A zuciyata na ce "Bari na yi alwala na yi salla raka'a 2 don gode wa Allah. Lokacin da na idar sai na ga ashe tare muka yi da ita. Yayin da 'yan uwa da abokai suka watse sai na matsa kusa da ita na miƙa hannuna. Sai ta ce "Dakata Abu-Umayya." 

Kundin Ma'aurata // 19: Ki Buɗe Idanunki
Baban Manar Alƙasim

Duk girmanki da wayewarki ƙila wanda yake nemanki ya fi ki, don mai son abinka ya fika dabara, haka muke cewa da Hausa, a cikin shika-shikan ƙauna akwai fadi da baki, da nuna wa a aikace bayan tabbatuwa a zuciya, tausayi dake cakude da soyayya shi yake bayyana irin yadda kake son masoyinka, komai naka nasa ne sai in bai nuna yana so ba, wani lokaci ma ba sai ya furta ba, in dai ka ga kamar yana so za ka iya ba shi, koda kuwa hakan zai iya baƙanta maka rai a nan gaba, galibimmu maza mun san wannan, mata ne dai ba su cika ganewa ba, wasu lokutan sai an kwashi ƙafafunsu suke fadaka, misali: Wata mata ta sami wani malami take cewa "Tsakani da Allah ni ba mazinaciya ba ce, amma maigidan da na aura tun shekara 16 da suka wuce wani abu ya faru kafin ɗaura aure"

Malamin ya tambaye ta "Kamar ya?" Ta ce "Ana sauran 'yan kwanaki kadan a ɗaura mana aure shedan ya dan yaudare mu, gaskiya malam mun san juna kafin aure, to ni abin yana min ciwo tsawon wannan shekarun, tunda ba mu yi istibra'i ba shin auremmu ya dauru ko ya?" A lokacin da ka ji ana cewa saura 'yan kwanaki a ɗaura aure shedan kan yi aiki da wannan damar don ganin ya cimma burinsa, ke amarya ki shiga taitayinki, sha'awa wani lokacin ba ta da linzami, ki guji duk abin da zai sa ki ki kebe da saurayinki nesa da idanun jama'a, bar ganin kina da wayau ko wayewa, namiji da wayewarki zai yi amfani ya cimma burinsa.

Batun ki zo dakinsa ko ku hadu a hotel wurin tattauna kaza da kaza bai taso ba, ke tasa ce tun daga ranar da aka ɗaura aure, tunda an kusa ya yi haƙuri kawai, kina ƙoƙari ne ki tafi masa a tsarkakkiyar uwa, don haka ya ba ki wannan damar, duk wani ban baki da taushe murya kar ki yarda da ita, zancen cewa ya kai sadaki gidanku don haka kin halasta masa maganar banza ce, in haka ne kuwa to meye amfanin ɗaura auren matuƙar kai sadaki ya gama komai, mace ba ta halasta sai ta gama cika duk rukuna ɗaura aure, kamar waliyi, shedu sadaki da sigar ɗaura auren, tunda ba a yi wannan ba to ki bari sai an yi tukun, namiji in yana buƙatar abu a wurin mace marairaice mata zai yi, da haka wasu 'yammatan suke zuwa dakunansu da ciki, bayan shekaru abin ya yi ta yi musu ciwo.

A Fahimtata
Walima akan yi ta ne don koyi da sunnan ma'aiki kuma mutun ya nuna jin dadinsa da gode wa Allah bisa wannan abin arziƙi da ya samu, sai dai shari'a ba ta bar ta haka kara zube ba, ta gindaya wasu sharuddai da dokoki wadanda za a bi, bai dace ba Allah ya yi maka arziƙi a maimakon ka gode masa wajen bauta masa, sai kuma ka juya ka saba masa kuma a daidai wannan lokacin kana neman ya yi maka albarka, ba a roƙon Allah SW da zunubi, ko walimar an ce ka kira mutanen kirki, ba ka rubuta a invitation kowani irin mutum ya zo ba, sannan an yi bayanin irin abincin da ya kamata ka bayar da wadanda suka dace ka tuntube su.

Hada 'yammata da samari ana kida ana rawa gami da wasu nau'o'i daban-daban na sabon Allah kamar shigar tsaraici da matan keyi, gwamatsuwa da maza har zuwa alfahasha a ƙarshe, wannan yana nuna yadda yadda kake so zuriyar ta kasance kenan a gaba, mutumin da ya yi walima bisa koyarwar Annabi SAW yana ladar kwatanta sunna, yana kuma da ladar ciyarwa, sannan in wani ya yi sha'awar yadda ka yi shi ma ya dauka daga wurinka ka nuna masa alkhairi kenan kai ma kana da ladarsa, to bare kuma za ka ji mutane suna ta zabga maka addu'o'i kamar yadda aka koyar, wasu har tsohonka sai ya sami kasonsa, masamman in walimar ta amsa sunanta, in ba ka da halin kiran mutum 70 ko mutum 7 ka kira ka yalwata musu ya fi.

Bayan Aure
Na tsinci wani labari a littafin "Az-Zauj Al-Mithaaliy" na Dr Ridal Nasriy p9-10, inda ya kawo cewa: wata rana Alƙali Shuraih ya sadu da Sha'abi, sai Sha'abin ya tambaye shi lamarin gida, sai Shuraih yake cewa "Shekara 20 kenan iyalina ba su taba yi min abin da ya baƙanta min rai ba" Sha'abiy ya ce "Kamar ya?" Shuraih ya ce "Ranar farko da na shiga dakin amarya na ga wani kyawun dake fisgar hankali wanda ba ko yaushe ake samun irinsa ba.

A zuciyata na ce "Bari na yi alwala na yi salla raka'a 2 don gode wa Allah. Lokacin da na idar sai na ga ashe tare muka yi da ita. Yayin da 'yan uwa da abokai suka watse sai na matsa kusa da ita na miƙa hannuna. Sai ta ce "Dakata Abu-Umayya." Ta yi hamdala da salati ta ce bayan haka. "Ni baƙuwa ce a gidanka. Ban san dabi'unka ba. Don haka karanto min abin da kake so don na riƙa yi maka, wanda ba ka so kuma na guje shi".

Ta ce "In a danginku akwai wace da ka so ka aura to ni ma haka ne, amma abin da Allah SW ya so shi zai faru, yanzu dai ni mulkinka ce ka yi abin da Allah SW ya amince maka, daganan ko dai ka riƙe ni da kyau ko ka rabu da ni cikin dadin rai, a wannan maganar nake nema mana gafarar Allah gaba daya" Shuraih ya ce "Sha'abi, sannan ne nima na yi yunƙurin yin tawa hudubar, na yi hamdala da salatin Annabi SAW, na ce " Kin yi wata babbar magana wace in kika tsaya a kai to kin yi sa'a, in kuma kika canja to za ta zamemin hujja a kanki, ina son kaza da kaza da kaza, in kin ga wani abu mai kyau ki bayyana a gani, mummuna kuma ki boye"

Ta ce "To ya maganar zuwa gaida 'yan uwana?" Na ce "Ban son surukaina su ƙosa da ni" ta ce "Maƙwabta fa, wa kake so ya shiga gidanka waye ba ka so?" Na ce "Gidan su wane mutanen kirki ne, su wane kuwa mutanen banza ne, daganan ne na sami kanta, shekararmu 20 ban taba ganin abin da zai baƙanta min rai ba sai sau daya, shi ma din ni ne na dauki alhakinta" namji in ya shiga dakin amarya wata muguwar sha'awa take lullube shi, ita matar ta sa hankali ta nuna masa abin da ya dace.