Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Ƙara Aure // 17: Wallahi Tausayi ne Kawai



Mutum irin wannan ka san daga shi har matansa ba su da kwanciyar hankali, sai in sun aurar da yaran...

Zan Ƙara Aure // 17: Wallahi Tausayi ne Kawai
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
Wani sa'in a tsakaninmu in ka dubi dan uwanka da kai komonsa da rashin natsuwa wuri guda bare a yi maganar hutu sai ka ga akwai tausayi, babban abin lura shi ne rashin katamaimen aiki ko wani kama-sayar, haka dai kullum zai fita ko a samu ko a rasa, wani goro yake saidawa, wani gauta, wani katin mtn ne, wanda sai ka sayar da na Naira 3,000 ba ka sami ribar Naira 100 ba, a gefe guda kuma ga yara na jiransa in zai shigo ya riƙo musu dan taɓa ka lashe, uwayensu na jiran na kalaci, kudin makarantar Islamiya bai gama haduwa ba bare na boko.
Masu wuta ko ruwa ba abinda ya dame su da samun mutum ko rashi, duk in suka kawo bill bai je ya biya ba su yanke, ko ya biya kudin sai ya ƙara na maidawa, ba makarantar boko ba ko ta Islamiya ce in mutum bai biya ba sai dai ya taras da yaransa a gida an koro masa su, gidan haya ma ba daga ƙafa, in ka biya din ma ya aka ƙare bare babu? Bar batun cin mutunci da masu gida za su yi maka in ka ƙi biya, na ga gidan da aka tashi wani ya ce sai an ba shi notice don ya sami damar neman wani, wallahi maigidannan haka ya yaye kankwanon gidan gaba ɗaya ya bar su suna kallon sararin samaniya, in ba sanyi ko ruwan sama ai ka yi tsoron barawo da daddare in gari ya waye kuma zafin rana, bare kuma daki wurin rufin asiri ne, ko ba magana za a sami mutsu-mutsu, dole dai kenan mutum ya tashi.
Wanda Allah SW ya azurta shi da 'ya'ya mata manya waɗannan kamar ƙari ne kan matansa, duk buƙatunsu iri guda ne, har gwara ma matan don duk yawansu ba za su wuce 4 ba, in kana da 'ya'ya mata da dama dole hankalinka ya tashi, suna buƙatar dakinsu daban, don ba za ka haɗa su da maza ba, suna rabe din ma ya aka ƙare bare suna hade? Ka ga ka sami tilascin ƙara dakunan haya kenan, yawan dakunanka yawan abinda za ka riƙa kashewa a shekara.
Mutum irin wannan ka san daga shi har matansa ba su da kwanciyar hankali, sai in sun aurar da yaran, ciyar da su, tufatartar da su, sama musu wurin zama, yalwata su da ilimin zamani ko na addini, ɗebe musu haso ta wurin shagaltar da su da wasu abubuwa kamar sana'a ko aiki, kawo musu 'yan abubuwan da suke buƙata don kawar da hankulansu daga samari, kare su daga sharrin 'yan gani ba ƙyalewa, wai wani taimako kake gani za ka yi musu ya yi maganin duk waɗannan matsalolin? Shi dai uban yarinya kullum yana waje, ƙila daga safiya har maraice, burinsa ya kalato dan abinda zai rufa musu asiri.
Ita kuwa uwar aikinta kenan bibiyarsu, don ko ƙawayensu tana da buƙatar saninsu da irin tarbiyyarsu. In ma shigowa gidan suka yi za ka taras tana ƙoƙarin sanin irin hirar da suke yi, don dai ta ba su tsaro. Ko fita za su yi sai ta iyakance inda za su, da wanda za su wurinsa, da lokacin da take buƙatar su dawo, tare da samun tabbacin kariya a fitarsu zuwa dawowa, barcinta kaɗan ne da rana saboda aiki, da daddare kuma aikin kenan yi musu nasiha da jan kunne, to wane kwanciyar hankali dayansu keda shi, kuma ya za a iya yi musu taimakon da zai zama dauwamamme ya shafe duk waɗannan abubuwan dake gajiyar da su yake raunana su?
Mafita kenan a raba su da yarannan gaba daya, a aure musu su, in ka auri diyarsu, cinta da shanta, matsuguni da tufafi, karatu da tarbiya komai ya tashi daga kansu, ashe a irin wannan zarafi taimaka wa waɗannan mutane ko tausaya musu babban dalili ne na ƙarin aure, bai yuwu kullum ka ba su kudin ciyar da kansu ko na yara, ba kuma zai yuwu ƙato da kai ka ba ni abu ka ce wai na kai wa matata ba bare diyarta, auri diyar kawai, in ka yi haka ka gama min komai.

Post a Comment

0 Comments