Ticker

6/recent/ticker-posts

Ɗora ma’anonin Wada Hamza da Aliyu Muhammadu Bunza a kan ‘Cuta’ a Mizanin Awon Al’ada.


Idan muka yi la’akari da abin da shaihin malami Aliyu Bunza ya faɗa a cikin wannan ma’ana da ya bayar za mu fahimci cewa, ma’anar ta bayar da ƙarfi ga abin da yake da ƙudurin ganowa a bincikensa. Wato ya ta’allaƙa ma’anar ga bincikensa. Wannan kuma ba ya rasa nasaba da ƙishirwar da ke cikin zuciyarsa ta ganin ya bayyana matsalar da yake yunƙurin gudanar da bincike a kai...
Ɗora ma’anonin Wada Hamza da Aliyu Muhammadu Bunza a kan ‘Cuta’ a Mizanin Awon Al’ada.

Haruna Umar Maikwari
07031280554

Gabatarwa
          Wannan jinga za ta mayar da hankali a wasu ma’anoni na “Cuta” da wasu masana suka bayar, kuma a cikin za a ɗora ma’anonin a mizanin awon al’ada domin a tantance ma’anonin da kuma abin da suke magana a kai. Amma dai kafin nan za a yi shimfiɗa da ma’anonin magani. Kasancewar idan cuta ta harbi halitta ko wani abu, magani ake nema domin a samu waraka ko sauƙi ko gyara ko canza a abin da nan da cuta ta yi wa illa. An samu wasu masana sun tofa albarkacin bakinsu dangane da abin da ake nufi da magani. Kamar Bunza (1989) ya bayyana ma’anar magani da cewa, wata hanya ce ta warkarwa ko kwantar da ko rage cuta ta ciki ko ta waje, ko wadda   ake samu daga haɗari ko kuma neman kariya ga cutar abokan hamayya ko cutar da su ko neman ɗaukaka ta daraja ko ta buwaya ta hanyar siddabaru da sihirce-sihirce na ban al’ajabi.” Ahmad (1984) yana cewa, magani shi ne duk wani abu da za a yi, ko wata hanya, ko kuma dabara da ake yi don gusar da cuta daga jikin mutum ɗungurungum, ko kuma kwantar da ita don kawo jin daɗi ga jiki ko ga zuciya da sawwaƙe duk wata wahala da damuwa da ita cutar kan iya haifarwa. Musa (1986) yana cewa, magani wata hanya ce kawai ta neman biyan buƙatar  wata matsala da ke damun mutum, ko kuma yana ganin matsalar tana yi masa barazana. Sarkin Sudan (2013) cewa ya yi, kalmar magani na nufin duk wata hanya da ɗan Adam zai bi wajen warkar da cuta ko rauni ko neman kariya daga cutar. Saboda haka, ana iya cewa, magani shi ne duk wani abu da aka yi amfani da shi domin magance wata cuta, ko cutar da wani aka saka ta ga jikinsa.
          A ganina, magani shi ne duk wata hanya da aka yi amfani da ita domin samun sauƙi ko waraka ko mafita a kan wata matsala da take damun jikin mutum ko zuciya ko kuma rayuwarsa gaba ɗaya. Maganin gargajiya kuwa shi ne, yin amfani da itatuwa ko rubutu ko addu’a ko surkulle, don warkar da wata cuta, ko neman wani amfani, ko gusar da sharri, ko haddasa wani abu saboda biyan buƙata (Alhassan da wasu 1986).
Ma’anar Cuta
          Masana da Manazarta sun tofa albarkacin bakinsu dangane da abin da ake kira ‘Cuta’? ga dai wasu daga cikinsu:
Shi kuwa Adamu (1998). “Cuta tana nufin rauni da raɗaɗi tare da wahala da mutum kan gamu da su a sanadiyar gazawar wata halitta a jiki ko kuma damuwa a zuci.”
          Cuta na nufin wani yanayi ko damuwa ko matsala ko muradi ko ma wani abu makamancin waɗannan da ke kama wani abu mai rai ko maras rai ya zame masa illa ko barazana ko tarnaƙi ko sauya wannan abin daga ainihin yanayinsa na asali da aka san shi, zuwa wani yanayi ko hali na daban. Kuma wannan yanayi yana buƙatar samar da wata hanya da za a magance wannan matsala, ko damuwar ko yanayin ko muradin ko dai wani abun da ya hardasa neman hanyar warware wannan abin.
Ɗora ma’anonin Wada Hamza da Aliyu Bunza a kan ‘Cuta’ a mizanin awon al’ada.
Mene ne Cuta?
          Wada Hamza (1977) a cikin kundinsa na digirinsa na BA mai take “Magungunnan Gargajiya” kundin wanda aka gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya na Jam’iar Bayero. Ya bayyana cewa, “Cuta na nufin wani yanayi ko wani abu da zai matsa wa rai ko ya kawo rashin gamsuwa a rayuwa”.
          Shi kuwa Shaihin Malami Aliyu Muhammadu Bunza(1990) a cikin kundinsa na MA da ya gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya a Jami’ar  Bayero da ke Kano. Kundin mai taken “Hayaƙi Fidda na Kogo”. Ya bayyana cewa, “Cuta wata damuwa ce da ke shiga jikin halitta, domin raunana lafiyarsa, ko kuma ta shafi zuciyarsa, ta fuskokin buƙatocinsa na jin daɗi, ko ɗaukaka darajarsa da sauransu”.
Ma’anar Wada Hamza a Kan “Cuta” a Mizanin Awon Al’ada
“Cuta na nufin wani yanayi ko wani abu da zai matsa wa rai ko ya kawo rashin gamsuwa a rayuwa”.
Idan muka lura da waɗannan kalmomi da aka jama layi a sama su ne suka gina wannan ma’ana.
Yanayi: Wannan wani hali ne da rayuwa kan shiga.
Wani Abu: Wannan yana iya shafuwar duk wani abu mai rai da wanda ba ya da rai.
Matsa Wa Rai: Wannan ya ƙunshi wani hali da ke kawo tarnaƙi, ko illa ga rai.
          Wannan ma’ana ta bayar da haske sosai a kan abin da ake kira “Cuta”. Amma kuma ma’anar ta kalli gundarin aikinsa. Don kuwa ya ɗan rago wani abu da ba a rasa ba, musamman cewar da ya yi “yanayi ko wani abu da zai matsa wa rai ko ya kawo rashin gamsuwa a rayuwa”. Kenan sai wani abu mai rai kawai zai iya kamuwa da cuta a tasa ma’anar.
A Bahaushiyar al’ada ‘Cuta’ na iya kama komai wato abin da yake da rai da ma wanda baya da rayuwa.
Ma’anar Aliyu Bunza a Kan “Cuta” a Mizanin Awon Al’adar Bahaushe
“Cuta wata damuwa ce da ke shiga jikin halitta, domin raunana lafiyarsa, ko kuma ta shafi zuciyarsa, ta fuskokin buƙatocinsa na jin daɗi, ko ɗaukaka darajarsa da sauransu”.
Damuwa: Damuwa wata abu ce da kan shiga jikin halitta ko wani abu don ta raunana wannan halitta ko abun ta fitar da shi daga hayyacinsa da aka san shi da shi a al’adance.
Halitta: Wannan kuma a al’adance tana nufin duk wani abu mai rai da yake rayuwa a doron ƙasa. Halitta na iya kasancewa mutum, ko dabba, ko dangin tsutsaye, ko ƙwari, ko tsirrai, ko dai duk wani abu da Allah ya halitta kuma yake rayuwa a doron ƙasa ko a a cikin ruwa, ko a ƙarƙashin ƙasa, ko a ƙarƙashin dutse, ko cikin dutse, da dai sauran wuraren da ake iya samun halittun su rayu.
Raunana lafiya: Kalmar ‘Raunana’ ta samu ne daga ‘Rauni’ wato mai nufin wani abu da ke naƙasa rayuwa ko wani abu ya fitar da shi a cikin yanayi ko halin da aka san shi da shi tun asali.
Zuciyarsa:  Zuciya na nufin wata tsoka da ke cikin jikin halitta.
Buƙatocinsa: Wannan kalma ce da ta samo asali daga “Buƙata”, wato tilo, idan buƙatar ta fi ɗaya za a kira su da “buƙatu” ko “Buƙatoci”, idan kuma an mallaka su buƙatun ga wani kuma za a ambaci kalmar da “Buƙatocinsa”.
Idan muka yi la’akari da abin da shaihin malami Aliyu Bunza ya faɗa a cikin wannan ma’ana da ya bayar za mu fahimci cewa, ma’anar ta bayar da ƙarfi ga abin da yake da ƙudurin ganowa a bincikensa. Wato ya ta’allaƙa ma’anar ga bincikensa. Wannan kuma ba ya rasa nasaba da ƙishirwar da ke cikin zuciyarsa ta ganin ya bayyana matsalar da yake yunƙurin gudanar da bincike a kai.

Mizanin Awon a Al’adar Bahaushe
Babban mizanin awon al’adar Bahaushe dai shi ne hankali da tunani. A tunanin Bahaushe idan aka faɗi wata kalma yakan kalle ta ciki da waje ya kuma ɗora ta sama da ƙasa da tsakiya ya ga ko za ta yi aiki a wurin da ya ɗora ta ko inda ya saka ta. Don haka idan aka ce wa Bahaushe “Cuta” zai duba kalmar ciki da waje ya ga ko za ta iya tasiri a kan “halitta” da kuma “ƙira”? Ko ga “Halitta” kaɗai ta dogara?

Post a Comment

0 Comments