Na ji wata da kunnena tana cewa almubazzaranci ne a ce
gida kamar wanda take ciki mace ɗaya ce rak. Maganar ba da ni ake ba bare na yi tambaya, amma...
Zan Ƙara Aure
// 19: Wadata ma Dalili ce
Baban Manar Alƙasim
Zauren
Markazus Sunnah
Da
yawan maza sun yarda cewa wadata babbar dalili ce ta ƙara aure, ina ganin da wannan ne ma ya fara zuwa a farko
da ya fi, domin galibin abida ake kira wa wanda ya ce zai ƙara aure kuma baida abin hannunsa sosai shi ne wahala, in
ya zamanto mutum baida matsala Allah bai ƙuntata masa ba me zai sa
kuwa ba zai ƙara ba? Na yarda da karatun da yake cewa in ba ka da
halin mace biyu to ka tsaya a guda, don wanda ya kwadaitar da cewa a yi auren
ma ai ya ƙara da cewa "Wanda ya ga yana da halin riƙewa to ya yi aure".
Ƙarara kenan wanda bai da
shi ya haƙura, indai ta farkon ma akwai wannan sharadin to mai ƙari shi ya kamata ya dan dakata har Allah SW ya yassare
masa, babban abin kula mata biyu masu zama a nesa da juna sun fi kowa rashin
fitina da tashin hankal a tsakaninsu, duk da cewa wasu matan su da kansu suke ƙin yarda a raba su, amma ina zaton irinsu ba su da yawa,
wani ya taɓa ce min akwai su a Nigeria, amma ni wata 'yar Indonesia ce take ce min ba
ta damu a yi mata kishiya ba, kawai dai abinda za ta roƙa shi ne ko dai su hadu a daki guda ni da turakata, ko
kuma kowa da dakinta amma gida guda, da yake duniyar da faɗi ban yi mamaki ba ƙila haka suke yi acan.
Mu kam
har karin magana ne da mu "Mata in ba ku ba gida, in kuka yi yawa gida ya
lalace" babban abinda muke gani wadata ce ke sakawa mutum ya yi aure biyu ɗaya na Borno dayan kuma
can Legas, tazarar da ta fi kowace nisa kenan a Nigeria, wani kuma a jaha ɗaya amma garuruwa
daban-daban, wani a gari guda amma ya raba unguwannin, wasu ma unguwarsu guda
amma gida kowa da nata, wasu a gida ɗaya kowa da ƙofarta.
Wannan
duk wadata ke kawo shi, akwai waɗanda falo ke haɗa su kowa da madafarta, na ga waɗanda hatta kicin da
ban-daki guda ne, dakin kwanciya ne kawai daban, galibin masu haɗa matan wuri guda za ka
ji suna cewa "Abinda Allah ya hore mana kenan zakaranka raƙuminka" to in waɗannan a irin wannan halin sun yi manejin rayuwa sun zauna
da mata 2-4 kai da kake da hali ko na ce mutumin da matsuguni ko sutura ko
abinda za a sanya a bakin salati ba matsalarsa ba ne me zai hana ka ƙarin aure?
Kamar
dan kasuwan da yau yana Kano in ya tafi Legas sai ya share wata 2 bai dawo ba
ai matar ma in ba ta ce masa ya dauke ta ba dole ne ma ta matsa masa ya ƙaro wani auren, don ko ba ta yi tunanin lafiyarsa ba dole
ta yi tata tunda duk abinda ya jajibo tare za a raba, babbar matsalar da za ta
hana aure rashi ce, su kuma Allah ya rufa musu asiri, in ta yi tunanin cewa ba
za ta iya zaman gida ba kamar za a cutar da ita sai a fara kaso, wannan ta yi
wata biyu a gida, in ya dawo da wancan sai ya koma da ita.
Yanzu
kamar matar da na ji tana neman mafita ai ka ga ba za a yi wa maigidanta
maganar aure ba, ta ce tana da yara da dan dama, babbar 'yar ta isa aure, amma
haka suke kwana a daki ɗaya kamar awaki har da maigidan, ta ce: Ko ciki da falo
ne akwai matsala bare daki ɗaya ne tilo kuma haka yake bin tsawon shimfidarsa, abinda
yake damunta shi ne; ba yadda za a ce wannan budurwar tata da wannan shekarun
ba ta san abinda yake faruwa ba, ta gwada wa maigidan amma ya ƙi saurara bare ya dauki mataki, shin za ta iya yi masa
kadada ta yi shinge?
Na ji
wata da kunnena tana cewa almubazzaranci ne a ce gida kamar wanda take ciki
mace ɗaya ce rak. Maganar ba
da ni ake ba bare na yi tambaya, amma dai na san uwayenmu a karkara in dai
magidanci yana noma abinda ya fi ƙarfin iyalinsa ga ajiyar
taki na noman badi gami da tarin sulalla a aljihu dole ne a ƙara aure. Na ji malamai na cewa Hadisin da aka ce in
talauci ya ishe ka ka ƙara aure bai inganta daga Annabi SAW ba.
Suka ce
hadisin yana da rauni ta bangaren sanadi da gundarin maganar, a taƙaice in mace ta ga maigidanta ya sami kuɗi takan yanke wa kanta
cewa amarya za ta shigo, masamman in ta ji za a sayi gida ko an fara gyaran
wani daki, a dabi'ance ma mai hali ake ba shi shawarar ya ƙara aure, talaka sai dai a hana shi saboda ganin abinda zai
kai ya komo, a kwanakin baya mun ji wanda ya saki amaryar saboda rashi, na kuma
ga wanda ya gudu wurin amaryar ya bar uwargidan da yara sai ya yo waya wai masu
garkuwa da mutane sun sace shi, kenan ya yi rigimar aure ba wadata.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.