Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Ƙara Aure // 10: Kun Bar Jaki Kuna Dukar Taiki



Zai iya yi miki kyautar dubu 20 ya kwana 7 ba ko sisi. Mutumin da bai da tausayi ko na anani, in yaro ya faɗi a gabanki zai kece da kuka saboda tsabar jin abin a jikinsa. Zai iya gaya miki bai taɓa yanka kaza ba kuma bai iya kashe cinnaka bare ɓera. In ya gano ke 'yar ɗariƙa ce kullum za ki gan shi da zabgegen carbi ga hoton Shehi a wuyarsa. Bai da zance sai na zikiri. In ke 'yar Izala ce ya ɗingile wando ga geme.

Zan Ƙara Aure // 10: Kun Bar Jaki Kuna Dukar Taiki

Baban Manar Alƙasim
ZAUREN MARKAZUS SUNNAH

Yanzu kan mage ya waye. Mata ba sa yarda su yi aure sai sun tabbatar da cewa wanda za su aura ɗin ya cancanta, masamman matan da suka yi jami'a ko wata makarantar gaba da sakandare. Ire-irenn waɗannan matan ba sa yarda uwayensu su zaɓar musu maza. Sun fi son su ƙwanƙwasa wanda suke ganin ya nuna su ɗauka. Wannan bayan wata jarabawa ke nan da suka yi masa tare da tabbatar da cewa ya cancanta. Da wahala wani ya fito wa 'yar boko ta karɓe shi ido rufe ba tare da fahimtar juna ba.
Wannan ce irin wayewar da muka samu a rayuwarmu ta yau, wacce matan karkara ko na marayar da ba su da cikakken 'yanci a gidansu ba su da ita. Akwai wata abokiyar aikina a shekarun baya da ta gaya min cewa ba za ta auri wani namiji ba sai ta tabbatar da cewa ya cancanci ya zama jagoranta kuma uban 'ya'yanta. Ba kowane namiji ne za ta miƙa masa wuya ta riƙa bin sa zaizai kamar wata raƙuma ba. Da yake ni namiji ne sai na yi dariya kawai na bi ta.
Kwanan nan wani mutum da na san yana da mata kuma ba abin da ya haɗa shi da Islamiyya ko Larabci na ga ya fara sanya jallabiya kuma yana maganar komawa makaranta don karantar addini. Ashe wata ya ƙyalla ido ya gani, kuci-kuci kaɗan ya fara muku zancen mutuwa da lahira. Bayan lamarin ya yi nisa sai muka gano ashe aure yake nema, kuma yarinyar 'yar Islamiya ce. Har wasiƙa take rubuto masa da Larabci yana amsawa. In ta turo masa sai ya tura wa wani abokinsa ya fassara masa kuma ya rubuta masa amsar ya aiko.
In taƙaice maka labari wallahi yanzu haka tana gidansa kuma a hakan. To ina bokon da wayewar da ta kasa gane cewa bai san komai ba? Namiji ya wuce duk inda kike zato, ɗan zakara ne da zai ɗauki ƙwaya ya ba ki shi ya ci tsakuwa. Zai iya yi miki kyautar dubu 20 ya kwana 7 ba ko sisi. Mutumin da bai da tausayi ko na anani, in yaro ya faɗi a gabanki zai kece da kuka saboda tsabar jin abin a jikinsa. Zai iya gaya miki bai taɓa yanka kaza ba kuma bai iya kashe cinnaka bare ɓera. In ya gano ke 'yar ɗariƙa ce kullum za ki gan shi da zabgegen carbi ga hoton Shehi a wuyarsa. Bai da zance sai na zikiri. In ke 'yar Izala ce ya ɗingile wando ga geme.
In kuwa 'yar Shi'a ce zai yi ta sanya baƙin kaya ya yi ta sumbatu kamar wanda ya kwana a waje. Wahala za ki sha da namiji. Hanya mafi sauƙi ita ce bincike, ba jarabawar da za ki yi wa namiji ki ci nasara in ba ita ba. In kika ce wayewarki ce sai ki kori mutumin kirki ki ɗauko tumun dare, don na kirkin zai fito da gaskiyarsa ne. Ƙila ki ce bai yi miki ba. Na banzan kuwa auna ki zai yi ya fito miki a sifar da kike buƙatar ganinsa. Duk mutumin da zai ƙara aure mace ta huta da dogon bincike; ya yake zama da matarsa? In matar cikin ce da matsala, za ta sani. In maigidan ne duk komai zai bayyana. Ba mutumin da wasu ba su san shi ba.
Babban abin da 'yar boko ba ta sani ba shi ne, wayewarki da karatunki ba zai taimake ki wurin gano namiji ba. Uwayenkin da kike raina musu, ko kike ganin cewa ba su yi wayewar da kika yi ba, sun fi ki sanin sharrin namiji. Mahaifiyarki ta kwashe shekara ashirin da shi. Har yanzu fama take da shi. Ta ina ke da ba ki yi ma auren ba za ki fi ta saninsa? Matarsa da mu'amalarsa da ita za su taimaka miki sanin halinsa a gida. Haƙurinsa, kyautarsa da mu'amalarsa, maƙwabtansa ba na jikinsa da za su ɓoye wani abin ba za su faɗi addininsa da hanyar tara dukiyarsa ta haram ko halas. Wayewa ko 'yancin da kike ganin za su yi miki komai ba abin da za su yi sai ɓatar da ke.

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.