Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Ƙara Aure // 14: Ina Son Magaji


Mu dai waiwayi tarihi kaɗan za mu ga cewa matar Ibrahim AS ita ta sami baiwan nan Hajir AS. Da dai ta ga suna buƙatar magaji wanda zai tausaya musu in sun girma sai ta ba shi Hajir ya aura.

Zan Ƙara Aure // 14: Ina Son Magaji
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Ba fa kasafai mata ke fahimtar namiji idan ya ce zai ƙara aure a dalilin neman haihuwa ba, ita a ganinta in mijin ne ke da da matsalar kuma ta jure zana da a haka tare da sanin cewa ita da haihuwa famfamfan, me zai hana shi ma ya kwatanta hakan? Amma gaskiyar zance mace ba ta ikon yin maza da yawa koda maigidanta na da matsala, ba kamar shi ba da yake da damar yin mata 4 a lokaci guda, koda kuwa iyalinsa lafiyarta lau bare kuma ga rashin haihuwa, na san tukka-tukkar da aka yi ta yi a wani gida bisa wannan dalilin.

Mijin ya ce zai ƙara aure, matar kuma ta daki ƙasa ta ce ba ta san wannan ba, ƙarshe ta ba shi damar yin auren amma bisa sharadi, tunda burinsa haihuwa ne in ya sami kamar yara biyu to fa amaryar dole za ta kama gabanta, sotolabin ya yarda, da kuwa ta haifa masa yaran ya sake ta, tabbas an kai matsayin da maza ke saki a dalilin rashin haihuwa, sai dai ba su kaɗai ba ne, matan ma kan bar gidajen aurensu ba don ba sa son mijin ba, matsalar dai kenan guda daya, burin samun haihuwa, kenan in aka ga ta barawo to fa a koma a ga ta mabi sawu.

Kuskuren da ake yi a yau za ka taras maza da uwayensu koda yaushe sukan liƙa matsalolin rashin haihuwa ne ga mace, ba sa tunanin cewa rashin haihuwannan fa cuta ne kuma zai iya kama kowa, wato shi ko ita, amma da farko ita ake fara liƙawa matsalar, ta yi ta shaye-shayen magani har ta gaji, kafin a ƙarshe a gano cewa ashe ma ba ita ce ke da matsalar ba shi ne, na san waɗanda har sun ƙara aure ma kafin suka tabbatar da cewa matsalar fa daga gare su ne ba matar ba, wasu mazan kan san haka tun wuri, amma su ɓoye wa macen saboda tsoron rugujewar gida.

Irin waɗannan mazan da suka tabbatar da cewa su ke da matsalar in suka tashi ƙarin aure ba sa yarda su auri uwar mata da ta san komai sai budurwa, ita kam kanta a rufe yake ba abinda ta sani komai ya faɗi yarda za ta yi, sai dai uwayenta in sun ga ta jima ba ta haihu ba, kuma suka bincika suka ji matarsa ta farko ma haka take sai zargin ya dawo kansa, ko ma su fara hure mata kunne.

Akwai wata da 'yan uwan mijin suka sanya ta a gaba kan cewa ba ta haihuwa, kullum sai su zo gidanta su yi ta yi mata habaici, wai sai cin abinci take tana ƙara ƙiba ta ƙi ta cika musu gida da yara, abin haushi har da ƙannin mijin waɗanda ko auren fari ba su yi ba bare su san cewa su din za su haihu ko za su zama kamarta, ai ba macen da ba ta son haihuwa, shi ya sa nake ganin wautar matan da suke ƙididdigar iyali ko jinkirinsa alhali da sauran ƙuruciyarsu, na ga wace ta yi don ta birge mijin a ƙarshe haihuwar ta tsaya cak, da mijin ya ganob haka ya sake ta ya auro wata.

In ma maigidan ne ya nuna yana buƙatar jinkirin haihuwar to shi ya kamata ya sha magunguna ko ya yi allurai, don shi ne ya bayyana cewa bai buƙatar yara, 'yar uwa ta ya zai matsa miki bayan ƙwai ɗaya tal kike nasawa a wata, shi fa an ce miliyoyi ne yake fitarwa a saduwa guda, kuma an ce tsarinnan fa ko maza suna yin sa, to in haka ne ya je ya yi kawai, don in ke ce kika yi a ƙarshe aka sami matsala lokacin da ya buƙaci haihuwar kika kasa tsab zai sami dalilin da zai auro wata, wani karatu zai yi miki wanda zai tafiyar da imaninki, in aka sami mai imani kenan.

Mu dai waiwayi tarihi kaɗan za mu ga cewa matar Ibrahim AS ita ta sami baiwan nan Hajir AS. Da dai ta ga suna buƙatar magaji wanda zai tausaya musu in sun girma sai ta ba shi Hajir ya aura. Kenan neman haihuwa na ɗaya daga cikin dalilan ƙarin aure, ko namiji bai yi tunani ba ke mace ya kamata ki tuna masa, ki taimake shi a kai, don a ƙarshe in an sami abinda ake so din ku biyu za ku amfana, kar ki ce tunda ba za ki haihu ba to ba za a auro wata ba, ki ba shi dama ya gwada mazantakarsa, in an sami haihuwar ku amfana tare, in ba a samu ba kuma zai gane cewa shi yake da matsala, ƙila ya miƙe ya nemi maganin da dukanku za ka haihu.

Post a Comment

0 Comments