Header Ads Widget

Request to place your ads here.

Kanu

6/random/ticker-posts

Yadda Ake Yin Sallar Jana'izaAkwai buƙatar a yaɗa wannan saƙo dan Allah ta hanyar share domin 'yan uwa Musulmai su ƙaru. Allah ya ba da ikon hakan. Ameen.

Yadda Ake Yin Sallar Jana'iza

'YAN-UWA mafi yawancinmu, muna yin Sallar Jana'iza amma kuma ba mu san abinda ake faɗa a cikin kowacce Kabbara ba. Dan haka ya sa muka ga cewa yana da kyau mu ware wani lokaci na musamman, Domin fahimtar da mu yadda ake yin sallar Jana'za.

'YAN-UWA ita dai Sallar janai'za, tana da babban lada, ga wanda ya aikata ta kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar, dan haka yana da kyau, mu tsaya mu koya. Kamar yadda na ce, sallar jana'za tana da kabbarori guda hudu ne kawai kuma kowacce Kabbara da abin da ake fada a cikinta.

1. KABBARA TA FARKO ana karanta {suraul-fatiha} ne kawai, banda wata sura, ko wata a'ya.
2. KABBARA TA BIYU ana karanta Salatin Annabi ba wani salati na daban ba.
3. KABBARA TA UKU ana yin addu'a ga wanda ya mutu mace ko namiji.
4. KABBARA TA HUƊU za ka yi addu'a ne ga sauran al'ummar Musulmi Waɗanda suke  Raye da matattu.

DAN UWA KANA GAMAWA sai ka jira Liman ya yi sallama.
Ita kuma sallamar guda ɗaya ce tak! Kuma za ka yi ta ne a ɓangaren damanka.
Allah muke roƙo da ya kara tabbatar damu akan Sunnar Annabin Rahama, Manzon Allah (S.A.W).

Akwai buƙatar a yaɗa wannan saƙo dan Allah ta hanyar share domin 'yan uwa Musulmai su ƙaru. Allah ya ba da ikon hakan. Ameen.

Post a Comment

0 Comments