Sai na kasa gane me mata suka fahimta game da aure? Masamman ma Hausa/Fulani, shi ya sa wasu ƙabilun ba sa yarda su auri Bahaushe saboda yawan saki. Su kuma mazan suna cewa "In kana son ka ga ladabi da iya riƙe miji ka auri ƙabila!" A ina matsalar take? Fulani kuma ka zagaya kotunammu duk su ne, sun je rigimar aure. Waɗannan...

Kundin Ma'aurata - 20: Matsayin Maigidanki
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Da yake ba ni da ilimin hadisi wanda zan iya tantance ingatacce da mai rauni sai na taƙarƙare a hadisan da Nasiruddeen Al-Albaniy kawai ya fitar a As-Saheeh Al-Jami', na san ba ni ba ko mai karatu zai sami natsuwa saboda sanin wannan malamin da kuma ƙoƙarinsa a wannan fanni, ya kawo hadisai masu dama da suka yi magana kan matsayin maigida, akwai wanda Annabi SAW yake cewa "Ki duba matsayinki a wurinsa, don kuwa shi ne aljannarki da wutarki" As-Saheeh Al-Jami' 1509, wannan yana nuna matsayin maigida ne a wurin mace, kai ma malam ka zabo wace kake ganin za ta karanta wannan ko in ka karanta mata za ta fahimta, kar ka bi hasken fata ko ƙarancin shekaru ko wayewa irin ta zamani, da yawammu anan muke yin kuskure.
.
Wata rana matar wani malamina ta zo ta same ni wai gardama suke yi, maigidanta ya ce mata: In ya nemi ya sadu da ita ta ƙi mala'iku za su yi ta tsine mata har ta wayi gari, ta ce "Na san ƙarya yake, buƙatarsa kawai yake so ya biya, na gaya wa ƙawata amma ta ce da gaske ne wai mu zo mu tambaye ka" na yi kasaƙe ina tunani, in har za ta ƙaryata malamina ta ina ni za ta gasgata ni? To amma a ƙarshe ta yarda din, sai nake cewa a zuciyata "Da mai ilimi ce sai dai ya bude mata wurin ta karanta" gaskiya ban ga laifinta ba, don in bai auro ta ba ba za ta rufe kanta ta zo a matsayin iyalinsa ba, wannan matar malam kenan ina ga sauran matan da ba ruwansu da karatun addini, ba su ma san haƙƙoƙin mazan a kansu ba?
.
Abin fa da Annabi SAW yake cewa "Da zan iya sa wani ya yi wa wanin Allah sujada, da na ce wa mace ta yi wa mijinta, na rantse da wanda ran Muhammad yake hannunsa, mace ba za ta iya ba da haƙƙin Ubangijinta ba sai ta ba da na maigidanta, da zai neme ta lokacin tana kan gwiwa ba za ta hana shi ba" As-Silsilatus Saheeha 1203, wannan isa matuƙa kenan wajen kwatance, Al-Ƙatb a Larabce dan surdi ne da matan Larabawa suke hawa in za su haihu, shi ne ya kwatanta da haka, kamar dai mu muce wance tana kan gwiwa, wannan fa maganar Annabi SAW ce, in ba mai addini ba wa za ta kiyaye maka buƙatunka? Shi ya sa Annabi SAW ya ba ka shawarar ka neme ta.
.
Da yawa matan yanzu ji suke yi kamar komai suka yi maka kyautatawa ce kawai amma ba dole ba ne, ba sa ji a jikinsu, na ji wata tana yi wa maigidanta wanki da guda sai daya a cikinsu ta ce "Allah ya kiyaye! Ai wallahi ko nawa ba da hannuna zan wanke ba bare na wani ƙato, uwayena ba su kawo ni don na yi wa wani bauta ba, mu a gidammu ko wanke-wanke ba ma yi bare wata uwar wai wankin kayan miji!" A lokacin wata mai fatawa a cikinsu ta ce "An ce fa hatta dafa abincinnan ba dole ba ne, taimakonsu kawai muke yi" abin mamaki duk sun san wannan hadisin ni ne kawai ban taba ji ba.
.
A ko yaushe mutum zai yi aure ya riƙa duba sashe da sashe, misali in mace ta zama kamar wancan ta saman ina za ka sa rai da cewa za ta ziyarci mahaifiyarka har ta taya ta wani aiki kamar wankin kayan ko dafa abinci? Na taba koyarwa a wata makaranta ta Ingila dake nan Sudan mai suna "City & Gilts" sai na sanya wa daliban darasi a ranar Lahadi, nan ne wata cikinsu take cewa "Gaskiya duk Lahadi nakan wuni a gidan surukata ne, ni nake yi mata duk aikace-aijacen ranar da ma wankin suturunta na makon, don haka ba zan sami damar zuwa ba" a kanta na canja ranar saboda matsayin uwar miji da ta ba shi mahimmanci.
.
In kai kanka a matsayin maigidan ba a kula da matsalolinka ba ya kake tsammanin mahaifiyarka? Wallahi ina karantarwa a gida Nigeria na ce a kawo cikakkun jumloli, wata da ta zo ba da nata misalin sai ta ce "Uwar mijina ta rasu!" Na dan gigita, amma sai na shanye na tambaye ta "Da gaske ne?" Sai ta ce "A'a misali ne ta ba ni" zan zo magana kan wannan gabar amma mu ma in za mu yi aure ya dace mu tantance wace ta dace mu zauna da ita, mace mai ƙyuya zai yi wahala ka same ta ta iya soyayya, don abin ba a baki kawai yake ba, in ba a aikata ba na bakin ba zai yi amfani ba, ta ya daga ganin mace ka ce ka mutu mata?
.
A kan haƙƙin maigida Annabi SAW ya ce "Bai halasta mutum ya yi wa wani sujada ba, da ya halasta da na ce wa mace ta yi wa mijinta don girman haƙƙinsa a wuyarta, na rantse da wanda raina yake hannunsa, da a ce daga ƙafarsa har madugarsa gyambo ne mai fitar da ruwa mai wari, ta zo tana lashe shi da harshenta ba ta gama biyansa haƙƙoƙinsa ba" As-Saheeh Al-Jami' 7725, ni wallahi na ga wace ta auri namiji don ta yi jinyarsa, na ga wadanda suka rabu da mazan don ba su da lafiya, ba wai rashin lafiya na jima'i ba rashin lafiyar jiki, na ga wace tana gidan amma ba abin da ya hada ta da maigidan wai ba shi da lafiya.
.
Sai na kasa gane me mata suka fahimta game da aure? Masamman ma Hausa/Fulani, shi ya sa wasu ƙabilun ba sa yarda su auri Bahaushe saboda yawan saki. Su kuma mazan suna cewa "In kana son ka ga ladabi da iya riƙe miji ka auri ƙabila!" A ina matsalar take? Fulani kuma ka zagaya kotunammu duk su ne, sun je rigimar aure. Waɗannan abubuwa ne da muka san su, tsakanimmu da matammu kowa sukar juna yake, don me ba za mu gyara ba? Mu rage karanta babobin saki mu koma na zamantakewa, na ga mata wadanda ake ce musu malamai, abin da suke yi da mazajensu da kiyoshinsu ko kare aka ba shi ba zai ci ba, mu ma ɗin ga matannan kullum kuka, anya ba a wurin zabi ake samun kuskure ba kuwa?