ce ka fuskanci ubana ma ka yi masa maganar aurena ka isa ne? Ni dama wallahi abin da nake so kenan, gidan wahala gidan banza, kalle ni ka ga yadda duk na lalace, na kode na ƙanjame ba abin da nake sha sai a hannunka sai wahala, ni alhamdu lillah!"

Tana magana tana kaiwa da komowa, ta shiga daki ta fito, ta tafa da bayan hannu ta sauke a cinya alamar baƙin ciki, duk hawaye ya hade mata da majina, sai kuma in ranta ya kwanta ne za ta fara fado wasu abubuwan duk da ya yi mata, tana gaya wa masu sauraronta don su yi mata hanzarin maganganun da ta furta, wasu masu hankali a cikinsu suna ba ta haƙuri a hannu daya, a ɗaya hannun suna cewa "In rai ya baci bai kamata hankali ya gushe ba" na ji wani hukunci da wani mutum yake gaya wa abokinsa yadda ya yi, muna mota a hanyata ta zuwa Kaduna daga Bauchi, a lokacin da abokin nasa yake nuna masa kuskurensa na sakin uwargidansa duk kuwa da jimawar da suka yi tare, da yawan 'ya'yan da ta haifa masa, da kada bakinsa sai ya ce "Tabbas abin da zafi, amma na so ne na nuna mata cewa lallai ni din da ne a cikin mahaifiyata, tabbas na haifu din, ni fa mace zan iya yi mata hanzari a komai, amma kar ta tabi mahaifiyata".

Ikon Allah, duk motar aka tsit ana jinsu, a tare da ni akwai wata da ta fito daga Jos, mutumin ya ce "In ta zage ni zan iya yi mata haƙuri, ai a baya ma ta zage ni din ba ɗaya ba kuma na shanye, a wannan karon ni ban ishe ta zagi ba sai da ta haɗa da mahaifiyata, don a tunaninta shi ne zai sa raina ya baci, saboda saninta da yadda nake girmama mahaifiyar tawa, ai na ƙyale ta ta gama zazzaga tsiyarta ina jinta, na yi kamar komai ya wuce, sai bayan kwana biyu ta gama sakkowa gaba ɗaya hankalinta ya natsu, ta gane cewa ta yi kuskure, ta gama duk abin da za ta yi don ganin na manta abin da ta yi min, sannan ne haka kwatsam na banka mata saki ɗaya tal, tana ganin zan dawo da ita yau ko gobe, sai labari ma ta ji cewa na yi aure, na ce ta zo ta kwashe sauran kayanta ko na tara mata su a store don ina da buƙatar dakin".

Wannan hukuncin ko a wurinmu maza ya yi tsauri da yawa. Kowa sai guna-guni yake yi amma ba zai iya yin magana ba tunda ba da shi ake yi ba. Duk da haka macen da take kusa da ni sai da ta ce "Amma kai ma tunda ta ba ka haƙuri da ka haƙura, ko ba don komai ba akwai yara ƙanana, za a maishe su marayu ga uwayensu da rai." Wasu mazan kuma suna cewa "Ka kyauta, nan gaba in aka ce ta maimaita abin da ta yi ba za ta ƙara ba" a taƙaice dai maza ya kamata su riƙa yi wa mata hanzari saboda fahimtarsu, su ma matan ya kamata ko sun yi fushi su san irin kalaman da za su riƙa fita daga bakinsu.

Post a Comment

0 Comments