Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Ƙara Aure // 15: Ta Ishe Ni



In dai ka raba su kowa da gidanta, wannan ba ta san abinda wancan take ciki ba, to ka huta...

Zan Ƙara Aure // 15: Ta Ishe Ni

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Da yawa mata na da rauni a wannan bangaren, koda yake ba dukansu ba ne, na ji wace aka ce ta taimaki maigidanta wajen ƙara aure, na ga wace ta kawo wa maigidan zanƙaleliyar mata ta ce ya aura, na ga wace ta rabu da mijin a kan ya ce zai ƙara aure, na ga wace ta kashe kanta a dalilin ƙara auren, wata mijin ta kashe saboda ya ce zai ƙara wata matar, na ga hoton wace ta hallaka shi gaba ɗaya duk dai a dalilin ya ce zai yi aure, babu wanda ba ya faruwa, mata kala-kala ne kamar yadda muke daban-daban, sai dai wasu sun fi wasu.

Akwai matan da ba sa son kishiya ko misƙala zarratin amma kuma sam ba sa kyautata wa mijin. Wallahi na ga wanda gidansa ke gagararsa zama saboda tsabar fitina, dole sai dai ya komo waje ya zauna, duk ya yi firgigi ya lalace a dalilinta, da bakinsa na ji yana cewa in ya bar gidan hankalinsa a kwance amma da ya dawo da fargaba zai shiga gidan, abin mamaki wallahi ya haife ta, ka ga da girma ne ƙarfi, da damisa ba ta kar raƙumin dawa ba, amma ba anan take ba, wai an danne bodari a ka.

Wani sa'in namiji yana da buƙatar kwanciyar hankali, kuma inda zai iya samu kenan a gidansa, da ya dawo ga murmushi fuskannan na annuri kamar wata a daren 15, ƙanshi ko ta ko'ina, sai dai ya ci abinci mai rai da motsi ya kwanta, in ba yara a gidan ma ya bi tsawon shinfidarsa a ƙarshe ya yi barci har da munshari, to in ya zama cewa masifar daga gida take tashi, kenan babu inda mutum zai sa kansa, rana zafi inuwa ƙuna, in yana da dan abin hannunsa sai ya nemi magani kafin a tura masa hawan jini yana da dan sauran ƙuruciyarsa.
Ba wani abu ne maganin ba kamar ya sami wani gidan inda zai riƙa fakewa ana mantar da shi duniya da abinda ke cikinta, wanda ya yi niyyar ƙara aure a bisa wannan dalilin, kuma ya haɗa amaryar da masifaffiyar matarsa to fa ya yi kisar macijin mata ne, an kashe ba a sare kan ba, don wuri guda dai zai komo, yana gidan ko ba shi bala'in dai yananan, amma in ya raba su, to zai sami kwana biyu cikin kwanciyar hankali da kyakkyawar natsuwa, wani abinda bai taɓa gani ba na ladabi da biyayya da sanin ƙimarsa da daraja duk zai gani.

Duk bala'in mace da ka ƙara aure za ka ji ta fara saukowa "Wai don Allah me nake ma?" Gaya mata ko ba ta bari duka ba za ta rage, abincinka zai gyaru, dadinsa zai dawo, cefanenka zai ragu, za ka riƙa cin abinci a kan kari, ƙananan ayyuka duk za a yi ma, har bashi sai a ba ka. Zancen shimfida ba daga ƙafa ba gajiya. Yanzu kusan komai kana da damar da za ka sa a yi ko ka hana. Hatta 'yan uwanka za su sami sassauci ba kamar da ba. In dai ka raba su kowa da gidanta, wannan ba ta san abinda wancan take ciki ba, to ka huta.

Post a Comment

0 Comments