Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Ƙara Aure // 28: Wata Kan Zama Dalili


Na ga wace ta tsaya wa wani ubangidanta tana masa komai, da wanda ya shafi ofis da ma wanda bai shafa ba. Kuma ta shahara da kamun kai kamar dai yadda maigidan nata yake. Ashe aurensa take so. Duk wani abu da ya shafe shi sai ta yi maza ta amshe. Yana da iyalinsa da komai bai ma da tunanin aure, amma a hankali ta yi masa allura ta wurin ƙanƙan da kai ga ladabi. Ai bayan wani ɗan lokaci sai kawai muka ji cewa...


Zan Ƙara Aure // 28:  Wata Kan Zama Dalili

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah      
  
Tarihi bai dauko mana cewa Khadija RA ta yi sha'awar Annabi SAW ne ya sa ta nemi ya yi kasuwanci a cikin dukiyarta don ta sami silar da za ta janyo shi kusa da ita ba, a zahiri mun ga cewa amanarsa da wasu alamu da aka gaya mata cewa an gani tare da shi su suka ja hankalinta, kuma ta yi dace da samun fiyayyen halitta, haka a yau akan sami masu hali da suke ganin mutumin kirki sai su yi sha'awar a ce ya zama maigidansu ba don suna sa rai da zai iya ba su wani abin duniya ba, tsabar natsuwarsa ce da hankalinsa, ko kuma ilimi ko wata halitta da suke matuƙar buƙata kuma suka tsince ta tare da shi.
.
Ko anan ƙasar ma na san matan da suka dauki malamai don su koyar da su a ƙarshe suka aure malaman don ganin ƙimarsu da hankalinsu, wannan kam ya faru, na taba zuwa wurin wani mai faci ban same shi ba, nan ne ake ba da labarin cewa wata mata kusan duk kwana biyu za ta zo faci ko ƙarin iska, a ƙarshe dai ta aure shi ta raba shi da sana'ar, ya zama babban mutum sai fantamawarsa yake yi, ita tana cikin farin ciki cewa ta sami mijin aure, ba kudinsa ta gani ba bare a ce tana nadama ashe bai da komai, har wurin sana'arsa ta bi shi ta dauko shi.
.
Na kuma taɓa ganin wani mutum ban san inda ya san ni ba, amma ya same ni shi da matarsa a mota, hajiya ce, ta yaba wa hankalinsa ta aure shi, sai hayayyafa take ta yi masa, a lokacin sun zo wurina ne wai tana son ta tura shi karatu waje, na gaya musu gaskiya ba aikina ba ne ban ma san yadda ake yi ba, ka san mu da son jin ƙwab, na ce duk yaran da na gani a mota nasu ne? Ya tabbatar min da cewa ita ta haifa masa, kuma tana bala'in son sa, na ce me ya sa to take ƙoƙarin tura shi waje? Ya ce ai in ya tafi ne zai sami dalilin da zai dauko su, Inyamura ce amma ta san abinda take yi sosai.
.
To duk irin waɗannan in ka tattara sai ka taras ƙila mutum ma yana da aure, wata ta fito masa kuma ta ce ba ta son kowa sai shi. A ƙarshe kuma ta aure shi, kenan tsayuwarta da amfani da damarta ya zama dalilin ƙara aure kenan, mun karanta tarihi inda wata ta ta zo fadar Annabi SAW ta ce masa ta ba shi kanta ya aura, yana da matansa, amma da ta tsaya ƙyam a ƙarshe dai auren an yi bayan wani ɗan lokaci, ta auri wani can daban amma zuciyarta tana tare da Annabi SAW, kuma sai da ya ƙara auren da ita.
.
Na ga wace ta tsaya wa wani ubangidanta tana masa komai, da wanda ya shafi ofis da ma wanda bai shafa ba. Kuma ta shahara da kamun kai kamar dai yadda maigidan nata yake. Ashe aurensa take so. Duk wani abu da ya shafe shi sai ta yi maza ta amshe. Yana da iyalinsa da komai bai ma da tunanin aure, amma a hankali ta yi masa allura ta wurin ƙanƙan da kai ga ladabi. Ai bayan wani ɗan lokaci sai kawai muka ji cewa ya yaba da hankalinta har ma ya  tafi wurin mahaifa sun amince masa da fito kawai, sai mu'amallarta da shi ta zama dalilin ƙara aurensa.
.
Ba na gardamar cewa wasu matan in suka yi arziƙi sukan nemi wani ɗan tagaje-tagajen namiji don su sami damar yin abinda suke so ba tare da takura ba, ko kuma shi kansa su riƙa juya shi yadda suke so, sau daya dai na taba jin wata mata wai ta yi wata attajira maganar banza, ta kira ta da wani suna wanda bai mata daɗi ba, don haka ta yi amfani da kudinta ta aure mata miji kuma ta kore ta, wannan bai cika faruwa ba, amma abinda muke ƙoƙarin fitarwa anan shi ne, za a iya samun mutum da iyalinsa bai da niyyar ƙara aure sai wata mace ta fito masa ta hanyar da take ganin za ta ci nasara kuma ta aure shi din.
.
Na dai sami wasu da suke aiki tare, kullum tana kawo masa kukan matsalolin rayuwa tsakaninta da maigidanta, shi ne yake ƙoƙarin sulhunta su, ko me ya faru oho, auren ya baci kuma sun auri junansu, ƙila ta amince da shi ne bisa maganganunsa da yadda yake ƙoƙarin sulhunta su din, da tsammanin samun sauƙi sama da tsohon mijinta wanda ya yi ta shiga tsakaninsu, da farko bai da niyyar aure, amma yanayin yadda ta tsaya a kansa da buƙatun sai ta aure shi din ya sa ya yanke hukuncin auren nata, komai na iya zama babban dalilin da zai sa maigida ya buƙaci ƙarin aure.

Post a Comment

0 Comments