Ticker

6/recent/ticker-posts

Kundin Ma'aurata // 25: Wasu 'Yan Shawarwar


In za ka tuna mun yi wannan maganar a baya cewa wasu abubuwan da dama mace kan yi su ne don zolaya ba da gaske take ba, ko don yanayin halittar da Allah ya yi mata. Misali: Za ka zaunar da ita ne ka yi mata lissafin duk matsalolin da kake da su, da yanayin yadda ka sami kanka, amma kana gamawa sai ka ga kamar ba da ita kuka yi maganar ba. Nan take za ta ce maka "Ba mu da kaza da kaza fa!" Ba wai ta ƙaryata ka ba ne ko maganarka ba ta dame ta ba, gani take waɗannan abubuwan da...


Kundin Ma'aurata // 25:  Wasu 'Yan Shawarwar

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

BAN DA SAURIN FUSHI
Ita mace bambancinta da namiji tana da saurin tasirantuwa ne da lamari, abu kadan zai iya sawa ta so abu ko ta ƙi shi, kamar yadda ƙaramin abu zai iya baƙanta mata rai ko ya sauko da ita bayan ta fusata, tana da saurin daukar zafi kuma cike take da haƙuri da saurin yafiya, waɗannan sifofin ne ma suka sa ake iya rayuwa da ita na tsawon lokaci, kai namiji bai kamata a ce ka dauki wasu 'yan sifofinta ba, masamman saurin fushi da ƙarancin duba abin da zai kai ya komo nan gaba, ita duk abin da ya gamsar da zuciyarta an gama, kai kana da buƙatar aiki da ƙwaƙwalwa wajen duba sakamakon abu in har ka sami kanka a ciki.
.
Misali mace tana matuƙar ƙaunarka za ta iya tsittsine maka ta uwa ta uba ta tsaya kan sai ka sake ta, in ka jure ka haƙura, ka kau da kanka za ta dawo tana ba ka haƙuri da guntun hawayenta da komai kan cewa sharrin shedan ne, in kuma ka biye mata za ka sake ta ƙarshe za ku yi nadama ku biyu din, ya kamata in har ta nuna maka nummunan hainta kai ka tuna alkhairinta, ka diba hidimar da take maka, bugu da ƙari ga ma wata zuriya da ta daure ku da ita gaba daya, ka kalli abin da zai biyo baya in ka rabu da ita.
.
Zurfin ciki bai nufin hadiyar magana kadai, akwai kuma iko na taskace fushi da damuwa ko markade su gaba daya, in tana da saurin fushi a matsayin mace kai namiji ka zama mai juriya da kai hankali nesa, wani mutum ya same ni a ofis yana gaya min cewa matarsa ta kai shi bango sosan gaske, ta yadda har ransa ta nema da wata sharbebiyar wuƙa, a gaskiya ya sake ta, na tambaye shi ko yana son ya dawo da ita ne? Ya ce tausayinta yake ji a irin halin da ta sami kanta a ciki, duk ta yi la'asar, sannan ga wasu ƙananan yara a gabansu bai son ya maishe su marayu da uwayensu da rai.
.
Na ce to ya dawo da ita mana bisa sharadi da shaidar uwayensu, sai ya ce min ya yi mata saki daya-daya daban-daban har guda uku, don in haukarta ta tashi ba ta tantance a gida suke ko a kasuwa, kuma a gaban 'ya'yanta suke ko su kadai, kawai za ta yi abinta, rigimar ƙarshe ma a kasuwar aka yi, to da na yi ƙoƙarin jawo masa ayoyin da suka yi magana a kan saki da sauran hadisai masu alaƙa da haka sai na iske cewa duk ya san su, kuma ya haddace su, amma da wannan din yana bincikawa ne ko ina da wata fatawa wace zan ba shi ta taimaka masa wajen dawo da iyalinsa, ya ba ni tausayi, don mutumin ya haura hamsin, ga iliminsa ga komai yana binciken hanyar da zai dawo da matarsa bayan ya sake ta saki uku da guda-guda a mabambamtan lokuta.
.
                 KABAR RUƘO
In za ka tuna mun yi wannan maganar a baya cewa wasu abubuwan da dama mace kan yi su ne don zolaya ba da gaske take ba, ko don yanayin halittar da Allah ya yi mata. Misali: Za ka zaunar da ita ne ka yi mata lissafin duk matsalolin da kake da su, da yanayin yadda ka sami kanka, amma kana gamawa sai ka ga kamar ba da ita kuka yi maganar ba. Nan take za ta ce maka "Ba mu da kaza da kaza fa!" Ba wai ta ƙaryata ka ba ne ko maganarka ba ta dame ta ba, gani take waɗannan abubuwan da ta gaya maka tabbas akwai buƙatarsu a gida, kuma in har ba ta gaya maka ba za ka iya yin fushi ka ce ba ta fada ba, shi ya sa kawai ta yanke wannan hukuncin.
.
To ka yi mu'ammala da ita a yadda take kawai banda ruƙo, kar in ta yi maka laifi ka riƙa karanto mata wasu laifuffuka da ta yi a baya, wadanda tuni ta ma manta da su ba ta tunaninsu, in ta yi abu ta roƙe ka cewa ka yi haƙuri, to ka daure ka haƙura din bayan nuna mata laifinta, amma ka sani mace ba halittar namiji ne da ita ba za ta maimaita, kai kuma dama a hadisin da Buhari da Muslim suka rawaito Annabi SAW yana cewa "Mai kayar da mutane a fagen fama ba shi ne jarumi ba, jarumi shi ne wanda yake iya mallakar kansa idan an baƙanta masa rai" wannan mace ce, kai kuma namiji ne, duk wani aikin ƙarfi da maza ke yi mace in ta tsaya za ta yi, ta ma fi namijin, amma banda sha'anin zuciya, anan rauninsu yake.
.
    KAR KA RIƘA DUBA ME KA YI

In dai mace ce, ka yi abin da ya zama wajibi a kanka kawai, ka dauka cewa duk abin da kake mata ba don ita kake yi ba, da farko dai don Allah ne, na biyu kuma kana son ka gyara gidanka ne, in har za ka riƙa ba iyalinka abu kana dubawa nan gaba har gori za ka riƙa yi, cewa "Ashe ban yi miki kaza da kaza ba?" Hakan kuma ba dabi'ar namiji ba ce, ka yi abin da ya dace kawai, ka nuna ƙaunarka kare ta, za ta ji daɗi ta dage wajen kyautata maka ita ma.
.
To bare kuma komai ka yi wa iyalinka, duk da cewa haƙƙinta ne a kanka sai ka yi, Allah kuma zai ba ka lada a kai, wani hadisi da Buhari da Muslim suka rawaito Annabi SAW yana cewa "Ba wani abu da za ka ba wa iyakinka wanda kake neman fuskar Allah da shi sai an ba ka ladarsa, har lomar da za ka saka a bakin matarka" ban sani ba ko shi ne na ga Larabawa suna yanko loma su sa a bakin matansu, ko ka taba gwadawa? A hadisin Muslim fa jima'i da za ka biya wa kanka buƙata ma lada za a baka, Allah sarki!


Post a Comment

1 Comments

Post your comment or ask a question.