Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Ƙara Aure // 18: Ya Dai Fi



Akwai mazan da tsawon gashinki bai dame shi ba. In haka ne me ƙarin gashi zai yi miki? In hasken da Allah ya halicce ki da shi ya yi masa don me za ki kashe kuɗinki a kan maida-tsohuwa-yarinya?

Zan Ƙara Aure // 18: Ya Dai Fi

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Kowace mace za ka taras tana da sifar adonta da yadda take abinta, don dama adon mace akan kasa shi har hudu ne, su suke daukar hankalin mai kallo:-

1) Mace a dabi'ance ta ƙara wani abu ko ba ta ƙara ba ado ce, dole namiji ya kalle ta matuƙar lafiyarsa lau, imani da tsoron Allah ne kawai za su hana, don ma a sauƙaƙe masa wajen kare wannan dabi'ar shi ya sa Allah SW ya umurce shi da samun na halalinsa har guda 4, sannan ya hana shi kallon matan wasu, ya sa matan ma kansu su ɓoye duk abinda zai sa a kalle su din.
2) Akan ƙara wa jiki wani abu don ya taimaka wajen fito da adon mace kamar dai: Turare, jan-baki, hoda, gazal, lalle, ko ta tamke ƙugu don fito da girman baya, ko ta daga ƙirji da sauransu, waɗannan in aka sa kafcecen gilashi, bayan niƙabi ko hijabi shikenan an gama.

3) Sai suturar jiki kan taimaka wajen ƙara fito da kyawun mace, masamman takalmi na zamani, ko irin ƙyallen da aka dunka, ko tsarin dinkin, da zane, riga, zuwa dankwali, sai dan kunnaye da ake liƙawa da abin wuya, na hannu, zobe da mannen hanci, duk dai mace za ta iya amfani da su don fito da kyawunta.

4) Kyawun hali da dabi'a abubuwa ne guda biyu da su ma sukan ƙara kyawun mace, duk kyawun da mace za ta yi, a dalilin wani ado ko wata kwalliya matuƙar maigidanta ba ya so wannan ya zama aikin banza barinsa ya fi, koda kuwa duk garin na yaba mata, wata macen takan burge maigidanta da gashi ne, wata hoda da jan-baki da gazal, wata ma lalle, akwai wace sutura ke bayyana adonta sosai har maigidanta ya buƙace ta.
A lokacin da kika fahimci cewa lalle ke dauke hankalin maigidanki, koda kuwa in kin yi bai yabawa ya zama dole ki riƙe shi da shi, don mata wasu na yi kuma ba sa ɓoyewa, wata in ta yi lallen hatta mata kan yi sha'awa bare kuma maza, sai ki koya in ba ki iya ba, ki duba kalar lallen da shi maigidan yake so, koda kuwa a tunaninki bai da kyau ko bai ba ki sha'awa, wani namijin jan-lalle ke janyo hankalinsa, wani kuma baƙi.

In fa ya nuna miki cewa yana bala'in son lalle, ke kuma kina ƙyamarsa kika ga ba za ki iya yi koda yaushe ba, ko yana son jan lalle ki ka ce ke baƙa ce jan lalle ba ya miki kyau to ki tabbatar in kin hana shi kallo a jikinki wasu matan suna bayyanawa kuma sau da yawa ba ya iya hana idonsa kallo, in aka yi dace da wata budurwa ko bazawara wace take yawan yi, wannan fa zai iya zama babban dalilin da zai sa ya fara tunanin ƙarin aure, haka sauran ababan adon na mata, abin nufi anan kar ki bari ya kalli abinda yake so a jikin wata don kar ya zama dalilin kusantarta.

Akwai mazan da tsawon gashinki bai dame shi ba. In haka ne me ƙarin gashi zai yi miki? In hasken da Allah ya halicce ki da shi ya yi masa don me za ki kashe kuɗinki a kan maida-tsohuwa-yarinya? Yi ƙoƙari ki san adon da zai birge maigidanki kawai, in namiji yana sha'awar doguwar riga, koda ba ki so je ki ki dinka, don ko kin yi riga da zane ko sikyal wani nau'in da ake yayi ba birge shi zai yi ba, ƙarshe za ki sha wahalar banza ko ki kashe kudinki a zo bai yaba ba.

In dai kina gidan mahaifanki kafin ki yi aure kina kyarkyara wannan kuwa, ƙila adon da ake yayi za ki yi don neman Allah ya turo rabonki ya fada tarkonki, tunda Allah ne zai turo sai ki yi ƙoƙari ki kiyayi saba masa wajen yin adon, amma in kika zama matar mutum to fa ba ki da wata kwalliya sai wace yake so, koda kuwa takin tana ba ki sha'awa haka za ki bari ki dauki wace yake so, bari na ari ta bakinku "Kafin shedan ya fara rada masa cewa wata na yin kwalliyar da yake so don haka ya kamata ya auro ta".

Post a Comment

0 Comments