Yarinyar murmushi kawai ta yi ta ba su wuri. Abin ya kai ga har binsa ofis take yi don ziyarar ba-zata. Tana so ne ta gani ko 'yan mata suna zuwa wurinsa. A dole ya shiga sanya wa wayarsa tsaro don ma kar ta buɗe. Duk da haka in yana waya sai ta zo kusa da shi ta zauna ta ji abinda yake cewa. In kuma ta ji da mace yake magana ta dunga bin ƙuƙƙufi ke nan sai ta san dalilin da ya sa ta kira shi ko ya kira ta. Duk dai burinta...


Zan Ƙara Aure  // 27:  Ke Ce Sila!!!

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
Kwanaki mun kawa maganar wata da ta sha alwashin rufe ni don ina yin maganar ƙarin aure, ban sani ba ko wasa take yi ko kuma da gaske ne Allah ne masani, amma tabbas wasu sun rufe ni din an kai musu rubutun suna ta fada wai sun gudu min an biyo su da shi, maganar ƙarin aure ce ba sa so, wasu matan duk ma'amallar arziƙi da kuke yi kana yi musu maganar kishiya an gama, sun daina ganin ƙimarka har abada, kamar da wasa har ya yi musu tasiri a zuciya ya ma fara shiga ma'amallarsu da maigidansu ba ma sauran jama'a ba.
.
Wasu uwayen sun saba da yaransu sosai, suna ma'amalla da su kamar abokanansu, in uba ya zo duba diyarsa sai ka ga ta zo da gudu ta rungume shi, wata rana yarinyar tana makaranta suka je kai mata ziyara, ta ji daɗi ta rungume babanta, sai uwar daga baya ta fara guna-guni wai "Ƙatuwar yarinya kamar wannan kake rungumewa kamar wata matarka, wallahi wannan Yahudanci ne" ya ɗan yi murmushi ya ja bakinsa da yake suna gaban yarinyan ne bai son ta fahimci wani abin daban, daga baya ya ce "Wannan dai muharramata ce, 'yata ce ba ta wani ba" da bude bakinta sai ta ce "Ka mai da ita matarka mana, ai ta isa! Sangamemiyar budurwa irin wannan ake rungumewa, mts!"
.
Yarinyar murmushi kawai ta yi ta ba su wuri. Abin ya kai ga har binsa ofis take yi don ziyarar ba-zata. Tana so ne ta gani ko 'yan mata suna zuwa wurinsa. A dole ya shiga sanya wa wayarsa tsaro don ma kar ta buɗe. Duk da haka in yana waya sai ta zo kusa da shi ta zauna ta ji abinda yake cewa. In kuma ta ji da mace yake magana ta dunga bin ƙuƙƙufi ke nan sai ta san dalilin da ya sa ta kira shi ko ya kira ta. Duk dai burinta kar ya ƙara aure, don ba za ta iya zama da kishiya ba, akwai wace ta ce wallahi gwara mutuwa da kishiya, kuma ba ta taba aure ba bare a ce ƙila an yi mata ne ba ta ji daɗi ba.
.
A ƙarshe dai maigidanta ya fara gajiya, har ya zama bai ƙaunar dawowa gida, sha'awar ganinta ko saduwa da ita ta fara raguwa a hankali, har ya fara tunanin ko zai ƙara aure ne, yana buda wa abokinsa irin halin da yake ciki ya ƙarfafa shi kan aniyarsa, nan fa suka fara shawarar irin matar da za a aura, wato wace za ta iya fuskantar kishiyar ta kowace hanya, an kawo 'yan mata sun kai bakwai ana canja su, saboda natsuwarsu da shiru-shirunsu, har sai da aka samo wata tsaleliyar da ko ba ta tanka ba uwarta kawai ta isa.
.
Kafin ta shigo an gaya mata duk irin maganganun da uwargidan take yi, da bibiyar bokaye da makircin mata kala daban-daban don haka da shirinta ta fado gidan, ranar daura auren ma 'yan uwan amaryar suka zo gaban uwargidan suka yi ta soka magana suna cewa "Duk shegen da yake ganin ya isa ya motsa, mu kuma za mu nuna masa iyakarsa, gida nnan ba zo fita ba, shiga sojan badaskare muka yi masa, fita mutuwa, in kuma aka ce za a fitar da mu ta wata hanya to dama a shirye muke, za mu nuna wa mutum iyakarsa" na ƙarƙare maka labari uwargidan yanzu ta yi sanyi ba abinda take iyawa, 'yan uwan mijin da take wulaƙantawa ne ma ke taimakonta a wasu abubuwan, zahiri wasu matan su suke jawo wa kansu matsala.
.
Wallahi na ga wace take bugun ƙirji tana cewa kishiya ba dai gidanta ba. Maganar tana dawowa kunnen mijin, kuma ana masa tsiyar zama ragon maza, ƙarshe ya tashi tsaye don ya nuna mata cewa ba fa yadda ta ɗauke shi yake ba. Ya fara neman aure. Ya nemi uku a gidan mutunci tana wargazawa. Ta  ce wa ta ukun in ta aura mata miji za ta kashe ta. Auren da bai yuwu ba kenan, amma fa ya auro wata tsayayyiyar da take juya ta yadda take so. Ita ma wannan uwargidan ta koma abar tausayi.
.
Don me za ki riƙa cika bakin wai maigidanki bai isa ya ƙara aure ba? Ba ki tunanin ko da ba ya nan za a iya kai masa maganar, bare kuma a ce a gabansa kika yi! Irin wannan ko bai yi niyyar yi ba kin ba shi babbar hujjar da zai nuna miki cewa lallai shi namiji ne, kishin mace da tsabar ƙin kishiya bai hana namiji ƙara aure in dai ya yi niyya, in kuma ya fara nema a gidan arziƙi inda za ki iya bata auren rufa wa kanki asiri ki ja bakinki, in ba haka ba kuwa to ki bata din, zai nemo fetsararriyar da ba yadda za ki yi da ita sai kallo.