Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Ƙara Aure // 20: Don Zumunci



Wani sa'in duk abinda ba naka ba sai ka ƙyamace shi komai kyawunsa kuwa. Wani abin takaici da na gani, wani baƙauye ne ya yi karatu. Allah ya taimake shi da ƙwaƙwalwa. Yana gama jami'a suka riƙe shi, ya zama malami

Zan Ƙara Aure // 20: Don Zumunci
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Wasu da dama in ka bincika aurerrakinsu za ka taras sun yi ne a dalilin gamuwarsu da juna a makarantu ko wuraren aiki, kullum ana haduwa har dai ƙauna ta shiga tsakani, koda kuwa ba wani abu da ya zo daidai sai dai dabi'ar zama tare kawai, sauran ababan da suka shafi ƙabila ko harshe ba a cika damuwa da su ba matuƙar akwai ƙauna da fahimtar juna, na sha ganin Bahaushiya ta auri ƙabilun kudancin Kaduna, wata ma maras salla ta aura, an yi ta dauki ba dadi amma a banza, na ga wata Inyamura ta auri Bayerbe, waɗanda suke muslunta su auri Bahaushe Allah ya yi yawa da su.

Sai dai galibin abinda yake faruwa shi ne ƙarancin fahimtar juna, masamman in ba a kai hankali nesa ba, don kowa da irin tarbiyar da ya dauko daga gidansu ko matattararsu wace ba dole ba ne ta zo daidai da muradin abokin rayuwar, kodai a yi karo da ƙaracin biyayya, rashin iya girki, gazawa wurin gyara kai, masifaffen kishi da sauransu, ko wani sa'in abin kai ga rabuwar aure, wanda shi ne mummunan, in ma ba a rabu din ba sai ka taras miji da matan suna zaune tare amma uwayensu da 'yan uwa ana ta yaƙar juna.

Na sha jin uwaye na ƙorafin cewa dansu ya ƙaurace musu tun lokacin da ya sami aiki a nesa, wanda zai matsa masa ya waiwayi gida kuma matarsa ce amma sam ba abinda take yi sai tara 'yan uwanta, ba ta ƙaunar ya ce ta je garinsu don wani sha'ani, bare a sa rai za ta kwashi 'ya'yan nasa su tafi tare, kenan da gaske ne ba ta son dangin nasa, na ga wace sam ba ta zuwa garin mijin, ko ma ta zo ƙafarta ƙafar 'ya'yanta, ba ta bari wani ya dauke su.

Wata ma in ta je garin mijin ko ta bari an dauki 'yarta ba za ta yi sake su bace wa ganinta ba, sai dai duk inda za su shiga su tafi tare, yadda ka san wasu bare ne waɗanda ba ta gama amincewa da su ba, tana tsoron kar ta yi sakaci su gudu mata da diya, akwai wace takwashe 'ya'yan gaba ɗaya a dalilin rabuwa da mijin da ta yi, 'yan uwansa sun yi ƙoƙarin karbo su amma abin ya faskara, a ƙarshe ma saduda suka yi suka haƙura, na sha jin uwaye na gargadin auren doguwar mace, wato wace aka dauko ta daga nisan duniya, ba don komai ba sai nisantar 'yan uwan mijin a dalilin rashin daidaituwar al'ada na yanki.

Wani sa'in duk abinda ba naka ba sai ka ƙyamace shi komai kyawunsa kuwa. Wani abin takaici da na gani, wani baƙauye ne ya yi karatu. Allah ya taimake shi da ƙwaƙwalwa. Yana gama jami'a suka riƙe shi, ya zama malami. A dalilin haka ya sami wata 'yar birni ya aura, duk da cews ita ma talaka ce irinsa amma ta ƙyamaci 'yan uwansa, ba ta ƙaunar ganinsu ko alama, duk in sun zo tana musu kallon sun zo kwadayi ne, ko neman taimako in ta kyautata musu zato, duk da cewa komai maigidan yake samowa 'yan uwanta su zo su lashe.

Ƙila abinda zai iya magance waɗannan matsalolin shi ne ƙara aure, wato ka auro wata 'yar zumuncinka, wace 'yan uwanka nata ne, duk wanda zai zo wurinka gidanta zai sauka, in kuma wani abu na zumunci ya taso za ta leƙa, alla-alla ma take yi a sami abinda zai kai ta cikin dangi, kowa ya ganinta zai ce ga matar wane can, na ji waɗanda suka yi ta zagin matar dan uwansu a dalilin zargin da suke yi mata na wulaƙancin da take musu, a ƙarshe suka matsa wa dan uwan nasu kan ya ƙara aure kuma a zumunci.

In har ta ga ya auro 'yar uwansa kuma hankalinsu ya koma kanta dole za ta sauko, in ba haka ba a maida ita sanuwar ware, za ta gyara mu'amalarta da 'yan uwansa gaba ɗaya, ta rage irin wulacin da take musu ko ma ta daina gaba daya, kenan ƙaurace wa 'yan uwan miji da rashin kyautata musu da mace ke yi yakan zama babban dalili na tilasta masa ƙarin aure, ko bai yi don kansa ba zai yi don kyautata alaƙarsa da 'yan uwansa.

Post a Comment

0 Comments