Ticker

6/recent/ticker-posts

Kundin Ma’aurata // 24: Matsalolin Farko


To shi namiji a farkon al'amari bai san nauyin gida ba. Zai iya kashe wa mace komai. Kuma ba wani nauyi a kansa wanda yake kula da shi. Cinta da shanta da sauran abubuwan da suka shafe ta duk ba su a kansa. Kenan da sauƙi, don maganganu masu daɗi ba matsala bane yana da lokacinsu kuma zai yi...


Kundin Ma’aurata // 24:  Matsalolin Farko

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah        
A zahiri ba matsaloli ba ne rashin fahimtar juna ne, ko kuma sabo da wasu abubuwan na baya, misali: Ita yarinya in ta girma a gidan ubanta ba komai take yi ba, kodai mahaifiyarta ta maishe ta ƙawa, ko a riƙa samun takon saƙa a tsakaninsu jin cewa ta girma, shi kuma saurayinta in ya zo kullum fara'a ne da maganganu masu daɗi wadanda suke tayar mata da sha'awa kowani lokaci, bai son damuwarta kokadan, duk wani ɗan motsi sai ya tambaye ta ko lafiya.
.
Abubuwan da take buƙata wasu ba sai ta fada ba za a kawo mata, wasu lokutan ma ba ta cewa tana son abu kaza, shi da kansa zai fara tambayarta ko tana son kaza da kaza? A zahirin gaskiya ba komai a kansa, a lokacin bai san nauyin gida ba, ga sha'awa ta dabaibaye shi ta ko'ina, don haka zai iya yin komai don cimma burinsa na maida ita iyalinsa.
.
To bayan daura aure kamar yadda muka sani komai ya canza, ayyuka sun yi wa matar yawa, kamar share-share da goge-goge, tsaftace ko'ina ciki da waje, hadi da ban-daki da kici, ga wanke-wanke, tana gama abincin safe maigida ya fita za ta wanke kwanoni ta yi duk wadancan ayyukan na sama, tana gama su za ta fara shirya abincin rana, kafin ta gama har ya shugo, da zarar ya kammala ita ma ta samu ta kimtsa za a ce la'asar, bayan salla kuma sai shirya abincin yamma, ma'ana dai ba hutu.
.
Shi ya sa galibin mata ba sa iya tsinana komai bayan sallar issha. Duk sun gaji! Ka ga dai waɗannan ayyukan ba ta saba da su a gida ba. Yanzu kuma da ta shugo ba wani mai kama mata. Komai ita za ta yi ita kaɗai. A dalilin haka tana buƙatar kulawarka sama da yadda kake yi mata a baya lokacin da ba ta yi maka wani abu, na farko ta gaji sosai, na biyu kuma duk gajiyar nan don kai ake yi, ko ba komai ya kamata ka nuna cewa lallai ka san abin da ake yi din.
.
To shi namiji a farkon al'amari bai san nauyin gida ba. Zai iya kashe wa mace komai. Kuma ba wani nauyi a kansa wanda yake kula da shi. Cinta da shanta da sauran abubuwan da suka shafe ta duk ba su a kansa. Kenan da sauƙi, don maganganu masu daɗi ba matsala bane yana da lokacinsu kuma zai yi.
.
To da zarar kin shugo cinki da shanki da duk abin da gida yake buƙata shi ne zai kawo, a karin safe kawai zai kashe kaza, ga na rana ga kalacin yamma, banda wasu 'yan ababan ƙwalama wadanda zai yi don tsare gida, duk abubuwan da ya saba yi a baya dole yanzu ya ninka, 'yan lokutan da yake da su a baya yanzu neman halas ya kwashe.
.
Abin da yake buƙata kawai hutu, don ya riga ya gaji a waje, duk gajiyannan yana yi ne don nema wa iyali abin da za su ci, su sha su yi sutura, da ya dawo gida hutu kadai yake buƙata, yana sa rai da irin karairayannan, da maganganu masu daɗi cikin sanyin murya da jin daɗi, to ashe ita ma abin da take buƙata kenan a wurinsa, in ba a yi sa'a ba sai ta fara ganin kamar kulawar da yake yi yanzu ya rage.
.
Wato ya riga ya sami abin da yake so, shi kuma sai ya ga kamar ba ta gode wa duk abin da yake mata alhali duk gajiyar da yake yi a dalilinta ne, in ba a kai hankali nesa ba wannan shi ne dalilin samun sabanin farko a tsakanin masoya, kuma wannan cutar in har ta harbe su ba ta da magani, in ma akwai abin da yake magance wannan matsalar shi ne fahimtar juna, ita matar ta fahimci cewa bai san nemo wani abu don iyali ba, yanzu dole ya fita, ko dama yakan nemo don mace daya ce jal, yanzu sun zama biyu abu ya ƙaru, aikin da za ta yi shi ne haƙuri da abin da ya samu, gami da yi masa godiya, da ƙarfafa masa gwiwa wajen yaba wa ƙoƙarinsa, nan take za ta ga farin cikinsa, sai hira ta barke.
.
Shi kuma in ya dawo ya kalli irin ƙoƙarin da ta yi na shirya kanta, gida da abinci, ya dubi irin ado da kwalliyar da aka yi dominsa, ya yaba mata, sai ta ji daɗi ta dada kusantarsa, in ba hakan aka yi ba, in dai mutum zai riƙa duba wahalhalun da ya sha a dalilinta ne, ko maganganun da za ta yi masa bayan ya ji jiki wajen nemo ababan rayuwa, haƙiƙa zai yi wahala a sami fahimtar juna, ka fahimci cewa ita yarinya ce ba ta riga ta san abin da ake ciki ba.

Post a Comment

0 Comments