Muguwar
sha'awa kuma takan ƙare daga watan da ka fara sanin iyalinka sai sha'awar ɗabi'a ta ragu. Waɗanda
suka san ma'anar soyayya sukan tsufa da ita, kuma ana ganinta tare da su. Wadanda suka yi mata gurguwar fahimta sukan ce ta ƙare daga shiga dakin aure.
Kundin Ma’aurata // 17:
Don Me Kake Ɓoyewa?
Baban Manar Alƙasim
Zauren
Markazus Sunnah
Ba ina
adawa da zuwan saurayi gidan budurwa hira ba ne, don na yi kuma ba zan ce ya
zama halas ba. Sai dai tambayar
ita ce: “Wace uwar
ake tsinanawa matuƙar ba a fitowa a nuna wa juna gaskiya?” In kana da wata ɗabi'a, ka fito ka nuna mata. Kar ka ji tsoron cewa
za ta iya rabuwa da kai. Wani yana da saurin
fushi, matsanancin kishi, faɗa ta ba gaira ba dalili, mugun son shimfiɗa a kowane lokaci,
da dai wasu abubuwa da kake ganin ba za ku daidaita a kai ba. Ka nuna mata. In ta yarda shi ke nan. Wannan ya fi sauƙi sama da a ce ka ɓoye in ta shigo gidanka ku fara yaƙin basasan da bai da iyaka. Na taɓa ji
wata tana gaya wa saurayinta cewa "Ni duk faɗan da za ka yi ba zai dame ni ba, amma kada ka yi min a gaban
jama'a." Alal aƙalla za su fahimci juna a nan, kowa ya san abin da abokin zamansa ba ya so da wanda
yake so.
Zan so
ku daidaita a kan wasu abubuwa. Mu dai mun taɓa aurar da wata yarinya sai maigidanta ya ce bai son kayan ɗaki. Ya tsaya a kan ta
sayar da su ta sayo kujeru. Ƙarshe hakan aka yi. Ke nan ya dace a san abubuwan da ba a buƙata ta zo da su tun da wuri. Babu laifi in ka san
cewa za ta iya cin irin abincin da za ka riƙa ba ta. Ba sai an yi ittifaƙi a kai ba, amma in ka san iyalinka ba
za ta yi aikin gwamnati ba, ko ba za ta ci gaba da karatun boko ba, to ka daure
ka faɗa mata
gaskiya tun kafin a kai ga an ɗaura auren.
Na san
mutane guda biyu. Ɗayan matansa 3. Suka nemi su ci gaba da karatu. Ya ce
bai da matsala zai iya ɗaukar
nauyinsu, amma ba zai yarda da aikin gwamnati ba. Da suka ji haka sai
suka fasa. Waɗannan ma bayan aure ne, amma akwai wata da suka yi alkawarin
cewa zai bar ta ta ci gaba da karatu bayan aure. Abin takaici sai ya ce
sam bai san wannan maganar ba. Tana tare
da shi, amma duk lokacin da ta ga sa'o'inta sun dawo makaranta ko wurin aiki
sai ta ce maigidanta ya cuce ta, kuma ba ta damuwa a gaban kowa takan faɗa.
Wasu
hatta maganar fita unguwa ba ya yarda da shi. Yana ganin wannan shi
ake kira kulle. Na ga mutumin da matansa suke fita unguwa
da asuba su dawo da daddare. Duk dai saboda tsaro. Na ce yana da gaskiya amma zai yi kyau ya gaya wa wanda zai
aura ɗabi'unsa,
don kar a zo ana ja-ni-in-ja-ka bayan aure. Akwai waɗanda samsam ma ba su yarda da maganar
zuwa unguwa ba. Ko uwayen yarinya ba sa ganinta in ba salla
ko wani abu mai girma ba. To mutum in ya san don
Allah yake abu bai dace ya ɓoye komai ba. Lallai Musulmai su
tsaya a kan sharuɗɗansu,
in har ka faɗi yadda
kake da wahala ka ji ana zagi ko zargi bayan aure.
Yadda
za ka san ɓata wa
juna lokaci ake yi a wuraren zance, akan ɗaura aure ma'auratan kullum sukan zauna
daga ƙarfe
9pm-11pm na tsawon shekara 1-4, amma ba su san dabi'un juna ba, saboda
ba abin da suke yi kenan ba. Ƙoƙarin kawar da sha'awa kawai ake yi ta wurin mannuwa da juna,
tsotson minti da wasa da hannu. Irin wannan ne bayan aure sai macen ta
ga kamar wani namiji ta aura ba wanda ta sani ba. Duk halin da ta san su
da shi ya canja. A gaskiya da ma ba sanayyar aka yi ba. Wani abokin aikina ya
gaya min cewa kusan shekararsa 3 yana neman aure amma ya zauna da matar sau 3 ne kacal.
Da na
gwada sai na ga to ni me nake ce mata? Duk da cewa ni shekara 4 na yi ina nema,
kuma na je gidansu ya kai sau 6. Nakan je bayan magriba. Duk da ɗan ɓata lokacin
da ake yi wurin shirye-shirye in na ga Isha ta gabato nakan gudu. Kenan nakan sami kamar minti 20 zuwa ishirin da wani abu. In na kwatanta da abokina to na matsa ƙwarai. Sai dai kuma in na ga
wasu to nawa ya dan fi kyau, don su ba a cikin gidan ba ne, a waje suke zama,
su biyu kacal da daddare a saƙo, sannan a cikin duhu kamar marasa gaskiya. Ban san wace fahimta ce da ba a yinta a cikin haske ba sai a
duhu. Kuma kullum sai an yi ta kamar masu haddar Ƙur'ani.
Wasu daga cikin
abubuwan da za su fi ba wa mai hankali da sanin yakamata (musamman idan ya damu
da muhimmancin lokaci) takaici su ne:
1. Yayin da za ka
bibiyi maganganun soyayar da suke faɗa wa juna, to duk
maimaici ne.
2. Yayin da za ka duba Chats da suke yi ko wasiƙu
da suke rubutawa, duk dai za ka ga maganganun ba sa wuce: “Ina son ka”, “Na damu
da kai,” “Ina kewarka” da makamantansu. Kullum su kuma ake maimaitawa. Har na
tuna Hausa da ake faɗin: “Maimaita aji sai jaki.” Wannan yana nuni da
ƙololuwar ƙarancin damuwa da lokaci da rashin fikira da ƙirƙira. Wanda ya sanya
muradin ci gaba a rayuwa, kai tsaye zai sai wannan ba komai ba ne face ɓata
lokaci.
Wani abin da zai ba da mamaki kuma shi ne, mata sun ɗauki
zuwan da ake yi wurinsu kamar burgewa. Suna ganin hakan ne kaɗai ke nuna an
damu da su. Haka ma kiran waya. Mace mai martaba cikin ƙawayenta ita ce wacce
saurayinta ya fi kiran ta a waya. Assha! Na taɓa jin wani malami ya wa’azi ta
Turanci, sai yake cewa: “The heavier you are on his pocket, the lighter you will
be in his heart.” Ma’ana: “Irin nauyinki a aljihunsa, shi zai nuna irin matsayi
da kimarki a cikin zuciyarsa.” (Wannan babbar magana ce). Da mata za su gane
haka, da sun san matsawa da suke yi a samarinsu wajen dole sai an ta ƙona kuɗi kan
waya na da tasiri matuƙa kan daraja da ƙimarsu ga samarin, da kuwa sun sauya.
Irin
wannan zaman na ɓata wa
juna lokaci shi ne ake kira da zaman soyayya wanda mace in ba ta yi shi ba take
ganin kamar an yi mata auren dole. A
haƙiƙanin gaskiya ba haka lamarin yake ba. Soyayya ba a yin ta kafin
aure. Akan ba da damar a yi wannan zaman ne don a
fahimci juna. Kowa ya san hali da ɗabi'un wanda zai aura. Ko dai
su sami ƙarfin
gwiwar ci gaba, ko su sami matsayar hanƙure wa juna. Su san abubuwan da
kowa yake so da waɗanda ba
ya so, don su kiyaye abin da za su aikata da waɗanda za su guje wa.
Soyayya
ba ta amsa sunanta sai ta cika, a kowani harshe ne kuwa. A Turance kalmar "love" sam ba ta tsaya kan abin da kake
ji a zuciyarka na ƙaunar wani ba. Ta shafi ma duk abin da za ka yi da gaɓoɓinka a dominsa. Haka "Hub" a
Larabce. A Hausa ma tana da faɗi sosai. Dole marubuta su
rarrabe wa jama'a bambancin da ke akwai a tsakanin ɗan kuka da ɗan tsamiya. Soyayya ta gaskiya
takan fara daga ranar da mace ta sa ƙafa a ɗakinka. Muguwar sha'awa kuma takan ƙare daga watan da ka fara sanin iyalinka sai sha'awar ɗabi'a ta ragu. Waɗanda suka san ma'anar soyayya sukan tsufa da ita, kuma ana
ganinta tare da su. Wadanda suka yi mata gurguwar fahimta sukan
ce ta ƙare daga shiga dakin aure.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.