Amma don Allah samari su riƙa barin mata suna aure. Wata yarinya ta ba ni tausayi. An hakaito mana cewa an yi mata aure da cikin wata 5. Duk da an zubar da cikin, ta yi roƙon duniyan nan da cewa mijin ya rufa mata asiri, ba ta damu ba ya sake ta, amma kar ya bari maganar ta fita. Ta ce ya bari ta ɗan sami kwana 2 ita ce za ta shirya yadda zai sake ta ɗin ba tare da mutane sun zarge shi ba. Amma duk hanyar da ta bi ya ƙi yarda, sai da ya sake ta kuma ya tona mata asiri kowa ya sani. Duk da cewa...


Kundin Ma'aurata // 23: Ka Yi Haƙuri

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
Maza da dama sukan so su auri budurwa, kuma mu a harshemmu yanzu budurwa ita ce wace ba ta taba yin aure ba, koda kuwa ta zubar da cikin shege a sanadiyar mutu'a da sauransu, galibin 'yammatan da suke lalata a waje suna da 'yan dabarun da suke yi kuma Allah yakan rufa musu asiri mazan ba sa ganewa, masamman samarin yanzu da suke shiga ɗaki ido rufe, wasu kuma tunanin tana da budurcinta ko an keta shi tun asali ma ba shi a ƙwaƙwalensu, to bare su yi zancen dubawa, buƙatarsu kawai mashayi ya shiga tandu, masamman idan suka gan ta tsab-tsab ta sha kwalliyar amartaka.
.
Sai dai ba anan take ba, inda gizo yake saƙar shi ne ya same ta da ciki, ko a gaya masa ta taba zubarwa so kaza, ko dama 'yar iska ce, da sauran ƙananan gulmace-gulmace irin wannan, an dai riga an yi kuskure tun farko tunda har aka kai ga daura aure ba ka yi wannan binciken ba, ga shi kuma yana da mahimmanci a wurinka, wasu 'yammatan sukan yi ta sheƙe ayarsu ne sai inda rana ta fadi musu, wasu kuwa yaudararsu aka yi, wasu daga fyade ne shedanun mutane suka sami ƙofa.
.
Akwai kuma waɗanda zarafin rayuwa ya tursasa su tambadewa, ko ma meye farkon lamarin in ka ga mace tana son aure hankali ne ya zo mata tana sha'awar kamewa, wannan tana buƙatar taimako daidai wa daida, na taba ganin wata shahararriya wace har kirari ake mata wurin lalacewa, da hankali ya zo mata ta natsu, wallahi ko wasu natsattsun tun farko ba su kaita ba, to bare kuma yanzu maza sun baci da gulma.
.
A shekarun baya ne muka yi bayanin wani da ya biya kudin mota takanas daka Saminaka har zuwa Kaduna don kawai ya gaya wa wani saurayi cewa yarinyar da yake ƙoƙarin aurennan fa ta taba yin fimdin tsaraice (wato blue film), a ƙarshe saurayin ya fasa auren, ban san ribar da magulmacin ya ci a ciki ba, ko ya neme ta ne ba ta ba shi hadin kai ba, ko burinsa ya ga ya hana ta aure ne Allah ne kadai ya sani, ni dai a ganina da ya rufa mata asiri ta yi aurenta.
.
Irin wannan wasan shedan da 'yammata suke yi takan tsaya a duk lokacin da hankali ya zo wa yarinya, ko in ta ga uwar bari, galibin waɗannan yaran za ka same su da kamun kai sama da wasunsu, har gwara su da mai halin dan bera ko maƙaryaciya, ko yarinyar da ta saba da kisar kudi ba adadi, bare yanzu zamanin shaye-shaye, a duk lokacin da ka sami labarin cewa matar da ka aura ta yi kaza a baya don Allah ka rufe wannan shafin gaba daya, ka bude sabo kawai ka roƙi Allah ya shirya muku zuriya.
.
Ba inda aka ce dole sai 'ya'yanka sun yi gadon kuskuren da mahaifiyarsu ta tafka a baya, na taba ganin wani malami da ya yi wa diyarsa muguwar kulle, wallahi har zuwa gidan muke yi don mu ga yarinyar, a sannan muna ƙananan yara, ba zan iya fadin kyawunta ko muni ba don lokacin muna ƙanana ne, amma dai na san fara ce, ba ta wuce shekara 12 ba, sai uban ya riski cewa wani shahwarakin ya lababo ya ƙumsa mata ciki, duk yadda ya kai ga boye maganar wallahi sai da muka ji.
.
Irin waɗannan misalan suna da yawa, ka ga dai in za a yi wa wannan uban adalci ba za a ci bai kula da tarbiyar diyarsa ba, ni kuma ban fahimci cewa tsaron ne ya kawo wannan aika-aikar ba, ƙaddara dai idan ta fado ba yadda za a yi da ita sai haƙuri, kawai idan kai mutum ne mai kamun kai, sanya matarka a mafificiyar hanya.
.
Amma don Allah samari su riƙa barin mata suna aure. Wata yarinya ta ba ni tausayi. An hakaito mana cewa an yi mata aure da cikin wata 5. Duk da an zubar da cikin, ta yi roƙon duniyan nan da cewa mijin ya rufa mata asiri, ba ta damu ba ya sake ta, amma kar ya bari maganar ta fita. Ta ce ya bari ta ɗan sami kwana 2 ita ce za ta shirya yadda zai sake ta ɗin ba tare da mutane sun zarge shi ba. Amma duk hanyar da ta bi ya ƙi yarda, sai da ya sake ta kuma ya tona mata asiri kowa ya sani. Duk da cewa daga baya ta sami wani na ƙwarai ya aure ta, amma wallahi ba mu ji dadin yadda ya yi mata haka ba, don ba ita ba har uwayenta sun ce ya ci mutuncinsu.
.
An ce shi ma ya yi iƙirarin cewa uwayenta sun san halin da take ciki amma suka kau da kai suka tura masa ita haka a duƙunƙune, wannan ya sa ya dauki matakin ramawa, mutumin ba sa'ammu ba ne bare ka ce za ka ba shi shawara, kai ko ma sa'anka ne lamari iyali ba a cika shiga ba, yanzu sai mutum ya ga yankar arbarka ko abin da ransa bai so ba, wasu abubuwan sai dai addu'a kawai.
.
KAFA GINSHIƘIN SOYAYYA
Matarka na shugowa ɗaki bayan abubuwan da aka sani na al'ada da dabi'a zaunar da ita ka zana mata yadda rayuwarka za ta kasance tare da ita, da dai an yi ta bege da sha'awar juna a karance, yanzu komai a aiwace za a yi shi, kai za ka yi matuƙar ƙoƙarinka wajen kula da duk abin da aka lissafo maka dinnan na sharudda da dokokin aure, ita ma ta bi nata, ka gaya mata abubuwan da kake so ta yi da waɗanda ba ka so don gyaran gidanka, kai ma ka yi ƙoƙarin kiyaye nata, daganan za ka taras kowa yana shauƙin dan uwansa, na san mai karatu ya taba ganin soyayyar wasu tsahhi da ta ba shi sha'awa, ga su dai sun tsufa, amma soyayyannan tana jikinsu, gaskiya da gaskiya kenan.