Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Ƙara Aure // 25: Tsohuwar Soyayya



Abin mamaki akwai wata tsohuwa da na sani wacce maigidanta ya rasu. Mun san dai ta gama tsufa ke nan. Kawai sai na sami labarin cewa ta yi aure. Ina ta mamaki, ashe wai

Zan Ƙara Aure // 25: Tsohuwar Soyayya

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Wani sa'in sai ka taras an yi irin mugunyar ƙaunar junannan tsakanin samari, abin ma ya zo ya yi tsananin da mahaifa ba su iya taka wa tafiyar burki sai dai su sanya wa sarautar Allah ido su saduda tsoron su dauki wani mataki a zo sakamakon ya zama mummuna a ƙare da da-na-sani, akan mutu ta hanyar shan wani abu, ko mace ta ƙona kanta, na san wace ta je karuwanci, na ji wace ta yi kisar kai duk dai a kan auren dole.

Wata rana ina kan hanyata ta zuwa Kano tare da wasu samari, ana zuwa wani ƙauye sai na ji wani daga cikinsu yana ba sauran labarin cewa an iso ƙauyen budurwarsa wace ya nema aka hana shi ƙarshe ta fada rijiya ta mutu, ta yi haka ne don huce haushi, tunda ba za t iya zama da wani namiji ba in ba wanda take so ta aura ba, an tausaya wa halin da ya shiga sosai, amma ni takaicin da na yi yadda za ta kashe kanta don za a aura mata wanda ba ta so.

Na halarci wata shari'a a wani ƙauye yanda wata yarinyar ita ma ta kai ƙarar mahaifinta kotu, yarinyar ta yi ridda don ta sami damar da za ta auri wani aljuhun baya, uban ya yi tsayuwar daka kan cewa ba ta isa ba, amma ta riga ta girma, haka dole ya haƙura a ba yadda zai yi, ta aure shi kuma ta hayayyafa, ta zo ta kwanta rashin lafiya kafin a ƙarshe ta ce ga garinkunan, duk dai irin wannan mugunyyar ƙaunar ce da take yin ƙamari a tsakanin masoya guda biyu.

Akwai wata mata da na san ta fara aurar da 'ya'yanta mata, amma na ji tana maganar wani saurayinta da irin yanayin da suka sami kansu a ciki na ƙaunar juna, tana kuma zargin mahaifanta da cewa an yi mata auren dole, bisa ga dukkan alamu da za ta sami yadda take so tabbas za ta bar waɗannan yaran ta koma wajen masoyinta na farko.

Wata kuma uban cewa ya yi ba zai aurar da ita ga wanda take so ba sai dai ta aure shi bayan ransa, na ji tana cewa "Ai kuwa zai mutun, kuma na aure shi in sha Allah" na ce " Wance ki riƙa bi a hankali, abinda babba ya hango fa yaro ko ya hau rimi ba zai hango ba" ta ce "Wallahi ni ma abinda na hango ko ya hau jirgi ba zai hango ba" a taƙaice dai an yi mata auren a kan ba ta so, da uban ya rasu ta fito ta koma wa tsohon saurayinta da take so.

Abin mamaki akwai wata tsohuwa da na sani wacce maigidanta ya rasu. Mun san dai ta gama tsufa ke nan. Kawai sai na sami labarin cewa ta yi aure. Ina ta mamaki, ashe wai ya neme ta tun yaranta auren nasu bai yuwu ba, ƙaunar dai tana cikin zuciyarsu har sai yanzu da aka kai ga daurin auren, na san in kowa zai kawo irin abubuwan da ya sani game da irin waɗannan al'amuran za ka iske yana da labarurruka kala daban-daban.

Sai da yawa mutum bai da niyyar aure kuma ba wani abinda ya shirya dangane da haka, idan ya ji cewa wata tsohuwar budurwarsa da suka sha soyayya tare ta fito, ko mijin ya rasu, nan da nan sai ka ga ya fara shirye-shiryen aure, kan ka ce wani abu har an sa ranar auren, sai ma ka ji har an ɗaura, anan tsohuwar soyayya ta zama dalilin ƙara aure kenan.

Post a Comment

0 Comments