Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Ƙara Aure // 23: Iya Girki



Wata dole ka ci tuwonta da cokali don ba zai cuwu da hannu ba. Kana ɗiba yana watsewa. Wasu matan ba su damu kowa ya ci abincinsu ba, saboda hujjar kai ne ba ka ba da cefane ba. Bahaushiya ce kaɗai take ganin rashin cikaken cefane dalili ne da zai sa abinci ya ƙi...

Zan Ƙara Aure // 23: Iya Girki

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Gaskiya na da wahalar fadi amma a ƙarshe in dai in ka fadi din dole a yaba maka, malam Bahaushe yana da 'yar matsala ta wannan bangare, koma na ce Bahaushiya kai tsaye, zan buga maka misali, wani abokina ya taɓa zuwa gidana aka fito mana da abinci, bayan ya ƙoshi ya wanke hannu sai ya ce "Don Allah ka yi haƙuri, amma matarka ƙabila ce ko?" Yana nufin ba Bahaushiya ba ce? Na ce "Abin mamaki Babarbariya ce" ya ce "Koda na ji" manufarsa Hausawa ba su iya abinci mai dadi ba.

Abu biyu suke tabbatar da wannan maganar, na farko wasu matan don wadata ko talauci ba su damu da koya wa yaransu nau'o'in girki ba, na biyu; Bahaushiya tana jiran ta sami nata ne a cikin kudin da aka ba ta, don ta yi adashi ko zumuncinta, ba wai ta ƙara daga aljuhunta ba, wasu daga cikin matan Hausawa ba su da wayewar ƙara cefane don abinci ya yi dadi, ba su damu wani ya ce "Wance ce ta dafa" ba, hujjarsu a koda yaushe ba ka ba da cefane isasshe ba, yadda ka bayar ta haka za ta yi, in har ba a rage ba kenan, idan muka lura za mu ga akwai kusan abubuwa guda uku anan:-

a) Rashin iya nau'o'in girki.
b) An ba ta bai isa ba, kuma ba za ta iya cikawa ba.
c) Ta rage kudin saboda buƙatunta.

Mu yi wa kammu adalci, ba cewa muka yi Bahaushiya ta riƙa cika kudin cefane ba, muna maganar dalilin da ya sa abincinta sau tari ba ya dadi irin na sauran ƙabilu ne, idan mace ta fito a gidan gata sai ka ga akwai 'yan aiki, yarinya ba abinda ta iya na abinci har sai ta zo aure tukun sai a kai ta wurin koyon abinci ta yi makwanni shida zuwa wata biyu, sai a ba ta takardar shedar diploma a fannin girki wai ta gama kenan, ta ya za a hada ta da wace ta gogu a gaban mahaifiyarta tun tana ƙaramar yarinya har girma?

Wallahil Azim, wasu mazan in za su yi baƙi sai sun zabi nau'in abincin da suke ganin iyalansu sun iya don kar a yi abin kunya, na taɓa hira da wani mutum ya ce min wallahi banda Indomie ba abinda matarsa ta iya dafawa, kuma ta yi makarantar kwana na tsawon shekaru, wannan laifin waye? Wai an yi mata gata ne amma na banza, A muslunce addini ya hana ka in ka ci abinci ka ce "Ba dadi" ko ba ta iya girki ba, mafita kawai ka samo wace ka tabbatar ta iya don ta koya wa ta gidan ko kuma ta riƙa fitar da kai kunya a wasu lokutan.

Bahaushiya ko ba ta iya girki ba maigidanta bai isa ya fada ba, kuma girman kai ba zai bar ta ta koya ba, wallahi na san makarantar Islamiyar da aka ce za a kawo musu wace za ta koya musu wasu girke-girke, sai suka ce za su bar makarantar don ba abinda ya kawo su kenan ba, ya za a ce wata za ta koya musu girki? Duk su bar gidansu su zo makaranta koyon girki? Abin mamaki wasu da ba Hausawa ba sai ga su suna tuna wa malaman maganar malamar da aka ce za ta koyar da su.

Idan 'yar masu kudi gata ta hana ta koyon girki me ya hana 'yar talaka? Talla da sauran lamura, duk daya ne, kwanaki na ji wasu alƙaluma masu ban mamaki, wai 'yan matan da aka aurar da su a wani ƙauye cikin kwana biyu sun kai sittin da wani abu, amma wai an sako sama da talatin da doriya kafin wata daya a kan matsala daya tal, wato rashin iya girki, wallahi na san wace ko mako guda ba ta hada ba aka turo ta gidan mahaifanta wai su koya mata girki.

Uwayemmu in suka yi maka tuwo wallahi ko da safe haka za ka sare shi kana jin dadi, da yawa tuwon yanzu ba ya dahuwa, haka ake baza shi a faranti kamar shinkafa, ba yadda za a yi ka yi tunanin dumama shi, kodai dalilin rashi dahuwa ko kuma ruwa-ruwa kamar fate, miya kuwa wata in ta gama bayan wani dan lokaci haka zai kwanta kamar yadda kasan kamun da aka tace, ban taɓa ganin miya na kwanciya ba sai a wurin wannan matar.

Wata dole ka ci tuwonta da cokali don ba zai cuwu da hannu ba. Kana ɗiba yana watsewa. Wasu matan ba su damu kowa ya ci abincinsu ba, saboda hujjar kai ne ba ka ba da cefane ba. Bahaushiya ce kaɗai take ganin rashin cikaken cefane dalili ne da zai sa abinci ya ƙi dadi, wallahi wata ko nawa ka ba ta abincin ba zai fi haka ba, in ta rage a cefanen yau ba ƙaruwa zai yi a na gobe ba, aljuhunta zai shiga, kuma dole ka kawo na goben kamar haka ko ka ji a ƙwaryar abincinka.

Idan mace ba ta iya girki ba, ko ta iya din amma abincin ba ya dadi tabbas mijinta yana da hujja ƙwaƙƙwara da zai fara tunanin samo wace za ta riƙa fitar da shi kunya a lokacin da zai yi baƙi, ko in za a yi wani sha'ani, yaran da muke da su a yau, in za ka ce su yi abinci ba nama ba spices da seasonings ka tabbatar abincin ba zai cuwu ba, sabanin uwayemmu da wani lokacin ko gishiri babu, amma sai ka rantse komai ya ji har da ƙari, tun azahar ake dora abincin dare, matammu a yau sa'a daya ta yi musu yawa har sun gama, shi ya sa muke samun dauki ba dadi a gidajemmu.

Post a Comment

0 Comments